ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
DANGOTE

Kamfanin Sufurin Siminti na Dangote, ya kara fadada shirye-shirye masu tasiri tare da amfani da fasahohin zamani domin inganta aiki, shugabanci nagari da kuma bin ka’idojin tsaron hanya.

A wata sanarwa da Sashen Hulda da Jama’a da Sadarwar kamfanin ya fitar, an bayyana cewa sabbin shirye-shiryen sun shafi muhimman fannoni na gudanar da ayyuka, ciki har da auna kwazon aiki, karfafa ka’idojin shugabanci da inganta tsarin daukar alhaki.

Sanarwar ta kara da cewa shirye-shiryen sun kuma hada da horar da direbobi tare da bunkasa kwarewarsu, amfani da tsarin tsaro na zamani da ke aiki da fasaha, tsara zirga-zirga cikin tsari, da kuma sabunta takardun cancanta akai-akai.

ADVERTISEMENT

Sauran shirye-shiryen sun hada da gwajin miyagun kwayoyi ga direbobi, kulla hadin gwiwa da sauran hukumomi da kungiyoyi, aiwatar da manufofin muhalli, zamantakewa da shugabanci (ESG), shirye-shiryen dorewar ci gaba da kuma ayyukan tallafa wa al’umma.

Sanarwar da kakakin kamfanin, Anthony Chiejina, ya sanya wa hannu ta tunatar da cewa Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta yaba wa kamfanin kan shirye-shiryensa na tsaron hanya, wadanda suka taimaka wajen rage haduran mota a fadin kasar nan.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

An kuma ambato Shugaban Sashen Sufuri na kamfanin, Murilo Silba, yana cewa kamfanin ya inganta tsarin gudanar da harkokin sufuri ta hanyar amfani da na’urorin bincike masu sarrafa kansu da kuma hanyoyin da ke amfani da basirar wucin gadi (AI) domin kara ingancin aiki da tsaron hanya.

Silba ya bayyana cewa kamfanin ya kuma girke ingantattun na’urorin GPS da tsarin telematics domin sa ido kan halayen direbobi a lokacin tafiya kai tsaye, lamarin da ke kara karfafawa kulawa da kuma tabbatar da tsaro a dukkan motocin kamfanin.

Ya kara da cewa, a kokarin da kamfanin ke yi na rage gajiyar direbobi, ya kara fadada shirye-shiryen kula da lafiyarsu tare da gudanar da tarurruka daban-daban da masu motocin dakon kaya da direbobinsu domin karfafa wayar da kai kan tsaro, bin ka’idoji da daukar alhaki a kan hanya.

Mista Murilo Silba ya ce hadin gwiwar da kamfanin ke yi da Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) ya fara samar da sakamako mai kyau, yana mai cewa wannan hadin gwiwa na ci gaba da karfafa ka’idojin tsaro a dukkan ayyukan kamfanin.

Ya kara da cewa jami’an FRSC na taka muhimmiyar rawa wajen horaswa da tantance direbobi a Makarantar Koyar da Tukin Motocin Dakon Kaya ta Dangote da ke Obajana, inda suke ba da shawarwari na fasaha, tabbatar da bin ka’idojin aiki mafi inganci da kuma taimakawa wajen samar da kwararrun direbobi masu kishin tsaro.

A cewarsa, adadin direbobin da ke samun horo cikin tsari, gwajin miyagun kwayoyi da barasa, da kuma sabunta takardun cancanta lokaci-lokaci ya karu sosai, inda ya bayyana wannan ci gaban a matsayin “mai ban mamaki kwarai.”

Silba ya bayyana cewa tsakanin zangon farko na shekarun 2025 da 2026, kamfanin Dangote Simintin na Obajana ya samu gagarumin ci gaba wajen bin matakan tsaro. Gwajin miyagun kwayoyi da barasa ya karu da kashi 245.2 cikin dari, binciken motocin kafin fara tafiya ya karu da kashi 489.1 cikin dari, yayin da shirye-shiryen horar da direbobi suka karu da kashi 128.4 cikin dari.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ya yaba wa kamfanin kan kafa sabbin ma’aunai wajen gudanar da tsaron hanya, tare da karfafa shi da ya ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da suka taimaka wajen inganta tsaro a fannin sufuri a Nijeriya.

Corps Marshal din ya bayyana cewa idan aka kwatanta shekarun 2025 da 2026, haduran da suka shafi manyan motocin kamfanin Dangote Cement sun ragu da kashi 56 cikin dari, mace-macen da suka biyo bayan irin wadannan hadurran sun ragu da kashi 36 cikin dari, yayin da yawan raunuka ya ragu da kashi 52 cikin dari.

Ya ce wannan ci gaban ya nuna cewa kamfanin ya aiwatar da shirin nazarin gibin da ke akwai da kuma manufofin gudanarwa da ya kamata sauran kamfanonin sufuri da dabaru a Afirka su yi koyi da su.

Ya ce: “Mun dade muna cewa idan Kamfanin Simintin Dangote ya yi abin da ya dace, Nijeriya da ma Afirka za su yi abin da ya dace. Wannan babban abin alfahari ne ga Nijeriya.”

DANGOTE
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutun Biyu Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.