ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Da Wasu Jiga-jigan APC Sun Samu Tikitin APC Ta Hanyar Sulhu

by Shehu Yahaya and Sulaiman
4 months ago
APC

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Dahiru Liman; da Mataimakin Shugaban Majalisar, Magaji Henry Danjuma, tare da shugabar Masu Rinjaye ta Majalisar, Munira Suleiman Tanimu, sun zama ‘yan takarar Jamiyyar (APC) domin wakiltar mazabunsu bayan gudanar da tantancewar sulhu a sassa daban-daban na jihar.

An tabbatar da Hon. Dahiru Liman a matsayin ɗan takarar APC na mazabar Makera bayan an gudanar da zaɓen sulhu da ya samu halartar shugabannin jam’iyya, jami’an zaɓe da magoya baya.

Da yake bayyana sakamakon, jami’in tattara sakamakon zaɓen, Injiniya Ezekiel Samuel Gode, ya ce Liman ya zama ɗan takara ba tare da hamayya ba bayan amincewa da shi a matsayin ɗan takarar sulhu guda ɗaya na mazabar.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Bayan karɓar sakamakon tabbatarwa daga rumfunan zaɓe guda biyar, kuma babu wani ɗan takara da ya tsaya takara tare da shi, ina ayyana Hon. Liman Tahiru a matsayin wanda aka tabbatar kuma aka dawo da shi a matsayin ɗan takarar APC na mazabar Makera.”

Haka zalika, Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Barr. Magaji Henry Danjuma, ya samu tikitin APC na mazabar Kagarko bayan mambobin jam’iyyar daga gundumomi daban-daban sun tabbatar da takararsa ba tare da hamayya ba.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Jami’in zaɓen APC, Abdulrahman Ibrahim Apo Jere, ne ya sanar da nasarar Danjuma a cibiyar tattara sakamakon ƙaramar hukumar bayan kammala tsarin tabbatarwar.

Ita ma Shugabar Masu Rinjaye ta Majalisar, Hon. Munira Suleiman Tanimu, ta samu tikitin APC na mazabar Lere ta Gabas bayan an gudanar da zaɓen sulhu cikin lumana a gundumomi shida na mazabarta.

Jami’in zaɓen mazabar Lere ta Gabas, Hon. Aminu Yaro, ya sanar da ita a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar bayan kammala zaɓen da aka gudanar a Saminaka.

A wani mataki da ake ganin na ƙarfafa haɗin kan jam’iyya gabanin zaɓen shekarar 2027, wasu masu neman takarar kujerun Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a ƙarƙashin APC sun janye daga takara tare da bayyana goyon bayansu ga ‘yan takarar sulhu na jam’iyyar.

Da yake jawabi a madadin waɗanda suka janye a Kaduna, Dakta Abdulrazaq Shuibu Labbo, mai neman takarar mazabar Kaka/Gogi ta Birnin Gwari, ya ce sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da shiga tsakani da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi domin tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyar.

APC
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
APC
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Kawancen Sin Da Rasha Na Kara Tabbatar Da Amincincewa Da Junansu A Duniya

Kawancen Sin Da Rasha Na Kara Tabbatar Da Amincincewa Da Junansu A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.