ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Mercedes Zai Shigar Da Osimhen Kara Kan Rashin Biyan Bashi

by Abba Ibrahim Wada
2 months ago
Mercedes

An ruwaito cewa kamfanin kera motoci na kasar Jamus Mercedes-Benz ya shigar da dan wasan tawagar Nijeriya da Galatasaray Bictor Osimhen kara a gaban wata kotu dake kasar Italiya kan zargin rashin kammala biyan kudin wata motar da ya saya a lokacin zamansa a kungiyar kwallon kafa ta Napoli.

A halin yanzu Osimhen yana daya daga cikin ‘yan wasan gaba mafi kwarewa a kwallon kafa a Duniya, ya taka leda a manyan kasashen Turai da suka hada da Belgium, Faransa, Italiya, da kuma Turkiyya, duk da haka, manyan nasarorin da ya samu sun zo ne a lokacin da ya lashe gasar Serie A ta kasar Italiya da kuma gasar Süper Lig ta kasar Turkiyya, inda ya lashe gasar tare da kungiyoyin Napoli da Galatasaray, bi da bi.

A lokacin zamansa na shekaru hudu da Napoli, Osimhen ya jagoranci kungiyar wajen lashe gasar Scudetto a karon farko cikin kusan shekaru 40, saboda wadannan nasarorin, komawarsa Galatasaray a bazarar da ta gabata ya sa ya zamo dan wasan da ya fi kowane dan wasan karbar albashi a tarihin gasar ta kasar Turkiyya da ake kira Turkish Süper Lig.

ADVERTISEMENT

Tauraron Super Eagles din a halin yanzu yana samun Yuro miliyan 20 a kowace shekara a matsayin albashi a Galatasaray, Osimhen ya samu yabo saboda ayyukansa na taimakon jama’a, yana yawan tallafa wa iyali, abokai, har ma da wadanda bai sani ba a shafukan sada zumunta, a karshen makon da ya gabata, ya dauki nauyin wasu magoya bayan Nijeriya domin su halarci wasan da Galatasaray ta doke kungiyar Fenerbahce da ci 3-0.

A cewar wani rahoto da jaridar Napolista ta fitar, Mercedes-Benz ta sanar da hukumomin Italiya game da bashin da take bin Osimhen, kamfanin ya yi ikirarin cewa Osimhen ya gaza kammala biyan kudin da ya sayi wata mota a shekarar 2023 kuma ya ki ya dawo da motar bayan ya kasa biya, sakamakon haka, ana zargin cewa dan wasan gaban mai shekaru 27 ya tara bashin Yuro 90,000 (kimanin Naira miliyan 142), wannan lamari ya bai wa mutane da dama mamaki ganin cewa albashin Osimhen na mako-mako ya zarce wannan adadin tun lokacin da ya lashe gasar Serie A.

LABARAI MASU NASABA

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

Lionel Messi Ya Kafa Tarihin Wanda Yafi Kowa Zura Kwallaye A Tarihin Gasar Cin Kofin Duniya

Kwanan nan ya nuna tarin motocin dake cikin garejinsa wanda ya kunshi Lamborghini biyu, Rolls-Royce, da Mercedes-Benz—wadda watakila ita ce wadda ake magana a kai, zuwa yanzu dai wakilan Osimhen ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, watakila dan wasan zai nemi warware matsalar da sauri domin ya mayar da hankali wajen taimaka wa kungiyarsa lashe kofin Super Lig na bana.

Mercedes
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Ɗanwasa Thomas Partey Ya Yi Rashin Nasara A Kotun Canada
  • Abba Ibrahim Wada
    FIFA Za Ta Biya Omar Artan Alawus Ɗin Da Za A Bai Wa Kowanne Alƙalin Wasa
  • Abba Ibrahim Wada
    Duk Da Rashin Halartar ‘Super Eagles’ Gasar Kofin Duniya, Nijeriya Ba Ta Rasa Wakilai Ba
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye Wakilan Afirka A Kofin Duniya?

MASU ALAKA

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino
Wasanni

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

June 24, 2026
Lionel Messi Ya Kafa Tarihin Wanda Yafi Kowa Zura Kwallaye A Tarihin Gasar Cin Kofin Duniya
Wasanni

Lionel Messi Ya Kafa Tarihin Wanda Yafi Kowa Zura Kwallaye A Tarihin Gasar Cin Kofin Duniya

June 22, 2026
Ɗanwasa Thomas Partey Ya Yi Rashin Nasara A Kotun Canada
Wasanni

Ɗanwasa Thomas Partey Ya Yi Rashin Nasara A Kotun Canada

June 21, 2026
Next Post
Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

ADC: Kwankwaso Ya Musanta Jita-jitar Ficewa Daga Jam’iyyar, "Har Yanzu Bai Yanke Hukunci Ba"

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.