Ƙungiyar hadin kai da ci gaban Arewa (ACI) ta bayyana aniyarta na lalubo hanyar magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya da haɗin kai tare da zaman lafiya yankin.
Darakta Janar na ƙungiyar, Dakta Abdullahi Idris, ya ce taron mai taken ” Wayar da Kai akan muhimmancin zaman lafiya da tsaro a Arewa” zai zama wata muhimmiyar dama ta haɗa masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da ƙarfafa haɗin kan al’umma.
A wani taron manema labarai da kungiyar a Kaduna ya bayyana cewa rashin tsaro ya yi mummunan tasiri ga rayuwar al’umma da tattalin arzikin Arewa, inda ya janyo asarar rayuka, rushewar harkokin kasuwanci da noma, tare da tilasta wa dubban mutane barin muhallansu.
Ya ce lokaci ya yi da kowa zai haɗa kai wajen neman mafita mai ɗorewa ga waɗannan ƙalubale.
ACI ta jaddada cewa ba gwamnati kaɗai za ta iya kawo ƙarshen matsalar tsaro ba, sai da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya, malamai, shugabannin addinai, ƙungiyoyin fararen hula, matasa, mata, kafafen yaɗa labarai da sauran al’umma.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da adalci, tare da gujewa yaɗa rahotannin da za su iya haddasa rikici ko tayar da zaune tsaye.
Ta ce aikin jarida na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
Taron wanda aka zai gudana a ranar Laraba, 5 ga Agusta, 2026, a dakin taro Arewa House, Kaduna, ana sa ran manyan jami’an gwamnati, shugabannin gargajiya, malamai, jami’an tsaro, ƙungiyoyin fararen hula, matasa da wakilan kafafen yaɗa labarai za su halarta.














