Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana alhini da jimamin rasuwar fitaccen ɗan jarida kuma mawallafin mujallar TERMS Magazine, Comrade Jafaru Yakubu Maitama.
Marigayin, wanda ya kasance Shugaban Ƙungiyar Muslim Mawallafa Jaridu Da Mujallu ta kasa (MMPAN), wanda ya rasu da safiyar Litinina Kaduna , lamarin da ya jefa ‘yan jarida da abokan aikinsa cikin jimami.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar ya bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa aikin jarida, jagorancin kafafen yaɗa labarai na Musulmi da kuma ci gaban ƙasa.
Maiyaki ya ce Jafaru Yakubu Maitama ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare ƙa’idojin aikin jarida, tare da amfani da kafarsa wajen yaɗa saƙonnin zaman lafiya, sahihin rahoto da kyakkyawan shugabanci a Kaduna da Nijeriya baki ɗaya.
Ya ce gwamnatin Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa, MMPAN da kuma ƙungiyar ‘yan jarida ta NUJ reshen Jihar Kaduna.
“Mun miƙa matuƙar ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokan aikinsa, MMPAN, da shugabanni da mambobin NUJ Kaduna a wannan lokaci na baƙin ciki,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ya kuma roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya jikansa, tare da bai wa iyalansa, ‘yan uwansa, abokan aikinsa da sauran waɗanda rasuwar ta shafa ƙarfin guiwar jure wannan babban rashi.
Ya ƙara tabbatar wa NUJ, MMPAN da iyalan marigayin cewa gwamnatin Jihar Kaduna na tare da ƙungiyar ‘yan jarida wajen jimamin rasuwar wani ƙwararren ɗan jarida wanda ya yi amfani da aikin jarida wajen taimaka wa ci gaban al’umma.














