Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da Cibiyar Kula da Masu Cutar Sikila, domin samar da cikakkiyar kulawa da magani ga masu fama da cutar, tare da raba na’urorin auna hawan jini na zamani guda 300 ga ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa.
Gwamnan ya ƙaddamar da waɗannan shirye-shirye ne a wani taro da aka gudanar a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed, inda ya kuma ƙaddamar da rabon kayayyakin kula da mata masu juna biyu da marasa lafiya na sashen gaggawa, tare da sabbin zanen gadon asibiti kyauta.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an bayyana cewa sabuwar cibiyar za ta riƙa ba da gwaji kyauta, shawarwari, magani, ci gaba da kula da marasa lafiya, wayar da kai kan cutar, inganta lafiya da kuma kulawa ta musamman ga masu fama da cutar Sikila a wuri guda.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Yusuf ya ce an kafa cibiyar ne domin inganta samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga masu fama da cutar Sikila, tare da rage wahalhalun da iyalansu ke fuskanta.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da isassun magunguna da sauran kayan tallafin da ake buƙata domin inganta lafiyar marasa lafiya a faɗin Kano.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa rabon na’urorin auna hawan jini guda 300 ya biyo bayan ƙara yawan mutuwar farat ɗaya da ake dangantawa da cutar hawan jini, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen gano matsalar da wuri da kuma kare lafiyar jama’a.













