Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya bayyana cewa, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai bayar da gudunmwar da ya kai kaso 1 bisa 4 na ci gaban tattalin arzikin duniya a bana.
A cewar IMF, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai karu a bana, bisa la’akari da farfadowar harkokin kasuwanci biyo bayan saukaka matakan yaki da COVID-19, wanda zai bunkasa tattalin arzikin duniya. Haka kuma, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai karu zuwa kaso 5.2 a bana, idan an kwatanta da kaso 3 na bara. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp