ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Jihar Katsina Na Shirin Samar Da Tsarin Kula Da Masu Cutar Daji

by Sagir Abubakar
4 months ago

Gwamnatin Jihar Katsina na shirin samar da tsarin kula da masu cutar daji a ƙoƙarin da take na bunƙasa kula da lafiya. 

Ana saran aikin samar da cibiyar zai amfanar da al’ummar jihar har ma da marasa lafiya daga faɗin Nijeriya da kuma ƙasashen maƙwabta. 

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya faɗi haka yayin da yake gabatar da jawabi ga wata tawaga daga ƙasar Jamus a gidan gwamnati da ke Katsina. 

ADVERTISEMENT

Gwamnan ya ce wannan cigaba zai ɗaga matsayin Jihar Katsina na zama gaba wajen samar da kayan aiki da kula da masu fama da cutar kansa. 

Gwamna Raɗɗa ya yaba wa ma’aikatar kula da harkokin lafiya ta jihar bisa haɗin guiwa da kamfanin ƙasar Jamus, yana mai cewa irin wannan haɗin guiwa hanya ce ta bunƙasa harkokin kiwon lafiya.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Gwamna ya bayyana fatan cewa haɗin guiwar za ta ci gaba da sanya injina da kayan aiki tare da ci gaba da horas da ma’aikatan lafiya. 

Ya bayyana cewa a halin da ake ciki wasu ma’aikatan lafiya na samun horo a ƙasar Jamus, yayin da saura ke karɓar horon ta yanar gizo kan yadda za a yi amfani da mashinan. 

A nashi jawabi, Manajan Daraktan Kamfanin mai kula da yankin gabas maso yamma na Afrika, Ansu Dukuray ya ce a kowacce shekara kimanin mutane miliyan 20 ke mutuwa a faɗin duniya sakamakon cutar kansa. 

Ya ce kamar yadda ƙididdiga ya nuna a kowacce rana mutane dubu 26 ke mutuwa sakamakon cutar.

Dukuray ya yi gargaɗin cewa muddin ba a ɗauki matakin da ya kamata ba, nan da shekara 2050 alƙalumman mutanen da za su rasa rayukansu zai iya ƙaruwa zuwa miliyan 35 kowace shekara.

Shi ma kwamishinan kula da harkokin lafiya na jihar, Alhaji Musa Adamu Funtua ya ce tsarin ya yi daidai da ƙudirin gwamnati na gina goben jihar. 

Sagir Abubakar
+ postsBio
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Za A Yi Gwajin Lafiya Ga Ƴan Jaridar Jihar Katsina – Kwamishina
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Gwamnan Katsina Ya Kai Ziyarar Duba Aikin Cibiyar Gyaran Motoci Mai Amfani Da Hasken Rana
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Hukumar RUWASSA Ta Kudiri Aniyar Samar Da Ruwa A Fadin Jihar Katsina

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Salon Sin Na Jagorancin Jihar Xizang Ya Nuna Tarin Damammaki Na Zamanantarwa A Jihar

Salon Sin Na Jagorancin Jihar Xizang Ya Nuna Tarin Damammaki Na Zamanantarwa A Jihar

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.