Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya roƙi ƴan Nijeriya da kada su yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuɗin-goro da zargin ayyukan da suka auku shekaru 33 da suka gabata.
Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake yunƙurin sakin wasu takardu da ake zargin suna da alaƙa da binciken fataucin miyagun ƙwayoyi da ya shafi shugaban ƙasar, lamarin da Buratai ya ce bai kamata a bar shi ya bata sunan Nijeriya a idon duniya ba.
A cikin wata takarda da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi mai taken “Nijeriya a Gaba,” ya jaddada cewa wannan batu ya wuce shugaban ƙasa a matsayinsa na mutum ɗaya, domin lamari ne da ya shafi kimar ƴan Nijeriya miliyan 250 da kuma tattalin arzikin ƙasar. Idan ba a manta ba, wata kotu a Amurka ta ba wa Tinubu, FBI, da Ma’aikatar Shari’a wa’adin zuwa 28 ga watan Agustan 2026 don gabatar da dalilansu kan hana sakin wadannan takardu.
Buratai ya nuna takaicinsa kan yadda za a bari wata kotun ƙasar waje ta yanke hukunci kan halayyar shugaban da ƴan Nijeriya miliyan da dama suka zaɓa, inda ya ce hakan zai iya zama tamkar katsalandan cikin harkokin siyasar Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da zaben 2027 da ke tafe.
Tsohon hafsan sojan ya tambayi ko akwai wani dan Najeriya da zai ce shi ne mutumin da yake a shekaru 33 da suka wuce, inda ya kara da cewa kamata ya yi a duba irin gudunmawar da Tinubu ya bayar, tun daga lokacin da ya zama gwamnan jihar Legas har zuwa shigarsa siyasar kasa.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta warware matsalar ta fuskar diflomasiyya, tare da roƙon lauyoyin shugaban ƙasa da su dage wajen kare a saki wadannan takardu domin kiyaye mutuncin ofishin shugaban ƙasa da kuma martabar Nijeriya.














