ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar RUWASSA Ta Kudiri Aniyar Samar Da Ruwa A Fadin Jihar Katsina

by Sagir Abubakar and Sulaiman
7 months ago
ruwassa

Hukumar samar da ruwa da inganta tsaftar muhalli a yankunan karkara ta Jihar Katsina (RUWASSA) ta ce tana kwazo domin tabbatar da aiwatar da ayyukan samar da ruwa a fadin yankunan kananan hukumomi jihar. 

Aikin da take yi yanzu haka ya kunshi kananan hukumomin Batagarawa, Baure, Daura, Funtua, Kafur da Katsina da ake aiwatarwa karkashin shirin SURWASH, wanda gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar Bankin Duniya suke daukar nauyi.

  • Yadda ‘Yan Ta’adda Suka Sace Matafiya 20 A Jihar Neja
  • Neymar Na Duba Yiwuwar Ritaya Daga Ƙwallon Ƙafa A Ƙarshen Shekara

Shugaban hukumar, Alhaji Abubakar Suleiman Abukur wanda ya yi magana a lokacin ziyarar duba wasu wurare a Katsina da Batagarawa. Ya ce hukumar na da kudirin tabbatar da cewa an aiwatar da aikin daidai da yadda aka tsara, domin amfanar al’ummomin yadda ya kamata.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana gamsuwa kan ginin wasu wurare, inda ya hori ‘yan kwangilar su tabbatar da cewa dukkanin wasu korafe-korafe da tsare-tsare da suka shafi aikin an shawo kansu kafin a hannata ayyukan ga hukumar.

Daga cikin wuraren da aka duba a lokacin ziyarar sun hada da famfunan hannu da famfuna masu amfani da hasken rana a Kambarawa layin Kawu, Kwado da Bayan Gidan Taki a Katsina da kuma Borar Gunduwa ‘A’ and ‘B’ a yankin karamar hukumar Batagarawa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A lokacin ziyarar, Alhaji Abubakar Abukur ya tattauna da wasu al’ummomin da za su amfana da ayyukan samar da ruwan da jami’an kwamitocin samar da ruwa da inganta tsare-tsaren ayyukan, gyara da kula da wuraren.

Haka nan kuma, a halin da ake ciki gwamnatin Jihar Katsina ta gina karin famfuna masu amfani da hasken rana a sansanin rundunar sojojin saman Nijeriya da ke Katsina.

Wannan wani Bangare ne na shiri na musamman da gwamnatin Dikko Radda ke gudanarwa da bunkasa samar da ruwan sha.

Da yake gabatar da jawabi a lokacin hannanta wurare samar da ruwa a sansanin, shugaban hukumar RUWASSA, Alhaji Abubakar Suleiman Abukur ya ce shirin na da nufin rage karancin ruwa a cikin sansanin.

Ya ce aikin ya kunshi hada famfunan da wurin tara ruwa da ke sansanin da kuma sake tsarin sassa daban-daban don al’ummar sansanin su samu damar amfana da wuraren yadda ya kamata.

Da yake mayar da jawabi, mukkaddashin kwamandan sansanin, Wing Commander N.C Okorie ya bayyana godiya ga Gwamna Radda bisa aiwatar da aikin samar da ruwa a sansanin. Ya yi alkawarin cewa al’ummomin da za su amfana za su kula da wuraren samar da ruwa yadda ya kamata.

ruwassa
Sagir Abubakar
+ posts Bio
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Za A Yi Gwajin Lafiya Ga Ƴan Jaridar Jihar Katsina – Kwamishina
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Gwamnan Katsina Ya Kai Ziyarar Duba Aikin Cibiyar Gyaran Motoci Mai Amfani Da Hasken Rana
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Gwamnatin Jihar Katsina Na Shirin Samar Da Tsarin Kula Da Masu Cutar Daji
ruwassa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Jam’iyyar NNPP Ta Yi Ɓatan Dabo A Tarkadar Zaɓen Cike Gurbi Na Kano

Jam’iyyar NNPP Ta Yi Ɓatan Dabo A Tarkadar Zaɓen Cike Gurbi Na Kano

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.