Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC (Trade Union Congress), Kwamared Festus Osifo, ya bayyana cewa duk da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na rage farashin man fetur, har yanzu farashin ya yi wa ma’aikatan Nijeriya tsada sosai kuma ya fi ƙarfinsu.
Da yake bayyana matsayar ƙungiyar kan halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki, Osifo ya bayyana cewa ragin da bai wuce Naira 30 zuwa Naira 60 ba a kowace lita ba zai taɓa magance raɗaɗin matsin tattalin arziƙi ba, Ya jaddada cewa matuƙar litar mai na kan kusan Naira 1,000, har yanzu ya fi ƙarfin aljihun ma’aikaci da talakan ƙasar.
Shugaban na TUC ya jaddada cewa a halin yanzu, mafi yawan ma’aikata na kashe sama da rabin albashinsu ne kawai wajen biyan kuɗin motar zuwa aiki da komawa gida, lamarin da ya tilasta wa iyalai da dama shiga matsanancin ƙuncin rayuwa.
A saboda haka, Osifo ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta mayar da hankali kan matakai masu ɗorewa maimakon rage farashi na ɗan lokaci.
Ya buƙaci a hanzarta inganta matatun man cikin gida domin kawo ƙarshen dogaro da man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje, a faɗaɗa shirin motocin safa masu amfani da iskar gas (CNG), sannan a tabbatar da cewa dukkan jihohi da hukumomi sun aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi domin ƙarfafa ma’aikata su iya fuskantar tsadar rayuwa.














