Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Luanda, babban birnin Angola, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Taron Gaggawa na 21 na Majalisar Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin Tarayyar Afirka (AU).
Taron na manyan shugabannin Afirka zai mayar da hankali ne kan dabarun warware rikice-rikice da kuma inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a faɗin nahiyar.
Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya bayyana cewa Shettima zai haɗu da shugabannin Afirka da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da ƙarfafa matakan hana rikice-rikice.
Ana sa ran Nijeriya za ta taka muhimmiyar rawa a tattaunawar, kasancewar ƙasar na daga cikin waɗanda ke da gogewa wajen shiga ayyukan samar da zaman lafiya da sasanta rikice-rikice a Afirka da sauran sassan duniya. Taron zai kuma tattauna hanyoyin ƙarfafa tsarin nahiyar na hana rikice-rikice, da warware taƙaddama da tabbatar da zaman lafiya.
Shettima, wanda ya tafi tare da manyan jami’an tsaro da na Sojoji, zai gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a taron, inda zai bayyana matsayin Nijeriya kan batutuwan da ake tattaunawa tare da sake jaddada aniyar ƙasar na tallafa wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka.
Bayan kammala ayyukansa a Angola, ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai dawo Nijeriya.














