ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Na Ci Gaba Da Bude Idon Matasan Afrika 

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Sin

A baya bayan nan, an gudanar da bikin bude jerin shirye-shirye domin murnar kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a ta Sin da Afirka a kasar Mauritius, wato jerin shirye-shiryen murnar bikin bazara da gasar fasahohin AI ta matasa, mai taken “Zumuncin Sin da Afirka”, domin inganta cudanyar jama’ar Sin da Afirka da samun makoma mai haske.

Fara aiwatar da wadannan shirye-shirye jim kadan bayan dawowar ministan harkokin wajen Sin da ya kaddamar da shekarar musayar al’adu ta Sin da Afrika, ya nuna cewa, kasashen Afrika da al’ummarta na maraba da wannan shiri kuma suna dokin cudanya da fahimtar juna tsakaninsu da kasar Sin.

Kamar yadda shugaban kasar Sin ke cewa, matasa su ne makomar dangantakar kasa da kasa. Mayar da hankali da Sin take yi sosai kan matasan Afrika, abu ne mai muhimmanci domin su ne masu raya dangantakar bangarorin biyu a nan gaba, kuma su ne za su ja ragamar kafawa da tafiyar da al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya.

ADVERTISEMENT

Yayin da duniya ke karkata ga kirkirarriyar basira, da kasancewar kasar Sin jagora a wannan bangare, gasar kirkirariyar basira tsakanin matasa a Afrika wata gagarumar gudunmawa ce ga bunkasa kwarewarsu, wadda za ta kara musu ilimi da basira da hikima. Sannan wata dama ce ga kasashensu na amfana da fasahar matasan wajen bunkasa harkokin da suka shafi raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Bisa la’akari da yawan al’umma a nahiyar Afrika, aikin yi wani babban kalubale ne ga matasan nahiyar, don haka irin wannan gasa za ta kara bude kwakwalwarsu, ta ba su damar zurfin tunani da yin kirkire-kirkire masu amfani da za su ba su damar dogaro da kansu har ma da taimakawa sauran matasa.

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Hakika ta hanyar dimbin shirye-shiryenta masu fa’ida, kasar Sin tana ci gaba da bude idon matasan Afrika, tana wayar musu da kai, kana tana ba su damarmakin raino da raya fasahohinsu, har ma da fito da kwarewa da basirar da suke da su.

Ta irin wadannan kyawawan manufofi, za mu gane cewa, ba karfafa mu’amala tsakaninta da nahiyar Afrika kadai Sin ke yi, har da kirkiro wa kasashen Afrika wata hanya ta samu ci gaba irin na zamani mai dorewa, tare da ba su damar shiga takara a duniya.

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • Sulaiman
    Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
  • Sulaiman
    Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

MASU ALAKA

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

July 17, 2026
Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
Daga Birnin Sin

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Next Post
Uba Sani Zai Gina Tashar Mota Mafi Girma Da Zamanantarwa A NIjeriya

Uba Sani Zai Gina Tashar Mota Mafi Girma Da Zamanantarwa A NIjeriya

LABARAI MASU NASABA

Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

July 17, 2026
Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

July 17, 2026
Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

July 17, 2026
Falalar Salatut Tasbihi

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026
A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

July 17, 2026
Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

July 17, 2026
Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

July 17, 2026
Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

July 17, 2026
Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.