ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: IBB Ya Bai Wa Shugaban PDP Satar Amsar Yadda Zai Jagoranci Jam’iyyar Har Ya Yi Nasara

by Leadership Hausa
9 months ago
Ibb

Tsohon shugaban ƙasan Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya buƙaci sabon shugaban jam’iyyar PDP, Kabiru Turaki, da ya sake gina jam’iyyar ta hanyar gyara kurakuran da aka yi a baya kuma ya samar da daidaito a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

IBB ya ba da wannan shawarar ne lokacin da Turaki da wasu zaɓaɓɓun mambobin kwamitin zartarwa na PDP suka kai masa ziyara a gidansa na Hilltop da ke garin Minna, babban birnin Jihar Neja.

  • Abiola Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 12 Ga Watan Yuni 1993 – Janar IBB
  • Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Rahotanni sun bayyana cewa a ganawar sun tattaunawa kan sabunta jam’iyyar da samar da daidaino da kwanciyar hankali da buƙatar ƙarfafa tsare-tsaren siyasa a faɗin ƙasar nan.

ADVERTISEMENT

Tsohon shugaban sojan ya yaba wa shugabancin jam’iyya saboda ta yi daidaito da tsarin gwamnati da mutanen Jihar Neja a lokacin da ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin lokuta mafi wahala tare da sake tabbatar da ƙarfin jam’iyyar PDP a ƙasa nan.

A cewarsa, PDP ta kasance jam’iyyar siyasa mafi ƙarfi a tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya, ya tuna irin ƙoƙarin da ya yi a baya na kafa tsarin jam’iyyu biyu, wanda ƴan siyasa suka ƙi yarda da shi.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Babangida ya yi kira ga Turaki da ya fifita dabara, yin shawara da shugabanci mai ratsa kowa yayin da yake fara sake gina jam’iyyar.

“Yayin da kake magana a baya, ka amince cewa jam’iyyar ta yi kuskure kuma ta riga ta ƙaddamar da hanyoyi don gyara su. Ina roƙonka ka yi amfani da hikima, ka nemi ra’ayoyin mutane, kuma ka yi aiki wajen gina jam’iyya da samar da zaman lafiya da ci gaba. Kana da ƙarfin yin hakan, kuma ina maka fatan alheri,” in ji shi.

Don nuna tsawon tasirin tsarin jam’iyyu a Nijeriya, tsohon shugaban ƙasa ya bayar da labari game da wani jami’in soja da ya taɓa naɗawa a Jihar Nija, wanda bai san cewa gwamnatin soja ya amshe mulkin Nijeriya ba, kuma ya nace cewa yana biyayya ga shugaba Shehu Shagari da jam’iyyar NPN mai mulki a lokacin ba. Babangida ya ce lamarin ya nuna yadda jam’iyyun siyasa suke matuƙar ɗauke hankalin al’umma.

A cikin jawabinsa, Turaki ya nuna godiya ga kyakkyawar niyya da jagoranci na Babangida, yana cewa PDP za ta ci gaba da amfana da ƙwarewarsa na jagoranci da fahimtarsa ta tarihi kan ci gaban siyasar Nijeriya.

“Mun himmatu wajen sake gyara wannan jam’iyya da sake haɗe dukkan ɓagarorinta wuri ɗaya da dawo da ruhun jam’iyyar domin samun nasara kafin zaɓen 2027,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa tawagar ta shirya wannan ziyara ta musamman don nuna godiya ga Babangida da kuma yin jaje kan garkuwa da mutae da aka yi kwanan nan a Jihar Neja ya sa ya zama dole a haɗe ziyarar da yin ta’aziyya.

Ibb
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Kujerar Shugaban Ƙasa Nake Buƙata A 2027 Ba Mataimaki Ba – Amaechi

Kujerar Shugaban Ƙasa Nake Buƙata A 2027 Ba Mataimaki Ba – Amaechi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.