ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gyare-gyare Sun Sa Zaman Al’umma Samun Ci Gaba

by CMG Hausa
4 years ago

Abokaina, ko kun jefa kuri’unku a babban zaben kasar Najeriya na wannan karo? Da fatan za a kammala ayyukan babban zaben lami lafiya, ta yadda za a aza harsashi na siyasa mai kyau ga ci gaban kasar Najeriya cikin shekaru masu zuwa.

A telabijin, na ga wani dan Najeriya da ya halarci babban zaben ya gaya ma manema labaru cewa, “Ya kamata mu jefa kuri’a, saboda muna bukatar wata sabuwar kasar Najeriya, da sauya abubuwa da yawa.” Maganarsa ta nuna ma’anar yin zabe, wato kawo sauye-sauye ga wata kasa, inda za a yi amfani da sabbin manufofi wajen daidaita matsalolin da ake fuskanta, da raya tattalin arziki, gami da kyautata zaman rayuwar jama’a.

Batun nan ya sa ni tunawa da wani taron da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mai mulki a kasar, ta gudanar da shi a birnin Beijing, a kwanakin nan, inda wani babban jigon da ake tattaunawa a kai shi ne yin gyare-gyare kan tsarin hukumomin kasar.

ADVERTISEMENT

Abokaina da suka fahimci tsarin siyasa na kasar Sin, za su san cewa, kokarin yin kwaskwarima kan manufofi da tsarin hukumomi wata babbar manufa ce da kasar ke nacewa a kai. Cikin shekaru fiye da 70 bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, an yi babbar kwaskwarima kan tsare-tsaren hukumomin kasar har sau 13, inda aka takaita wasu hukumomi da ma’aikatansu, da inganta kwarewar hukumomin gwamnati ta fuskar samar da hidimomi ga al’umma, da sanya yanayin aikin mulki ya dace da tsarin baiwa kasuwa damar yin halinta, da dai makamantansu, tare da samun nagartaccen sakamako.

Idan mun dauki aikin takaita hukumomi a matsayin misali, wata kwaskwarimar da aka yi wa hukumomin kasar Sin a shekarar 2018 ita kadai, ta sa yawan ma’aikatun gwamnatin kasar ya ragu da wasu 8. Ta wannan hanya, an daidaita tsarin hukumomi, da samun karin jami’ai masu kwarewar aiki. Ban da haka, an rage ma jama’ar kasar nauyin biyan haraji, kana sun samu sauki sosai yayin da suke gudanar da wasu ayyuka a hukumomi daban daban.

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Wannan kwaskwarima ta nuna yadda gwamnatin kasar Sin ke iya sabunta tsare-tsare da kanta, inda take neman zamanintar da dabarun mulki a kai a kai, ba tare da tsoron gudanar da gyare-gyare kan hukumomin kasa kai tsaye ba, musammam da zummar tabbatar da ci gaban kasa da na zaman al’umma, da gamsar da daukacin al’ummun kasar. Ma iya cewa, dukkan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya tattalin arizki, cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, shaida ce ga yadda gyare-gyare ke haifar da ci gaban zaman al’umma.

To, tun da aikin kula da wata kasa na bukatar a yi masa kwaskwarima a kai a kai. Shin duniyarmu ita ma tana bukatar samun gyare-gyare a kan tsarinta?
Hayley Arceneaux, wata ‘yar saman jannati ce, wadda ta taba rubuta cewa, “ Yayin da nake hangen duniyar Earth daga sama, na ga a karkashin abubuwa masu kyan gani, akwai wasu abubuwa marasa kyau. Misali, ko da yake dukkanmu na rayuwa kan wannan duniya, amma mutanen da aka haife su a wannan bangare na duniya, da wadanda suke zama a waccan bangare, gibin zaman rayuwarsu ya yi yawa.”

A da can, wasu kasashen yammacin duniya masu karfi sun kafa wani tsarin duniya maras adalci, ta hanyar yake-yake, da mulkin mallaka, da raba ikon mallakar yankunan duniya tsakaninsu, wanda ke ci gaba da kasancewa a duniyarmu har zuwa yanzu. Sa’an nan wasu kasashe sun dade suna rike da ra’ayin “cin nasara daga faduwar wani bangare”, saboda haka suna ta neman toshe wa kasashe masu tasowa hanyar samun ci gaba.

Ganin wannan yanayin da ake ciki ne, ya sa kasar Sin ta dau niyyar kafa wata sabuwar huldar kasa da kasa, wadda ta daukaka ra’ayin hadin gwiwa da samun moriya tare, gami da gabatar da shawarar kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Ayyukan kula da harkokin kasa da kasa ma suna bukatar a yi musu gyare-gyare, kana kasar Sin na ta kokarin samar da sauye-sauye da kwaskwarima kan tsare-tsaren duniya, ta yadda al’ummar dan Adam za ta dinga samun ci gaba. (Bello Wang)

CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya
Daga Birnin Sin

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Daga Birnin Sin

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Next Post
2023: Kotu Ta Aike Da Mawallafin Jaridar WikkiTimes Gidan Yari Kan Zargin Haifar Da Fitina

2023: Kotu Ta Aike Da Mawallafin Jaridar WikkiTimes Gidan Yari Kan Zargin Haifar Da Fitina

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.