ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karuwar Rashin Tarbiya A Makarantunmu

by Rabi'at Sidi Bala
5 months ago
Tarbiya

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da yadda ake samun tabarbarewar ilimi da rashin tarbiyyar yara a wasu makarantun gwamnati da makarantu masu zaman kansu. Duba da yadda yaran ciki ke kasancewa marasa tarbiyya, ga zage-zage a bakinsu kamar ba ‘ya’yan musulmai ba. Wani lokacin ma har da guje-guje da tsalle-tsallen da bai kamara ace yara mata na yi ba, ga raina malamai. Idan yara sun fito daga aji madadin malami ya mayar da su a tsanake, sai ya fara ruwan ashar, suna yi masa dariya da girgiza jiki da gwalo. Shi kuma malami ya bisu a guje tare da ruwan ashar kamar bamaguje, su yi ta aibata yaran suna koya musu ashar.

  • Kasar Sin Na Da Kayayyakin Tarihi Na Halittu Na Duniya Guda 15
  • Gyaran Dokar Zabe: Yadda Jinkirin Majalisar Dattawa Zai Iya Kawo Tsaiko Ga Zaben 2027

Sai dai wasu na ganin hakan yafi faruwa ga makarantun gwamnati. Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko me yake kawo haka, kuma me ya sa malaman makarantun gwamnati da makarantu masu zaman kansu suka bambanta, musamman ta tsarin tarbiyyar yara, da kuma yadda su yaran suke iya jin maganar malamansu?. Ta wacce hanya ya kamata a shawo kan irin wadannan matsalolin, kuma wadanne hanyoyi ya kamata malamai su bi, domin inganta tarbiyyar yara ba tare da sun zama batattu ba?.

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kanar haka;

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, Dala, Kano:

LABARAI MASU NASABA

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

Babu shakka akwai tabarbarewar tarbiyya a makarantun gwamnati musamman kuma na firamare, inda nan ne tushen tarbiyyar. Wannan shi ne mai dokar barci, ya bige da gyangyadi. Wannan matsala ta samo asalin ne daga gurbatattun mutanen da gwamnati take dauka a matsayin malamai. Siyasa, sanayya da alfarma sun lalata harkar ilimi sosai, ba a daukar wadanda suka cancanta. Duk lalacewar mutum da rashin cancantarsa, indai ya san wani dan siyasa to za a dauke shi aiki. Ba shi da nutsuwa ba shi da nagarta, bai tsaya ya yi karatun ba yadda ya dace bare ya zama nagartacce abin koyi. Gwamnati ta ji tsoron Allah. Ta cire alfarma ko sanayya daga tsarin daukar aiki, musamman malaman makaranta. Gwamnati ta yi koyi da tsarin makarantu masu zaman kansu da suke bi wajen daukar malamai, duk wanda bai cancanta ba ko dan waye, kada a dauke shi. Wadanda suka riga suka shiga, a ba su horo da bita ta inganta tarbiyyarsu, kuma a saka doka mai tsauri game da yin zagi ko furta miyagun kalamai ga dalibai.

Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Ƙaura-Namoda, Jihar Zamfara:

Mafi akasari malaman makarantar gwamnati ba su cancanci zama malamai ba, amma a haka ake yi musu alfarma ba tare da sun san dabarun koyarwar ba ballantana hanyoyin bayar da tarbiyya ga dalibai. Sabanin Makarantar kudi da ba sa daukar malami har sai sun tabbatar da iyawarsa. A fara tantance wane ne malami, kafin a ba shi gurbin aiki, bayan an tantance a rika sauke hakkinsu a kan lokaci. Don wani zubin har da matsalolin rashin sauke hakkokinsu yana kara fusata su, har su yi ta zagin dalibai, su ki mayar da hankali a kan abin da ya dace.

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

Ana kafa makarantu ne domin samar da ilimi da kuma tarbiyya, don haka koda a wajen bayar da shaidar kammala karatu ake cewa, an gamsu da ilimin da dalibi ya samu da kuma tarbiyyarsa. Domin tarbiyya da ilimi suna tafiya ne kafada da kafada. Sai dai wani abin lura shi ne, tarbiyyar dalibi ba ta inganta sai da gudunmawar iyaye. Idan har iyaye ba sa karfafa malami akan kokarin da yake yi kan ‘ya’yansu to, haka yaran za su tashi suna raina malamansu, kuma ba za su mayar da hankali ga abin da ake koya musu ba. Wani abin takaici kuma shi ne iyaye sun fi raina malaman makarantun gwamnati, saboda ganin na kyauta ne, ba wani abin kirki ake kashewa wajen biyan kudin makaranta ba. A saboda haka ba a cika mutunta karatun makarantun firamare na gwamnati ba, wadanda kuma akasari daliban ‘ya’yan talakawa ne, da yawansu ba su dauki zuwa makarantar da muhimmanci ba. Su kuwa makarantun kudi wadanda akasari ana bude su ne da niyyar kasuwanci, suna tsayawa kai da fata don ganin ba a samu matsalar da za ta sa iyaye su yi korafi a kansu ba, kuma su ma iyayen na takatsantsan, don sun san suna kashe kudi sosai a kan biyan makarantun yaran. Akwai kalubale sosai wajen ganin yadda ake yi wa makarantun gwamnati rikon sakainar kashi, ba a ba su muhimmancin da ya kamata. A rika bai wa malamai horon sanin dabarun koyarwa akai-akai, kuma a rika daukar tsauraran matakai don ladabtar da dalibai da malaman da ba sa kiyaye dokokin makaranta da tsarin tarbiyya a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:

Gani suke kamar gwamnati ce ke biyansu, yaran idan sun je kamar kyauta ne ba kudi ake biya sosai ba. Ya kamata gwamnati ko shi ministan ilimi ya zauna ya canja tsari, ina ga minista ne ya kamata ya gyara tsarin makarantun gwamnati ko wani babba. Dan babu kulawa ka ga yaro kaya duk datti da sauransu.

Sunana Jibrin Yusuf Kaila, daga garin Hadejia, a Jihar Jigawa:

Babu shakka wannan batu ne da ya jima ana tattaunawa akai, musamman idan aka lura da makarantun kudi suna da karancin albashi amma kuma suna da kiyayewa, duk da rashin kula da harkokinsu. Amma makarantun gwamnati idan ana kwatantawa akan harkokinsu za a ga ba a cika kiyayewa ba, sai tarin kalubale. A gaskiya ba na zargin Gwamnati akan irin wannan batun, domin kaso mafi yawa na fi zargin malaman makaranta su ya kamata su nuna gyara a ayyukansu, su kuma ba da muhimmanci akan gyara tarbiyyar yaran da suke kula da su. Su ma kansu al’ummar da ke maƙwaftaka da wadannan makarantun suna da nasu kuskuren wajen biris ko rashin daukar abu da muhimmanci, musamman akan abin da ya shafi kayan gwamnati. Akwai abin da gwamnati ba komai za ta iya ba, sai da taimakon al’umma. amma al’umma sun kasa ganewa cewa ita gwamnati ta al’umma ce idan ka yi sakaci da abin da ya shafi kayan Gwamnati tamkar kanka ka yi wa.

Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga, Jihar Jigawa:

Eh hakan na faruwa musamman a makarantun gwamnati, amma matsalar ta malaman ce a harkar koyo da koyarwa, san yin ashar a yara ba daidai bane. Ya kamata malaman makaranta su kiyaye zagin yara barkatai. Gwamnati ta rika yin semina akai-akai domin nunawa malamai cewa, tarbiyar yara bata tsaya akan iyaye ba har malamansu. Shawara, Malamai su tuna cewa su fa wata fitila ce wacce take haska duhu, ba wai iya koyon karatu za su rika bawa yara ba har ilimin zamantakewa ,tarbiyya da sauran su .

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano A Jihar Kano:

Rashin samun wadatar kayan aiki da kuma biya wa malaman albashi, sannan wasu malaman makarantun gwamnatin basu cancanta ba, wasu da ma ‘yan kwalta ne. A rika dibar malaman da suka dace, wadanda suka sami ilmi da tarbiyya mai kyau. Gwamnatin ya kamata ta rika bawa malamai kayan aiki masu kyau, sannan ta rika biyansu hakkinsu akan lokaci kamar yadda makarantu masu zaman kansu suke yi.

Sunana Muktari Sabo, Jahun, Jihar Arewa:

Gaskiya ne akwai wasu malaman makaranta masu irin wannan dabi’a, amma hakan ba kawai ya takaita a makarantun gwamnati bane, a’a har amakarantu masu zaman kansu ana samu. Amma abin yana faruwa ne saboda daukar malaman da basu dace da aikin koyarwa ba, saboda koyar da tarbiyya ai sai mai tarbiyya, wanda ba shi da tarbiyya taya zai koyar da ita ga wani. Shi kuma yaro yana mu’amala da malami ne irin yadda malamin yake mu’amala da shi, don haka sai an sami malami mai tarbiyya sannan ake samun dalibi nagari. A rika daukar malaman da suka dace suka san aikin koyarwa, musamman makarantun gwamnati domin a nan abin yafi faruwa. Idan malami yayi kuskure a yi masa gyara, in ya wi gyarawa a hkunta shi.

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, Jihar Kano:

Ai ina ganin su kansu malaman masu irin wannan hali tarbiyyar bai ishe su ba, bale su bawa wasu. Gwamnati ta rika tacewa kafin ta dauki malamai kawai. Su sani cewa yara dai amana ce a hannunsu bai dace ba ace suna irin wannan dabi’u marasa kyau.

Tarbiya
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A

MASU ALAKA

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi
Manyan Labarai

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

June 25, 2026
EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53
Manyan Labarai

EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

June 25, 2026
Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya
Labarai

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbo Na Gwaji Da Za A Iya Sake Amfani Da Shi

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbo Na Gwaji Da Za A Iya Sake Amfani Da Shi

LABARAI MASU NASABA

APC Ta Dage Yakin Zaben Shugaban Kasarta A Kano

An Dakatar Da Shugaban APC Na Kebbi Da Kwamishina Kan Zaɓen Cike Gurbin Zuru

June 25, 2026
Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

June 25, 2026
EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

June 25, 2026
Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.