Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da hular Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya ce tambarin sarƙar da ke jikin hular na ɗauke da saƙon ’yanci da samar da ci gaba.Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2027 a Banquet Hall da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.
A yayin taron, Abba Yusuf ya bayyana cikin jerin manyan ’yan jam’iyyar APC da suka halarci taron, sanye da hula mai launin Ja dake da duhu, wanda a jikinta aiwai tambarin Sarƙar wanda ya zama ɗaya daga cikin alamomin da ake danganta shi da siyasar Tinubu.
Da yake magana kan hular, Tinubu ya nuna cewa abin da ya fi jan hankalinsa shi ne ma’anar tambarin, ba kawai kalar ko salon hular ba. Rahoton Voice of Nigeria ya ce shugaban ya bayyana tambarin a matsayin alamar ƙudurin shawo kan matsalolin da suka daɗe suna kawo cikas ga ci gaban al’umma.
A cewar bayanin da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnatin Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Tinubu ya danganta tambarin da aiki tuƙuru da tsame mutane daga ƙangin talauci, jahilci da rashin tsaro, yana mai cewa waɗannan na daga cikin manyan matsalolin da ke fuskantar Najeriya.
Bayan taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin cikinsa kan yadda Tinubu ya fahimci ma’anar tambarin da ke jikin hular. Ya kuma sake bayyana goyon bayansa ga shugaba Tinubu na neman wa’adin mulki na biyu, yana cewa komawarsa jam’iyyar APC an yi ta ne da niyyar bayar da gudummawa wajen nasarar Shugaban Ƙasar a zaɓen 2027.














