ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kaduna Ta Ce Shari’ar Zidan Ta Gudana Cikin Gaskiya da Adalci

by Shehu Yahaya and Sulaiman
8 months ago
Kotu

Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada cewa an bi dukkan ka’idojin shari’a yadda ya dace, bisa hujjoji da shaidu na gaskiya inda ta karyata rahotonin kafafen sada zamunta dangane yanke hukuncin kisa da aka yanke wa Zidan.

Da yake jawabi kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke a ranar 6 ga Janairu, 2026, Kwamishinan Shari’a, James A. Kanyip, ya bayyana cewa Victor Solomon wanda akafi sani da Zidan ya fuskanci shari’u guda biyu daban-daban a gaban kotuna biyu mabambanta, kan laifuffuka daban-daban da suka shafi mutane daban-daban.

ADVERTISEMENT
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 3 Da Abubuwan Fashewa A Katsina
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 3 Da Abubuwan Fashewa A Katsina

A wata sanarwa da rabawa manema labarai Kwamishinan yace “Babu wani sabani a hukuncin da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Victor Solomon an gurfanar da shi ne a shari’u biyu daban. An wanke shi daga zargi a shari’a guda a shekarar 2024, amma kuma an same shi da laifi a wata shari’ar daban a 2026 bisa ga shaidu da aka gabatar a kotu,” in ji Kanyip.

Ya bayyana cewa shari’a ta farko mai Lamba KDH/KAD/73C/2020 wadda ta shafi haɗa baki wajen aikata laifi da yunƙurin aikata kisan kai, ta ƙare da sallamar sa tare da wanke shi daga zargi a ranar 21 ga Mayu, 2024”

“Shari’a ta biyu mai Lamba KDH/KAD/78C/202 ta shafi manyan laifuffuka da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, jikkata mutum ba tare da dalili ba, da kuma kisan kai da ke da hukuncin kisa. An kammala sauraron wannan shari’a a watan Oktoba, 2025, inda daga bisani aka same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 6 ga Janairu, 2026.

“Kotun ba ta yanke hukunci bisa son rai ko dalilan siyasa ba. An bi doka da oda, an gudanar da cikakkiyar shari’a, kuma alkalin kotu ya tantance hujjoji da shaidu yadda ya dace,” in ji Kanyip

Ya ƙara da cewa wanda aka yanke wa hukunci yana da ‘yancin daukaka ƙara har zuwa Kotun Koli kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Da Yake Karin haske kan hukuncin kotun , Kwamishinan Yada Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya gargaɗi jama’a kan yaɗa labaran ƙarya musamman a kan muhimman batutuwan shari’a.

“Yaɗa labaran ƙarya game da hukuncin kotu abu ne mai hatsari. Yana iya tayar da hankalin jama’a da haddasa rikici ba tare da dalili ba. Muna kira ga al’ummar Kaduna da su rika tantance sahihancin labari kafin yadawa,” in ji Maiyaki.

Kaduna
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
Kaduna
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Yawan Motoci Masu Aiki Da Sabbin Makamashi Da Sin Ta Sayar Ya Ci Gaba Da Zama Matsayin Farko A Duniya A 2025

Yawan Motoci Masu Aiki Da Sabbin Makamashi Da Sin Ta Sayar Ya Ci Gaba Da Zama Matsayin Farko A Duniya A 2025

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.