Lokacin da ya siffanta abokantakar dake tsakanin Sin da Afirka, babban jami’in kasar jamhuriyar Nijar Ibrahim Manzo Diallo, ya ambaci karin magana da na yiwa wannan rubutu take da shi.
Alhaji Ibrahim Manzo Diallo, shugaban kwamitin sa ido kan ayyukan watsa labaru na kasar Nijar, yana halartar taron dandalin hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka karo na 7 a birnin Beijing na kasar Sin. Yayin da nake hira da shi, ya ce yadda shi da dimbin wakilan kafofin yada labarai na kasashen Afirka suka samu gayyata zuwa kasar Sin, don halartar wannan kasaitaccen biki, shaida ce ta zumuntar dake tsakanin Sin da Afirka.
Ta yaya za a iya karya babakere da kasashen yamma suke yi ta fuskar aikin yada labarai a duniya? Wannan tambaya ce da Alhaji Ibrahim Diallo ke kokarin neman amsarta. A cewarsa, a baya kasashen yamma sun dade suna shawon kan kafofin yada labarai na kasar Nijar. Amma bayan da kasar Sin ta fara watsa shirye-shiryen rediyo da yaren Hausa da sauran harsunan Afirka, gami da wani salon yada labarai da ya sha bamban da na kasashen yamma, jama’ar kasar Nijar sun rika samun labarai na gaskiya. Hakan ya shaida muhimmancin hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren watsa labarai. Haka zalika, ya kara da cewa, ko da yake kasashen yamma sun dade suna kokarin shafa wa kasar Sin kashin kaji, amma ‘yan Afirka sun san wace ce sahihiyar abokiyarsu. Duk wanda ke neman bata huldar dake tsakanin Sin da Afirka, to, ba ya son ganin ci gaban kasar Sin, gami da na kasashen Afirka, in ji shi.
Ban da haka, a ganin Alhaji Ibrahim Diallo, akwai alaka tsakanin ci gaban fasahohin yada labarai da zamanantarwar wata kasa. Ya ce, kasar Sin ta yi nisa a fannin kula da sabbin dandamalin yada labarai, irinsu shafin yanar gizo na sada zumunta, da kafar watsa labarai ta kai, da dai makamantansu. Ya ce yana son komawa Nijar tare da fasahohin kasar Sin, don matasa su fahimci cewa, ban da ba da damar yin zage-zage da nuna fushi, sabon dandalin yada labarai na da daraja a fannin raya kasa da zaman al’umma. Alhaji Ibrahim Diallo, ya ce yana fatan ganin matasan kasashen Nijar da Sin sun karfafa cudanya a fannin aikin watsa labarai, ta yadda za su samu karin ilimi, da samar da karin gudunmowa ga ci gaban kasashensu.
Kana duk a wajen taron dandalin hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka na wannan karo, na yi hira da Raymond Dokpesi, shugaban kamfanin watsa labarai na DAAR na kasar Najeriya. Ya ce shekarar bana da ta kasance shekarar cudanyar mutane da al’adu tsakanin Sin da Afirka, tana da matukar ma’ana. Ya ce, kasar Sin daya ce daga cikin manyan abokan hulda na kasar Najeriya mafiya samar da tasiri a duniya. A matsayinta na wata babbar kasa mai karfin tattalin arziki, kasar Sin ta nuna wa Najeriya, da sauran kasashen dake nahiyar Afirka wata sabuwar hanyar raya kai, wadda ta sha bamban da tsohuwar alakar mulkin mallaka da aka samu tsakanin kasashen yamma da na Afirka, da sa kaimi ga sauye-sauyen da ake samu a nahiyar Afirka, musamman ma a fannonin siyasa da tattalin arziki. Yanzu dukkan bangarorin Sin da Najeriya na son ganin an habaka hadin gwiwa da ake yi tsakanin gwamnatocinsu zuwa tsakanin al’ummun kasashen 2, da sanya jama’arsu fahimtar juna da kaunar juna. A kokarin neman cika wannan buri, Mista Raymond ya ba da shawarar gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarorin Najeriya da Sin, wajen tsara shirye-shiryen bidiyo wadanda za su yi bayani kan alakar Sin da Afirka a tarihinsu.
Wadannan mutanen biyu da na yi hira da su, sun zo daga Najeriya da Nijar, kasashe 2 daga cikin kasashe 45 dake nahiyar Afirka masu halartar taron dandalin hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka na wannan karo. Duk da haka, maganarsu tana iya wakiltar ra’ayin galibin manyan baki ‘yan Afirka da suka halarci taron, wanda shi ne darajanta zumuntar dake tsakanin Afirka da Sin, da sa ran samun karin sakamako a hadin gwiwar bangarorin 2. Sai dai ta yaya kafofin yada labaru na Sin da Afirka za su karfafa hadin kansu a nan gaba? Manyan baki masu halartar taron na wannan karo, sun ambaci yadda za a karfafa hadin gwiwa wajen tsara wasannin kwaikwayon da ake watsawa a wayar salula, da amfani da kirkirarriyar basira ta AI, da cudanya tsakanin manyan jami’ai, da matsasa, da dai sauransu. A zahiri, kafofin yada labarai za su ci gaba da taka muhimmyar rawa a fannin karfafa cudanya tsakanin al’ummun Sin da Afirka, da tabbatar da ci gaban bai daya na bangarorin biyu. (Bello Wang)














