ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dawo Da Tallafin Man Fetur Zai Dagula Tattalin Arziƙin Nijeriya – Shehu Sani

by Sadiq
2 weeks ago

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi gargaɗin cewa dawo da tallafin man fetur da Atiku Abubakar ya yi alƙawari zai iya jefa tattalin arziƙin Nijeriya cikin ƙarin matsala.

Sani ya bayyana alƙawarin Atiku na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a matsayin “yaudara”, yana mai cewa Nijeriya ba za ta iya komawa tsohon tsarin biyan tallafin ba.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, inda ya ce tsohon tsarin tallafin ya janyo asarar maƙudan kuɗaɗen gwamnati tare da ƙara matsalolin cin hanci da fasa-ƙwaurin man fetur.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, komawa tsarin zai ƙara wa gwamnati nauyin kashe kuɗi tare da rage kuɗaɗen da za a iya amfani da su wajen ayyukan raya ƙasa, kiwon lafiya, ilimi da sauran muhimman buƙatun jama’a.

Kalaman Sani na zuwa ne bayan Atiku ya ce ba zai janye shirinsa na dawo da tallafin man fetur ba domin sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya wahalar tsadar rayuwa ba.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Atiku ya bayyana cewa shirinsa zai mayar da hankali kan tallafa wa matatun mai na cikin gida da rage kuɗin samar da man fetur.

Sai dai Sani ya ce ya kamata a nemi wasu hanyoyin rage tsadar rayuwa ba tare da komawa tsohon tsarin biyan tallafin man fetur ba.

Muhawarar kan tallafin man fetur na daga cikin manyan batutuwan da ake sa ran za su mamaye yaƙin neman zaɓen 2027, musamman ganin yadda cire tallafin ya shafi farashin sufuri da kayayyaki a ƙasar.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga Tare Da Ceto Mutane 14 A Zamfara

Sojoji Sun Daƙile Harin 'Yan Bindiga Tare Da Ceto Mutane 14 A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.