Rundunar sojin Iran ta gargaɗi ƙasashen yankin Gulf kan haɗa kai da Amurka wajen shirya mata hare-hare.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa Ɗ, babban hafsan rundunar sojin ƙasar Iran, Ali Abdollahi ya ce “Ba zai yiwu a jibge ɗimbin jiragen yaƙi, musamman jiragen ɗaukar mai, a yankin ba tare da ƙasashen sun sun sani ba.”
Ya ce Iran za ta ɗauki duk wani “taimako” da aka bai wa sojojin Amurka a matsayin haɗa kai ko bayar da goyon baya ga dakarun Amurka.
ADVERTISEMENT
A tsawon lokacin yaƙi tsakanin Iran da Isra’ila tare da Amurka, Iran ta kai hare-hare sau da dama kan sansanonin soji da ke ƙasashen yankin waɗanda ke ƙawance da Amurka.














