Jami’an tsaro a Jihar Sokoto sun samu nasarar cafke wani mutum da ake zargi da kasancewa ɗan bindiga, ɗauke da wata akuya da ake zargin ya sato ta ne a yayin da yake ƙoƙarin wucewa da ita a Gidan Madi da ke ƙaramar hukumar Tangaza.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a yayin wani aikin sintiri da jami’an tsaron suka gudanar a wani yankin jihar, bayan nuna shakku a kan yadda yake tafiyar da dabbar ba tare da wata gamsasshiyar hujjar mallakarta ba.
Binciken farko da jami’an suka gudanar ya nuna cewa mutumin yana da alaƙa da ayyukan ƴan bindiga da ke addabar al’ummomin karkara a jihar, inda kuma aka ƙwace dabbar domin gano ainihin mai ita bayan kammala tantancewa.
Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da kama wanda ake zargin, tana mai bayyana cewa yana tsare a sashin binciken manyan laifuka inda ake ci gaba da yi masa tambayoyi domin gano sauran abokan harƙallarsa da maɓoyar sauran dabbobin da aka sace.
A ƙarshe, hukumar tsaron ta buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da sanya idanu da kuma sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko mutum da ba a aminta da shi ba a unguwanni da kasuwannin dabbobi, domin dakatar da ayyukan ɓata-gari da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.













