ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yansanda Sun Cafke Mutun Biyu Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Adamawa

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Adamawa

Rundunar ’Yansandan Jihar Adamawa ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da aikata laifin fashi da makami a Karamar Hukumar Yola ta Arewa.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a ranar Talata, ya ce jami’an ’yansanda da ke aiki a Hedikwatar ’Yansanda ta Doubeli ne suka kama mutanen biyu dangane da wasu laifuka daban-daban.

“Ranar 3 ga Yuni, 2026, jami’an ’yansanda sun kama wani Idris Auwal mai shekaru 22, mazaunin Doubeli Culbert da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa,” in ji sanarwar.

ADVERTISEMENT

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya hada baki da wasu mutum uku da har yanzu suka tsere, inda suka kutsa cikin wani shago da ke Nassarawo Borehole mallakin Abdullahi Sunusi.

Sanarwar ta ce wadanda ake zargin sun sace jaka mai dauke da kudi, muhimman takardu da kayayyakin masarufi na shago da darajarsu ba a bayyana ba.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

“Bayan gudanar da bincike mai zurfi, an samu nasarar kama Idris Auwal, yayin da ake ci gaba da kokarin cafke sauran abokan aikinsa da suka tsere.”

A wani makamancin lamari da ya faru a ranar 5 ga Yuni, 2026, jami’an rundunar da ke Doubeli sun kama wani da ake zargin dan kungiyar ‘Shilla’ ne, wadda ta shahara wajen kai hare-hare da kwace kayan jama’a.

Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya tare wani Abubakar Abdullahi a hanyar Doubeli Bypass dauke da adda, inda ya kwace masa wayar salula kirar Itel da kuma kudi Naira 19,000.

An kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya ji wa wanda abin ya shafa rauni a kai da adda.

“Abin farin ciki, jami’an ’yansanda sun isa wurin cikin gaggawa, suka kama wanda ake zargin tare da tabbatar da cewa an kai wanda aka kai wa harin asibiti domin samun kulawar gaggawa.”

Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da adda, wuka da kuma wayar salular da aka sace.

Nguroje ya ce ana ci gaba da bincike kan mutanen biyu, yayin da rundunar ke kara kaimi wajen cafke sauran ’yan kungiyar da suka tsere domin gurfanar da su a gaban shari’a.

Rundunar ta tabbatar wa jama’a da jajircewarta wajen yaki da ayyukan kungiyar Shilla da sauran nau’o’in laifuffuka.

Ya kuma bukaci mazauna jihar da su ci gaba da bai wa ’yansanda sahihan bayanai cikin lokaci domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Adamawa
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya - Matawalle

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.