Rundunar ‘Yansandan Jihar Benue ta tabbatar da cewar mutane huɗu sun mutu sakamakon wani hari da aka kai ƙauyen Abaushwa da ke ƙaramar hukumar Guma.
Kakakin rundunar, DSP Orchia Peter Aondona, ya ce ana zargin ‘yan bindiga ne suka kai harin.
Ya kuma ce an fara bincike domin gano tare da kama waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
Harin ya faru ne a daren ranar Litinin, lokacin da maharan suka shiga ƙauyen suka riƙa harbin mutane.
Wata majiya ta ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai wani mutum da ɗansa da kuma ‘yarsa, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Guma, Maurice Orwough, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu tare da yi wa waɗanda suka ji rauni addu’ar samun sauƙi.
Ya kuma ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya da kuma hana sake aukuwar harin.
Haka kuma ya buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
Wannan harin ya sa jama’a sun nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar ƙaramar hukumar Guma, inda ake yawan kai hare-hare a yankin.














