ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukuncin Kotu Na Barazana Ga Zaben 2027 —INEC

by Yusuf Shuaibu
3 months ago
INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta yi gargadin cewa sabbin hukuncin kotu da suka shafi jadawalin tsare-tsaren ayyukanta na zaben 2027 na iya kawo cikas ga shirye-shiryen zaben idan ba a gaggauta warware su ba kan lokaci.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, shi ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron hukumar karo na biyu tare da shugabannin jam’iyyun siyasa a Abuja.

Amupitan ya bayyana cewa hukumar ta riga ta shiya daukaka kara kan hukunci biyu na manyan kotun tarayya wanda suka kalubalanci wasu lokuta da ke cikin jadawalin INEC na zaben 2027.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, duk da cewa hukumar tana girmama hukuncin kotuna, hukuncin yana tayar da tambayoyi ta shari’a game da iyakokin ikon INEC na tsarin mulki da na doka wajen tsarawa da daidaita ayyukan zabe.

Manyan kotunan tarayya da ke Abuja sun yanke manyan hukunci biyu da suka soke lokuta a cikin jadawalin zaben 2027 da INEC ta fitar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Kotunan sun yanke hukunci cewa a daidai lokacin da tsarin mulki ya bai wa INEC izinin fitar da jadawalin zabe, ba za ta iya amfani da ka’idojin gudanarwa don gajartawa ko karawa kan lokutan da dokar zabe ta 2026 ta tabbatar wa jam’iyyun siyasa ba.

Amma Amupitan ya bayyana cewa a shari’ar da jam’iyyar matasa ta shigar a kotu mai lamba ta No. FHC/ABJ/CS/517/2026, da aka yanke hukunci a ranar 20 ga Mayu, 2026, kotu ta kalubalanci wasu lokuta da ke cikin jadawalin hukumar da tsarin ayyukanta na zaben 2027.

Ya kara da cewa a cikin wani hukunci na daban da aka yanke a ranar 26 ga Mayu, 2026, a shari’ar mai lamba No. FHC/ABJ/CS/720/2026, wanda jam’iyyar SDP ta kai karar INEC a kotun, kan kotu ta tabbatar da ikon hukumar na fitar da jadawalin zabe amma ta soke wasu lokuta da suka shafi zaban ‘yan takara da maye gurbin ‘yan takara.

Shugaban INEC ya jaddada cewa ayyukan da ke cikin jadawalin hukumar suna da alaka da juna a matsayin hanyoyin aiki da aka tsara don tabbatar da gudanar da zabe cikin tsari da gaskiya da nasara.

Ya ce a yayin da dokar zabe ta tsara jaddawali don wasu ayyukan zabe da wasu muhimman tsare-tsare da dama ba a bayyana su a cikin doka ba, amma dole ne a hada su cikin dukkanin jadawalin zabe.

Duk da kalubalen shari’a, shugaban INEC ya tabbatar wa jam’iyyun siyasa da jama’ar Nijeriya cewa hkumarsa na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da zaben 2027 bisa ga dokokin kundin tsarin mulki da dokar zabe da duk wasu umarnin shari’a da suka inganta.

A yayin da yake magana, shugaban cibiyar hadakar jam’iyyu (IPAC), Dakta Yusuf Mamman Dantalle, ya ce cire tsarin zaben fitar da gwani kai tsaye daga tsarin zaben Nijeriya ya ba da gudummawa sosai ga rikice-rikice da tashin hankali da kalubalen gudanarwa da jam’iyyun siyasa suka fuskanta yayin zaben fitar da gwani da aka kammala kwanan nan.

INEC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Real Madrid Ta Kammala Ɗaukar Bernardo Silva Daga Man City

Real Madrid Ta Kammala Ɗaukar Bernardo Silva Daga Man City

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.