ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyun Adawa A Nijeriya Sun Amince Da Tsayar Da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Guda A 2027 — Turaki

by Muhammad
5 months ago

Jam’iyyun adawa a Nijeriya sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda domin zaɓen 2027, kamar yadda Kabiru Tanimu Turaki, shugaban ɓangare na jam’iyyar PDP, ya bayyana a ranar Asabar.

Turaki ya bayyana hakan ne a taron ƙolin jam’iyyun adawa na ƙasa da aka gudanar a Ibadan, inda shugabannin jam’iyyun siyasa daban-daban suka hallarta domin tsara dabarun siyasa gabanin zaɓen 2027.

Ya ce wannan matsaya na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan jam’iyyun adawa domin ƙara samun damar cin zaɓe, musamman a daidai lokacin da ya ce jam’iyyar APC ke ƙoƙarin tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zama ɗan takara ba tare da ƙalubale ba a 2027.

ADVERTISEMENT

A cewarsa: “Duk da matsin lamba da dabarun da APC ke yi domin ganin Shugaba Tinubu ya zama ɗan takara shi kaɗai a 2027, mu za mu tsayar da ‘yan takara kuma mu fafata a zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓe.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyun adawa sun yanke shawarar haɗa kai a kan ɗan takara guda.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

“Mun amince cewa za mu yi aiki domin tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a 2027, wanda dukkan jam’iyyun adawa za su mara masa baya domin ceto ƙasa da jama’arta,” in ji shi.

Taron ya kuma fitar da buƙatar a yi wa shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Joash Ojo Amupitan, murabus kan zargin nuna son kai ga jam’iyyar APC.

A cewar shugabannin adawar, ci gaba da kasancewar Amupitan a kan muƙaminsa na iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe tare da ƙara zafafa rikicin siyasa gabanin 2027.

Sun ce: “Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya nuna son kai ga APC, bai kamata ya jagoranci zaɓen 2027 ba, domin jama’a sun rasa amincewa da shi wajen gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.”

Taron ya samu halartar fitattun ‘yan siyasa na adawa ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, inda aka tattauna kan haɗin kai, gyaran tsarin zaɓe, da kuma matsalolin tattalin arziki da tsaro da ake fuskanta a ƙasar.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Gwarzo Na Shirin Sake Fitowa Domin Kawo Sabbin Salon Siyasa A Kano

Gwarzo Na Shirin Sake Fitowa Domin Kawo Sabbin Salon Siyasa A Kano

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.