ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hasashe Game Da Siyasar Nijeriya A 2027 (2)

by Sulaiman
8 months ago
vector illustration of Nigeria flag and map

vector illustration of Nigeria flag and map

Nan da shekara mai zuwa, wato 2027, Nijeriya za ta gudanar da zaɓe, wanda a tarihin kasar kamar ba a taɓa irinsa ba.

A makon da ya gabata, mun tattauna hasashen siyasar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

A wannan makon, za mu ci gaba da tattauna hasashen siyasar manyan ‘yan siyasa da taurarinsu za su haskaka a 2027.

ADVERTISEMENT

 

Atiku Abubakar 

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Atiku Abubakar yana ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasa a Nijeriya, wanda aka fi sani a matsayin Mataimakin Shugaban Nijeriya (1999–2007) da kuma wanda yafi kowa fitowa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jere.

An haife shi a ranar 25 ga Nuwamba, 1946, a Jihar Adamawa.

Ya fara aikin gwamnati a matsayin jami’in kwastam a Hukumar Kwastam ta Nijeriya.

Ya yi ritaya a ƙashin kansa a shekarar 1989 bayan ya kai matsayin Mataimakin Daraktan Kwastam, wanda hakan ya share masa fagen tsunduma cikin siyasa.

Ya zama mamba a Jam’iyyar PDP a shekarar 1998.

Ya taka muhimmiyar rawa a sauyin da Nijeriya ta samu daga mulkin soja zuwa dimokuraɗiyya.

An zaɓe shi Mataimakin Shugaban Nijeriya bayan ya lashe kujerar Gwamnan jihar Adamawa a shekarar 1999 a ƙarƙashin Shugaba Olusegun Obasanjo inda suka shafe wa’adi biyu tare daga 1999–2007.

Atiku Abubakar ya yi takarar shugabancin ƙasa sau da yawa, wanda hakan ya sanya shi ya zama na ɗaya a fitowa takara a jere a tarihin dimokuraɗiyya a Nijeriya:

1993 – Ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar SDP amma ya sauka daga baya.

2007 – Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar AC.

2011 – Ya yi takarar zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP sai dai ya sha kaye.

2015 – Ya yi takarar zaɓen fidda gwani a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, nan ma ya sha kaye a hannun marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

2019 – Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, duk da haka, ya ƙara shan kaye a hannun Buhari).

2023 – Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, ya sake shan kaye a hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A zaɓen da ke tafe na 2027, ya sake haɗa gagarumar adawa a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC don ƙalubalantar APC a zaɓen da ke tafe.

 

Peter Obi

Peter Obi na ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasa a Nijeriya a cikin shekaru 20 da suka gabata.

An haife shi a 19 ga Yuli 1961 a Onitsha, Jihar Anambra.

Ya fara siyasa a 2003, inda ya tsaya takarar gwamnan jihar Anambra a ƙarƙashin Jam’iyyar APGA.

Ya sha kaye a zaɓen a hukumance a hannun Chris Ngige na Jam’iyyar PDP, amma ya ƙalubalanci sakamakon a kotu. Bayan kusan shekaru uku ana gwabza shari’a, kotu ta soke zaɓen Ngige ta kuma ayyana Obi a matsayin wanda ya yi nasara. Ya hau mulki a ranar 17 ga Maris 2006.

Bayan hawa kujerar mulki, rashin jituwa ta kaure tsakanin ɓangaren zartarwa da na dokoki wanda hakan ya sanya majalisar dokokin jihar Anambra ta tsige shi a ranar 2 ga Nuwamban, 2006, ta maye gurbinsa da mataimakiyarsa, Virginia Etiaba, wacce ta zama gwamna mace ta farko a tarihin Nijeriya.

Obi ya yi nasarar ƙalubalantar tsige shi a kotu, inda kotun ta mayar da shi a ranar 9 ga Fabrairu, 2007.

Bayan taƙaddama kan tsawon lokacin da aka ɓata wurin shari’a kan lokacin da zai yi wa’adin mulki, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa, wa’adinsa na shekaru hudu zai fara ne daga ranar da aka rantsar da shi a watan Maris na 2006.

Wannan ya ba shi damar kammala cikakken wa’adinsa na farko.

An sake zaɓarsa a shekarar 2010 kuma ya yi gwamna har zuwa 17 ga Maris 2014, inda ya mika wa Willie Obiano mulki.

Da wannan, Obi ya yi Gwamnan jihar Anambra tun daga 2006-2014.

A zaben shugaban ƙasa na Nijeriya na 2019, an zaɓi Obi a matsayin mataimakin shugaban kasa ga Atiku Abubakar a karkashin jam’iyyar PDP.

Takarar Atiku-Obi sun sha kaye a hannun marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na APC.

Daga baya, Obi ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar Labour (LP) a shekarar 2022 bayan ya rasa tasiri a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na PDP.

Ya tsaya takarar Shugaban Nijeriya a zaɓen 2023 a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar LP tare da Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakinsa. Duk da cewa bai yi nasara ba, yaƙin neman zaɓensa ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda aka fi sa ido a kansu a tarihin Nijeriya inda matasa magoya bayan takararsu ake musu take da “Obidients.”

A shirye-shiryen zaɓen 2027, Obi ya sauya sheka zuwa sabuwar jam’iyyar adawa mai suna ADC domin ƙalubalantar jam’iyya mai mulki, APC.

Yayin da Peter Obi ya bayyana komawarsa jam’iyyar ADC, a matsayin jam’iyyar hadin gwiwar jam’iyyun adawa, don cimma burin siyasarsa a 2027. Har yanzu yana daga cikin wadanda taurarosu za ta haska a ciki siyasar Nijeriya. Ba kamar Atiku Abubakar ba, wanda ya a hukumance ya yi murabus daga PDP kuma ya karbi katin ADC a wani taron da aka gudanar, Obi ya sauya sheka ne daga jam’iyyar LP.

Babban abin mamaki shi ne, ko Obi zai amince ya zama mataimakin takarar Atiku. Ya bayyana cewa zai yi takarar shugaba kasa ne kawai, duk da haka yana ci gaba da zama a tebur daya da Atiku a tarurrukan jam’iyyar ADC. Akwai jita-jita cewa Obi yana jiran sakamakon gyaran tsarin mulki, musamman sabon jadawalin dokar zabe ta 2025, kafin ya tsai da shawara.

A lokuta da dama Obi ya ambata cewa zai kasance zai yi wa’adi mulki guda ne na shekara hudu wajen farfado da kasar. Duk da haka, bai fayyace ko wannan tayin wani bangare ne na yarjejeniya don samun goyon bayan Atiku ko kuwa alkawari ne na musamman ga masu zabe ba. Shirin Obi zai tabata ne a lokacin babban taron ADC da ake sa ran za a yi a farkon shekarar 2026.

Siyasar Nijeriya
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Yawan Hatsin Da Kasar Sin Ta Noma Ya Kai Wani Sabon Matsayi Na Koli A 2025

Yawan Hatsin Da Kasar Sin Ta Noma Ya Kai Wani Sabon Matsayi Na Koli A 2025

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.