ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iyayen Jaririya Mai Watanni 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna Sun Samu Ƴanci

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago
Kaduna

Magidanci Ahmed Abubakar Zakka tare da matarsa da jaririyarsu mai watanni shida a duniya mai suna Fatima, sun kuɓuta daga hannun ƴan bindigar da suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna bayan kwanaki tara suna tsare a daji. Majiyoyi sun tabbatar da cewa an sako iyalan ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, 2026, kuma tuni suka nufi cikin birnin Kaduna domin sake haɗuwa da ƴan uwansu.

Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanan yadda aka kuɓutar da su ko kuma an biya kuɗin fansa ba, wani tsohon jami’in tsaro mai ritaya wanda ya yi aiki tare da tawagarsa domin ganin an ceto su, ya tabbatar da labarin ga manema labarai.

Rahoton Daily Trust ya Jami’in ya nuna cewa ƙoƙarin tawagarsa da gudunmawar wasu mutane ne suka share fagen kuɓutar da su, inda ya ƙara da cewa iyalan na kan hanyarsu ta komawa gida a cikin motarsa tare da direbansa.

ADVERTISEMENT

Bayanai dai sun nuna cewa ƴan bindigar sun sace Zakka da matarsa da jaririyarsu ne daga gidansu da ke rukunin gidaje na Alrahus Estate a yankin Millennium City, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, a ranar 6 ga watan Oktoba, 2026. Ma’auratan, waɗanda aka bayyana a matsayin marayu, sun shafe kusan shekaru shida da aure ba tare da samun haihuwa ba har sai kwanan nan da suka haifi Fatima.

Sace iyalan ya haifar da gagarumar fargaba da fushin al’umma a faɗin ƙasar, biyo bayan watsuwar wani faifan bidiyo mai ban tausayi a kafafen sada zumunta. Bidiyon ya nuna jaririyar Fatima tsirara tana kuka mai tsanani a hannun mahaifinta, yayin da wani ɗan bindiga ya saita bindiga a kansa a yayin da ma’auratan ke roƙon a ji ƙansu tare da kiran hukumomi da jama’a su kawo musu ɗauki.

LABARAI MASU NASABA

Shirin Tinubu Na Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 20.5 Ya Tabbatar Da Hasashena – Atiku

Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

Kuɓutar da iyalan ta kawo gagarumin sauƙi da farin ciki ga ƴan uwa da ɗaukacin ƴan Nijeriya da suka shafe kwanaki suna gudanar da addu’o’i da matsin lamba ga jami’an tsaro domin ceto su, a daidai lokacin da al’ummomin yankin Chikun ke ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ƴan bindiga.

Kaduna
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata
  • Abubakar Sulaiman
    ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

MASU ALAKA

EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Zarge-Zargen Cin Hanci Kan Atiku
Siyasa

Shirin Tinubu Na Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 20.5 Ya Tabbatar Da Hasashena – Atiku

October 28, 2026
Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna
Manyan Labarai

Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

October 28, 2026
Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda
Manyan Labarai

Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

October 27, 2026
Next Post
Tinubu Ya  Yabi  Hular Abba, Ya Bayyana Ma’anar Tambarin Da ke Jikinta

Tinubu Ya Yabi Hular Abba, Ya Bayyana Ma’anar Tambarin Da ke Jikinta

LABARAI MASU NASABA

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

October 28, 2026
Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

October 28, 2026
EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Zarge-Zargen Cin Hanci Kan Atiku

Shirin Tinubu Na Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 20.5 Ya Tabbatar Da Hasashena – Atiku

October 28, 2026
2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

October 28, 2026
Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

October 28, 2026
Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2026
An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

October 27, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

October 27, 2026
ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

October 27, 2026
An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

October 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.