An gudanar da wani taro a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, don tattauna batun aikin bayar da ilimi na kasar Sudan a jiya Juma’a, inda wani jami’in kasar Sin ya bayyana cewa, rikice-rikice a kasar Sudan sun sa yaran kasar kusan miliyan 8 rasa damar shiga cikin makarantu, kana a sakamakon wutar yaki dimbin makarantun kasar Sudan sun riga sun zama baraguzai, abun da ya haifar da dimbin illoli ga rayuwar yaran kasar.
Ban da haka, jami’in na kasar Sin ya ce ya kamata a kama mutanen da suka lahanta tare da cin zarafin yara yayin yakin, da gurfanar da su gaban kotu, ba tare da wanke wani daga cikinsu ba.
Haka zalika, a madadin bangaren kasar Sin, jami’in ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su samar da karin kudi wajen raya aikin bayar da ilimi a kasar Sudan, da ba da taimako a fannonin gyara da sake gina makarantu, da horar da malamai, da samar da isassun kayayyakin da ake bukata domin gudanar da aikin bayar da ilimi, da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata dabarun koyarwa, ta yadda karin yara da matasa na kasar Sudan za su samu damar samun karin ilimi.
A sa’i daya kuma, jami’in na kasar Sin ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki a rikice-rikicen da ake yi a kasar Sudan da su tsagaita bude wuta cikin sauri, ta yadda za a samu damar koma wa teburin shawarwari, da daidaita al’amuran kasar ta hanyar lumana. (Bello Wang)














