ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Da Rashin Halartar ‘Super Eagles’ Gasar Kofin Duniya, Nijeriya Ba Ta Rasa Wakilai Ba

by Abba Ibrahim Wada and Sulaiman
3 weeks ago
Super Eagles

Duk da cewa tawagar Super Eagles ta Nijeriya ba ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 da aka fara daga ranar 11 ga watan Yuni ba a Amurka da Canada da kuma Meɗico.

Amma za a iya cewa ba a bar Nijeriya a baya ba wajen samun wakilai a gasar ta duniya. Bisa ƙididdiga, ƴan wasa 16 ƴan asalin Nijeriya ne za su wakilci ƙasashe dabandaban a tsakanin ƙasashe 48 a karon farko a tarihin gasar.

Kenan za a iya cewa rasa samun damar shiga gasar da Nijeriya ta yi ta bana, bai hana ta samun ƴan ƙwallonta da za su wakilce ta a babbar gasar ta duniya ba.

ADVERTISEMENT

Nijeriya tana da wakilci na daban a gasar wanda ba a kan sunan ƙasa kai tsaye bane amma ta hanyar ƴan ƙwallo fiye da 16 masu asalin Nijeriya da za su wakilci ƙasashe tara dabandaban a gasar da ake yi a yanzu. Wannan yana nuna yadda ƴan wasan Nijeriya suka bazu a faɗin duniya, suna taka rawa a manyan liglig na Turai da Amurka, har ma sun kai matakin wakiltar ƙasashen da suka taso ko suka girma a cikinsu.

Ga Sunayen ƴan Nijeriya guda 16 da suke wakiltar wasu ƙasashen a gasar kofin duniya

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira

Argentina Ta Kai Zagayen Kwata Fainal Bayan Nunawa Egypt Ƙwanji

Ingila: Babbar cibiyar ƴan Nijeriya a gasar kofin duniya. Ingila ce ƙasar da ke da mafi yawan ƴan Nijeriya a wannan jerin. A nan za a ga wasu manyan taurari da suka yi fice a gasar Premier League: Bukayo Saka (Arsenal) An haifi ɗan wasa Bukayo Saka a Ingila, amma iyayensa ƴan Nijeriya ne daga ƙabilar Yarabawa.

Eberechi Eze (Arsenal) An haifi ɗan wasan a Ingila, amma iyayensa ƴan Nijeriya ne kuma yana ɗaya daga cikin ƴanwasan da kociyan tawagar Ingila, Thomas Tuchel ya gayyata domin buga gasar cin kofin na duniya.

Noni Madueke (Arsenal) Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ne kuma kamar Saka da Eze, an haife shi a Ingila, amma iyayensa daga Nijeriya suke daga ƙabilar Igbo.

Waɗannan ƴan wasa sun riga sun zama ginshiƙai a cikin tawagar Ingila da Arsenal, kuma suna daga cikin manyan sunaye da ake dogaro da su a gasar a daidai wannan lokaci.

Faransa:

Michael Olise (Bayern Munich), An haifi Olise a Ingila, kuma mahaifinsa ɗan Nijeriya ne da kuma mahaifiyarsa daga Aljeriya  ya samu damar wakiltar ƙasa uku da ya haɗa da Ingila da Nijeriya da kuma Faransa, hakan ya sa ya zabi buga wa tawagar Faransa wasa.

Ɗan wasan ya buga wasa tun farko a tawagar matasan Faransa da wakiltarta a gasar gujeguje da tsalletsalle ta Olympic, yanzu yana cikin babbar tawagar ƙasar a gasar cin kofin duniya. Tuni kuma Olise ya zama ɗaya daga cikin sabbin taurari da ke bai wa Faransa ƙarin ƙarfi a gurbin kai harehare a tawagar.

Jamus:

Jamal Musiala (Bayern Munich). An haifi ɗan wasan a birnin Stuttgart a Jamus, yana da fasfo biyu da yake riƙe da shi na Jamus da na Ingila. Tushen kuwa mahaifiyarsa ƴar Jamus ce da kuma mahaifinsa ɗan Nijeriya da kuma Ingila. Ya fara buga wa matasan Ingila wasa kafin daga baya ya zabi Jamus.

Musiala musamman ya zama ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa a Bundesliga, kuma yana daga cikin matasan da ake ganin za su iya canza wasa a kowane lokaci.

Feliɗ Nmecha (Borussia Dortmund). An haifi Feliɗ a birnin Hamburg a Jamus, kuma mahaifiyarsa daga Jamus take da mahaifinsa ɗan Nijeriya yana kuma da tsatson Ingila, ya kuma samu damar wakiltar Jamus ko kuma Ingila, wanda ya fara buga wasa a matasan Ingila daga baya ya sauya ya koma buga wasa a Jamus.

Austria: Dabid Alaba (Real Madrid). Yanzu ya bar Real Madrid, bayan da kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen kakar da aka kammala ta bana. Alaba yana wakiltar Austria, wanda aka haifa a birnin Ɓienna, shi ne ma kyaftin ɗin tawagar ƙasar. Mahaifinsa ɗan Nijeriya ne da kuma mahaifiyarsa daga Philippines.

Alaba ya shahara musamman a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun masu tsaron baya a duniya, sai dai kuma ya yi fama da jinya, wataƙila wannan ce gasar kofin duniya ta ƙarshe da zai halarta.

Carney Chukwuemeka (Borussia Dortmund). An haifi Carney a birnin Ɓienna a Austria, kuma mahaifansa daga Nijeriya, ya fara buga wasa a matasan Ingila daga baya ya sauya zuwa buga wa babbar tawagar Austria wasa.

Switzerland:

Manuel Akanji (Manchester City) Tun farko Akanji ya samu damar wakiltar Switzerland ko kuma Nijeriya, an haife shi a birnin Wiesendangen garin mahaifiyarsa a Switzerland, mahaifinsa kuwa daga Nijeriya. Sai dai Switzerland yake yi wa wasa tun daga matasa har zuwa babbar tawagar ƙasar. Akanji yana daga cikin ginshiƙin masu tsaron bayan Manchester City, kuma yana taka muhimmiyar rawa a tawagarsa.

Noah Okafor (AC Milan), shima ɗanwasan an haife shi ne a birnin Binningen a Switzerland, wanda mahaifinsa daga Nijeriya yake. Ya fara buga wa babbar tawagar ta Switzerland wasa tun daga shekarar 2019.

Amurka:

Folarin Balogun (AS Monaco). Ɗan wasan ya samu damar wakiltar Amurka ko kuma Ingila, wanda aka haifa a birnin New York, amma a Ingila ya girma, iyayensa ƴan Nijeriya ne. Ya fara buga wa babbar tawagar Amurka wasa daga shekarar 2023.

Canada:

Tani Oluwaseyi (Minnesota United). Shima wannan ɗan wasan ya samu damar wakiltar Super Eagles ko kuma Canada. An haife shi a babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, amma sai iyayensa suka koma Canada suka zauna a Mississauga a Ontario a lokacin da Tani yake da shekara 10 da haihuwa. Daga nan ya fara buga wa tawagar Canada wasa.

Promise Dabid (Union SaintGilloise). Tun farko Promise ya samu damar wakiltar ƙasashe biyu tsakanin Canada da Nijeriya. An haife shi a Brampton a Ontario, kuma iyayensa ƴan Nijeriya ne, har ma ya fara buga wa matasan Nijeriya wasa daga baya ya zabi Canada, wadda ta fara saka shi a wasan babbar tawagar a watan Fabrairun 2025.

Owen Goodman ( South Simcoe United). An haifi Goodman a Landan, Ingila, iyayensa sun koma Canada yana da shekara biyar da haihuwa, inda ya girma a Alliston, Ontario a Canada. Yana buga wasa a South Simcoe United, wanda tun farko mai tsaron baya ne, amma yanzu ya koma tsare raga. Mahaifinsa Philip ɗan Ingila ne, yayin da mahaifiyarsa Abi ƴar Ogbomosho ce a Nijeriya.

Afirka ta Kudu:

Ime Okon (SuperSport United) An haifi Ime a birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu, inda mahaifinsa ne daga Nijeriya, kuma rayuwarsa gabaki ɗaya a Afirka ta Kudu ya yi ta, hakan ya sa ya zabi buga wa ƙasar wasa. Waɗannan ƴan wasa suna nuna yadda ƙwallon ƙafa ke zama wasan duniya, inda kenan babu wata iyaka ko katanga tsakanin ƙasashe.

Norway:

Antonio Eromonsele Nordby Nusa (RB Leipzig). An haifi ɗan ƙwallon ranar 17 ga watan Afirilun 2005 a Langhus, Norway, wanda ke buga wasa a RB Leipzig mai buga gasar Bundesliga ta Jamus. Mahaifinsa mutumin Benin ne a Nijeriya, yayin da mahaifiyarsa ƴar Norway ce.

Wannan lamari yana da muhimmanci sosai ga Nijeriya. Duk da cewa Super Eagles ba ta kai ga samun tikitin shiga gasar ba, Nijeriya na da tasiri a ƙwallon ƙafa ta hanyar ƴan asalin ƙasar da ke buga wasa a manyan ƙasashe a duniya.

Sannan hakan yana nuna abubuwa uku masu muhimmanci:

Ƙwarewa, Inganci da hazaƙar ƴan Nijeriya, Yawan ƴan wasa masu asali daga Nijeriya a manyan liglig a duniya, yana nuna irin baiwar da ƙasar nan ke da ita a fannin ƙwallon ƙafa.

Rashin tsarin riƙe ƴan wasa.  Wasu daga cikin waɗannan ƴanwasan sun zabi wakiltar wasu ƙasashe saboda tsarin horo da kulawa da suka samu a can.

Super Eagles
Abba Ibrahim Wada
Website |  + posts Bio
  • Abba Ibrahim Wada
    Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?
  • Abba Ibrahim Wada
    Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji
  • Abba Ibrahim Wada
    Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City
  • Abba Ibrahim Wada
    LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 
Super Eagles
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B
  • Sulaiman
    CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare
  • Sulaiman
    Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

MASU ALAKA

Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira
Wasanni

Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira

July 10, 2026
Argentina Ta Kai Zagayen Kwata Fainal Bayan Nunawa Egypt Ƙwanji
Wasanni

Argentina Ta Kai Zagayen Kwata Fainal Bayan Nunawa Egypt Ƙwanji

July 7, 2026
FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA
Wasanni

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran

Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

July 10, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

July 10, 2026
CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

July 10, 2026
Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

July 10, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?

July 10, 2026
“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.