ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan

by Ra'ayinmu
4 months ago

A bisa ƙoƙarin da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa ke ci gaba da yi, na daƙile ci gada da aikata, musamman manyan laifuka, a gidajen da ke a ɗaukacin faɗin ƙasar ne, ta samu nasarar bankaɗowa da kuma lalata, sama da Wayoyin Salula guda 1,167, da wasu masu zaman Jarun, ko dai  suka shiga da su cikin gidan ta ɓarauniyar hanya, ko kuma da haɗin bakin, wasu ma’aikatan a gidajen.

Kazalika, ta kuma bankaɗso ƙarin wasu haramttun kaya, a ɗaukacin gidajen kaso, da ke a ɗaukacin faɗin ƙasar.

Shugaban Hukumar na ƙasa Sylɓester Ndidi Nwakuche, ya ce, an gano tare da kuma ƙwato  kayan ne, a wasu ayyuka da Hukumar ta gudanar, a watanni takwas, da suka gabata, inda ya ce, wasu daga cikinkayan sun haɗa da Wayoyin Salula na alfaram wato smartphones da layukan Waya da katin da ake lodawa Wayoyin da kuma sauran, wasu haramtattun kaya.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, kasancewar waɗannan haramtattun kayan a gidajen gyran hali na ƙasar, lamarin ya zamo, babbar barazana a ɓangaren tsaro, wanda hakan ke bai wa, masu zaman Jarun ɗin damar aikata, manyan laifuka.

Shugaban ya ce, Hukumar ta hukunta jami’an ta, 147, saboda aikata laifuka da ban da ban, na rashin nuna ɗa’a da shigar da haramtattun kaya, zuwa cikin gidajen gyaran hali na ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Bugu da ƙari, Hukumar ta kuma cafke wasu mata biyu, kan zargin su, da  yunƙurin shigar da kayan maye, cikin gidan hali na jihar Kano.

An ruwaito cewa, a watan Afirilun 2026 kacal, akwai sama da masu zaman Jarun 80,000 da ake da su, a  gidajen gidan gyaran hali guda 241 cikinsu, har a sauran wasu cibiyoyin da ake tsare da masu laifi.

Akasarin gidajen a cunkushe suke da masu zaman jarun waɗanda suka kasance, ba a wadata su, da kuɗaɗen gyaransu ba, tare da rashin kula da jin daɗi da walwalar jami’an da ke aiki, a gidajen.

Haka zalika, an ruwaito cewa, a 2025, sama da masu zaman jarun, a wasu gidajen gyaran hali na ƙasar guda 145 suka ranta a na Kare tare da kuma ƙara samun tserwar wasu, daga tsakanin watan Maris zuwa na Agustan 2025.

A hukumance, an kafa gidajen gyaran hali ne, ba wai kaɗai, dolamutaneunta, waɗanda ake tsare da su ba, amma domin gidajen, su kasance, wajen bin doka da oda da kuma sauya nugayen ɗabi’un, waɗanda ake tsare da su.

Amma abin takaicin shi ne, yadda ake ci gaba da samun shigar da Wayuyin Salula da miyagun ƙwayoyi, ta ɓarauniyar hanya, tare da haɗin bakin ɓata garin jami’an da ke kula da gidan, inda hakan ya janyo gidajen, suka koma tamkar bigiren hada-hadar aikata muggan laifuka.

A ra’ayin wannan Jaridar, bankaɗowa da kuma ƙwace miyagun ƙwayoyin tare da kuma ƙwace Wayoyin 1,100, ba wai wani namijin ƙoƙari, Hukumar ta yi ba, kamar yadda ta ke shelanta cewa ta yi, amma kamata ya yi, Hukumar ta fi mayar da hankali, kan lamarin ƙalubalen da gidajen a ɗaukacin faɗin ƙasar, suke ci gaba da fuskanta.

Akuwar waɗannan matsalolin a gidan, hakan ya nuna cewa, har yanzu, akwai sauran Rina a Kaɓa, game da matsakaitan da gidajen ke ciki, duk da iƙirarin samar da sauye-sauyen da Hukumar ke cewa, ta gudanar.

Kazalika, ɗai yi wuya a san shin a tayaya ne, ake shigar da Wayoyin na Salula gidajen, idan har ba ta hanyar haɗa baki da wasu marasa kishin jami’an gidan ba.

A mafi yawancin lokuta, da irin waɗannan Wayoyin ne, ake yin amfani da su, a cikin gidajen, ake tsara yadda za a aikata muggan ayyuka, a cikin alumma kamar irinsu, garkuwa da mutane da fashin a yanar Gizo da fashi da makami.

Bisa waiwayen da wannan Jaridar ta yi, kan rikicin batun zargin da ya.wani fitaccen mai amfani da kafar sada zumunta Martins Otse, da aka fi sani da VeryDarkMan a watan Satumbar  2024 a tsakaninsa da fitaccen Ɗan Daudun nan, Idris Okuneye, da aka fi sani da Bobrisky, inda aka samu ɓullar wata muryar a faifan da aka naɗa, an ji Bobrisky, ya yi zargin cewa, ba a gidsn kason da aka tsare shi, ya kammala zamansa ba.

Bobrisky, a wancan lokacin, ya dage kai da fata cewa, a wani gida na da ban, aka tsare shi ta hanyar sa bakin wasu, masu faɗa aji.

Sai dai, kwamitin bincike, a rahotonsa da ya fitar kan batun ya ce, babu wani ƙamshin gaskiya, kan iƙirarin na Bobrisky, sai kwamtin ya tabbatar da cewa, Bobrisky, ya samu wata alfarma kan batun.

Batun dai, ya haifar da tayar da jijiyar Wuya da zargin cin hanci da rasahawa da cin mutuncin tsarin gidajen gyran hali, da wasu jami’an gidan gyran hali suka kitsa, domin su nuna fifiko, kan batun na Bobrisky.

A zahiri, batun ya wuce maganar ƙwace Wayoyin da kuma miyagun ƙwayoyi, amma babban mahimmancin shi ne, yin komai bisa ƙa’ida da kuma kare ƙimar hukumimim gwamnatin ƙasar.

Koda yake dai, za a iya cewa, Hukumar ya kamata a yaba mata, kan ƙoƙarin hukunta jami’anta, da aka samu hannunsu dumu-dumu, wajen taimaka wa shigar da waɗannan haramtattun kayan cikin gidajen da kuma ƙwace waɗannan kayan.

Haka zalika, abin da ake da matuƙar buƙata shi ne, ci gaba da samar da sauye-sauyen da za a inganta tsarin tare da ci gaba da sanya ido a gidajen.

Haka ya zama wajibi, mahukunta su mayar da hankali wajen ingnata rayuwar jami’an gidan gyran halin, musamman domin a daƙile karɓar na Goro, a tsakaninsu.

Dole ne kuma Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da zuba jari a fanin musamman a ɓangaren bayar da horo da sanya na’urorin sanya ido kamar na CCTV, a ɗaukacin gidajen.

Bugu da ƙari, ya zama wajbi, a samar da tsarin kula da lafiyar masu zaman jarun.

Lokaci ya yi da Gwamnatin Tarayya, mai maimakon shelar samar da sauye-sauye a fannin, amma ta tabbatar da dawo da nuna ɗa’a, domin dawo da ƙimar, tsarin.

Matuƙar Gwamnatin ba ta ɗauki wannan matakin ba, tsarin zai ci gaba da zama tamkar ƴar gidan jiya.

Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sallar Bana: Yadda Tsadar Ragunan Layya Ke Neman Dusashe Armashinta

Sallar Bana: Yadda Tsadar Ragunan Layya Ke Neman Dusashe Armashinta

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.