ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Harin Iran: Amurka Da Isra’ila Sun Bata Lissafi

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Iran

Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hare-hare kan Iran ne bisa wai “wani matakin da ya dace don kawar da barazana.” Amma da yawa manazarta da suka san yankin Gabas ta Tsakiya da kuma musamman tarihin kasar Iran mai shekaru sama da 2000 da kafuwa, suna ganin cewa harin na iya zama kuskure ko batan lissafi, bisa tunanin yadda sakamakon da zai biyo baya na iya daukar tsawon shekaru ta fuskar zaman lafiya, matsin lambar diflomasiyya, da kuma kara hadarin matsalar tsaro.

Masu lura da al’amura sun lura cewa daya daga cikin manya-manyan kura-kurai shi ne tunanin cewa matakin soji zai raunana tsarin siyasar Iran. A maimakon haka, da alama harin ya karfafa ikon hukumomin Iran bisa kara dankon hadin kai a tsakaninsu da mabambantan sassan siyasa da suke da sabanin ra’ayi, da rage damar yin sulhu da kuma karfafa muryoyin masu kishin kasa da ke kara yekuwar nuna wa al’ummar kasar cewa wannan yakin na gwagwarmayar dorewar kasar ne. Don haka, ake ganin bin hanyar diflomasiyya ta gaskiya tare da Amurka zai yi matukar wahala. Ana iya samun maslaha amma ta wucin-gadi, amma babu zancen amincewa da juna.

Wani abin damuwa da masana yankin suka nuna shi ne girman ramuwar gayyar da take biyo bayan hare-haren. Martanin Iran, wanda ya hada da harba makami mai linzami da tattaro kungiyoyin kawance a duk fadin yankin Gabas ta Tsakiya, ya nuna irin karfin da wasu manazarta ke ganin Amurka da Isra’ila suna masa kallon reni. Kuma wannan ne zai zama silar kara fadada rikicin Gabas ta Tsakiya wanda tuni ya shafi kasashe da dama, lamarin da ke kara nuna fargabar barkewar fadan da zai dade ana yi yankin. Sannan wadanda suka haddasa fitinar ba su da wata taswirar kawo karshen lamarin ko takamaimiyar hanyar siyasar da za a bi.

ADVERTISEMENT

Abubuwan da ke faruwa sun zarce batun matakin sojin da aka dauka. Masu sharhi na ganin lamarin yana da illoli ta fuskar diflomasiyya, musamman ga Isra’ila, wadda a yanzu ke fuskantar karin matsin lamba daga kasashen duniya tun daga kan kisan kiyashinta na Gaza. Ga bangaren Amurka kuma, lamarin zai iya haifar mata da tutsu daga abokan hulda da ke fargabar wargajewar tsarin samarwa a kasuwar makamashi ta duniya da kuma sauran hanyoyin kasuwancin yanki. Kazalika, daukar matakin soji zai iya zama na dogon lokaci wanda hakan zai kara karkatar da hankali da albarkatun Amurka daga wasu abubuwan da ta sa gaba a duniya, kamar cike gibin kasuwanci da sauran matsaloli na cikin gida.

Trump ya yi yakin neman zabensa da cewa ba zai tsunduma Amurka cikin yaki na dogon lokaci ba a wa’adinsa. Amma yanzu ya saba lamba, kuma har manyan ’yan siyasar Amurka masu goyon bayan kudurinsa na siyasa irin su Marjorie Taylor Greene, Thomas Massie, Rand Paul, Turker Carlson da sauransu sun yi Allah wadai da yakin na Iran.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Kisan jagoran addini na Iran Ayatollah Khomeini wani babban kuskure ne a cikin wannan yakin saboda ba wai kai a matakin kasar Iran yake da tasiri ba, yana da dimbin mabiya wadanda za su iya sadaukar da rayukansu a sassan duniya daban-daban wajen neman daukar fansa. Kuma matukar zuciyar dan’adam take kashe a kan wani abu, to ba a san ranar samun mafita ba.

Kamar yadda Hausawa ke yawan fada, fitina bacci take, kuma Allah ya la’anci mai tayar da ita, muna fata wannan la’ana ta tsaya kan wadanda suka tayar ba tare da sauran al’ummar da ba-ta -ji-ba-ba-ta-gani ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Iran
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Iran
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

Next Post
Kafar CGTN Ta Fitar Da Rahoto Game Da Hasashen Ababen Mayar Da Hankali Yayin Manyan Taruka Biyu Na Sin

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.