ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kanu, Salah, Drogba Da Manyan ‘Yan Wasan Da Ba Su Taba Lashe Kofin Afirka Ba

by Abba Ibrahim Wada
6 months ago

Mutane da dama za su yi mamaki idan suka ji sunayen manyan ‘yan wasan nahiyar Afirka da ba su taba lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka duk da irin bajintar da suka nuna a nahiyar Turai.

Ana ganin wannan ce gasa ta karshe da Muhammad Salah zai buga a tarihinsa na kwallon kafa kuma dama ta karshe da yake da ita ta lashe gasar a bana a kasar Moroko.

  • Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Taurarin Dan Adam Na Sadarwar Intanet
  • Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Ta Farko Game Da Tattalin Arziki Mai Alaka Da Yanayin Duniyarmu

Duk da cewa dangantakar Mohamed Salah da Liberpool na tabarbarewa a halin yanzu, amma duk da haka ba a shakkar kokwanton nasarar da ya samu a kungiyarsa ta Liberpool.

ADVERTISEMENT

Fitaccen dan wasan na Masar ya lashe gasanni da dama a lokacin da yake tare da kungiyar Liberpool, amma abin mamaki bai taba lashe gasar cin kofin Afrika da kasarsa Masar ba.

Yayin da dan wasan gaban zai iya sauya wannan labarin a cikin wata mai zuwa a gasar ta 2025 da tuni aka fara a Morocco, hankali ya fara komawa kan wasu daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa na Afirka da ba su taba samun nasarar lashe kofin ba.

LABARAI MASU NASABA

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

 

Mohamed Salah (Masar)

Shekarar Muhammad Salah 33 a duniya, ana ganin wannan ce damar karshe da kyaftin din na Masar ke da ita na lashe gasar. Masar ita ce kasar da ta fi kowacce kasa samun nasara a gasar, inda ta lashe kofunan sau bakwai a tarihi.

Abin mamaki shi ne Masar ta kasa samun tikitin shiga gasar AFCON na 2012 da 2013 da 2015, wanda ke nufin ya buga gasarsa ta farko ne a 2017 lokacin da kasar da ke yankin arewacin Afirka ta sha kashi a hannun Kamaru a wasan karshe.

Salah, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika a shekarar 2017 da 2018, ya jure rashin nasara a gida a gasar AFCON ta 2019, wadda Afrika ta Kudu ta yi waje da ita a wasan zagaye na ‘yan 16.

Masar ta koma wasan karshe a gasar ta 2021 – wasan da Salah ya sha kashi a hannun abokin wasansa na Liberpool a lokacin Sadio Mane a wasan da aka tashi da bugun fanerati.

Salah wanda yanzu yake na biyu a jerin ‘yan wasan da suka fi zura kwallaye a tawagar Masar, ya ji rauni a matakin rukuni na gasar AFCON na 2023, lamarin da ya tilasta masa kallon yadda DR Congo ta fitar da tawagarsa a zagaye na biyu.

 

Didier Drogba (Ibory Coast)

Shahararren dan wasa Didier Drogba ya kasance danwasa mai taka rawar gani a manyan wasanni a kungiyar da ya bugawa wasa wato Chelsea, inda ya zura kwallaye tara a manyan wasannin karshe 10 da ya buga wa kungiyar ya kuma dauki kofin a wasanni takwas cikin wadannan wasannin.

Duk da kokarin danwasan, bai samu nasarar samun nasara ba a wasannin karshe biyu da ya jagoranci tawagar Ibory Coast a matsayin kyaftin. A shekara ta 2006, Elephants ta buga fanerati da mai masaukin baki Masar, amma Drogba ya barar da bugunsa, inda Masar ta yi nasara da ci 4-2.

Kasar ta Afirka ta Yamma ta sake zuwa wasan karshe a shekarar 2012 a matsayin kasar da aka fi tunanin lashe gasar, amma ta yi rashin nasara. Sauran gasannin da ya buga wa kasar akwai wadda suka kare a matsayi ta hudu a shekarar 2008 da guda biyu da aka cire su a matakin kwata fainal (2010 da 2013), kafin ya yi ritaya daga kwallon kafa a watan Agustan shekara ta 2014. Sai dai wata shida bayan ritayarsa, Ibory Coast ta doke Ghana a wasan karshe na 2015, a bugun fanarati.

 

George Weah (Laberiya)

Tarihin kwallon kafa a duniya da nahiyar Afirka ba zai taba cika ba dole sai an saka sunan George Weah. Domin in dai batun lashe kyautuka a fagen wasa ne, tsohon dan wasan na Paris St-Germain da AC Milan da Chelsea ya fi kowane dan wasan kwallon kafa na Afirka.

George Weah ya kasance mutum daya tilo daga nahiyar Afirka da ya lashe kyautar Ballon d’Or, inda ya samu kambun a shekarar 1995 – a wannan shekarar ne ya zama gwarzon dan kwallon Afrika a karo na biyu.

Amma duk da haka bai iya samun irin nasarorin da ya samu a kungyarsa da Laberiya ba. Kasar Laberiya ta buga wasanni biyu ne kacal a rukuninsu na farko a gasar a shekarar 1996, bayan da Nijeriya ta fice daga gasar.

An yi waje da ita daga gasar ne bayan da ta yi nasara a kan Gabon sai kuma ta sha kashi a hannun Zaire (DR Congo).

Laberiya ta koma gasar AFCON a shekara ta 2002, a lokacin da shekaru suka cimma Weah.

Yana da shekara 35, amma ya zura kwallo daya tilo da ya taba ci a AFCON a wasan farko da suka buga da Mali, amma tawagar Lone Stars ta sake kasa fitowa daga rukuninta. Bayan kasancewa kyaftin din kasarsa, Weah ya ci gaba da jagorantar al’ummarsa a matsayin shugaban kasa tsakanin shekarar 2018 zuwa 2024.

 

Nwankwo Kanu (Nijeriya)

Lange-lange, shi ne sunan da ake kiran tsohon dan wasan Nigeriya Nwanko Kanu, dan wasan na gaba ya lashe kofuna da dama a Turai, ciki har da gasar Zakarun Turai a Ajad da kuma kofin UEFA Cup a Inter Milan kafin ya samu nasarar lashe kofuna a Arsenal.

A lokacin ne Kanu ya rubuta sunansa a tarihin kwallon kafa na Nijeriya a matsayin wani gwarzon dan wasa tawagar Nijeriya a bangaren da suka lashe gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekara 17 a 1993 da kuma lambar zinare a gasar Olympics ta 1996.

Sai dai kofin AFCON ne ya gagare shi, kuma ya kusa da lashewa a shekarar 2000, lokacin da Super Eagles ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Kamaru da bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Kanu, mai shekara 23 a lokacin, bai yi nasara a nasa bugun ba, kuma Nijeriya ba ta sake komawa wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ba a lokacin da yake buga wasa.

Gwarzon dan kwallon Afirka sau biyu, ya yi ritaya da zinare a gasar Olympic amma azurfa da tagulla ne kawai ya samu daga gasar cin kofin Nahiyar Afrika.

 

Michael Essien (Ghana)

Gasar firimiyar Ingila a shekaru 15 baya ta yi nasarar samun zakakurin dan wasa Michael Essien, wanda ya shafe kusan shekara biyar tauraruwarsa tana haskawa a kungiyoyin Chelsea da Real Madrid.

Nasarar karshe na AFCON guda hudu da Ghana ta yi, ta zo ne a shekarar 1982, wanda hakan ke nufin manyan ‘yan wasa da dama da suka bugawa kasar sun kasa daukar kofin tare da tawagar yanwasan Ghana.

Daga cikinsu akwai Essien, wanda za a iya cewa shi ne dan wasan tsakiya mafi hazaka a kasarsa. Kamar Drogba, ya ci nasara tare da Chelsea tsakanin 2006 da 2012 amma bai samu irin wannan nasarar ba a kasarsa.

Lokacin da Essien yake matashi ya shiga tawagar da aka doke su a wasan dab da na kusa da na karshe a shekara ta 2002, Ghana ta rasa samun gurbi a 2004, yayin da ya ji rauni a 2006.

An sanya sunan shi a cikin tawagar gasar a lokacin da Ghana ta karbi bakunci a 2008, amma Kamaru ta lallasa ta a wasan kusa da na karshe kafin ta dawo ta kare matsayi na uku.

Essien ya ji rauni ne a tsakiyar gasar ta 2010, abin da ya tilasta masa kallon yadda abokan wasansa suka koma wasan karshe a karon farko cikin shekaru 18, amma Masar ta doke su da ci 1-0.

Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 
  • Abba Ibrahim Wada
    An Raba Jadawalin Gasar Premier Ta Ingila Ta Kakar Wasan 2026/2027
  • Abba Ibrahim Wada
    Daga 1930 Zuwa 2026: Yadda Aka Buga Wasa Na Dubu Ɗaya A Gasar Kofin Duniya
  • Abba Ibrahim Wada
    Babu Wani Saɓani Tsakanin Osimhen Da Lookman – Ndidi

MASU ALAKA

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?
Manyan Labarai

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

July 5, 2026
LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 
Wasanni

LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

July 5, 2026
Enekweci Ne Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya A Wasannin Commonwealth Na Bana
Wasanni

Enekweci Ne Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya A Wasannin Commonwealth Na Bana

July 5, 2026
Next Post
Yawan Kudin Da Manyan Kamfanonin Kasar Sin Suka Samu A Farkon Watanni 11 Na Bana Ya Karu Da 0.1%

Yawan Kudin Da Manyan Kamfanonin Kasar Sin Suka Samu A Farkon Watanni 11 Na Bana Ya Karu Da 0.1%

LABARAI MASU NASABA

Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata

Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata

July 5, 2026
Ba Mu Yarda Da Maƙiyanmu Ba, A Shirye Muke —Iran

Ba Mu Yarda Da Maƙiyanmu Ba, A Shirye Muke —Iran

July 5, 2026
Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

July 5, 2026
LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

July 5, 2026
Enekweci Ne Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya A Wasannin Commonwealth Na Bana

Enekweci Ne Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya A Wasannin Commonwealth Na Bana

July 5, 2026
Dakarun Tsaron Teku Na Sin Na Ci Gaba Da Sintirin Wanzar Da Doka A Yankunan Ruwa Na Gabashin Tsibirin Taiwan

Dakarun Tsaron Teku Na Sin Na Ci Gaba Da Sintirin Wanzar Da Doka A Yankunan Ruwa Na Gabashin Tsibirin Taiwan

July 4, 2026
Wasu Matasa Amurkawa Sun Ziyarci Sin Don Kara Fahimtar Kasar

Wasu Matasa Amurkawa Sun Ziyarci Sin Don Kara Fahimtar Kasar

July 4, 2026
Wakilin CMG Ya Zanta Da Mataimakin Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

Wakilin CMG Ya Zanta Da Mataimakin Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

July 4, 2026
CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

July 4, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Jinjina Wa Shugaban NAHCON Kan Nasarar Aikin Hajjin 2026

Gwamnatin Zamfara Ta Jinjina Wa Shugaban NAHCON Kan Nasarar Aikin Hajjin 2026

July 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.