ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Komai Nisan Dare Gari Zai Waye

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Dare

Yadda sojojin kasar Amurka suka kutsa cikin kasar Venezuela, da sace shugaban kasar da matarsa a kwanan baya, ya nuna mana wani salon huldar kasa da kasa: Babbar kasa ta yi amfani da karfin tuwo wajen wulakanta, da shawo kan wata karamar kasa, da kwace dukiyoyinta yadda take so. A zahiri, wannan salon hulda ya yi hannun riga da bukatar tabbatar da daidaito da adalci a duniya, kuma ya saba da yanayin ci gaban al’ummar bil Adama.

Saboda halayyar mutum ta son ganin tabbatuwar adalci, al’ummun duniya suna Allah-wadai da kasar Amurka wadda ke daukar matakan zalunci, da yin kira da a kare hakkin Venezuela, da na sauran kananan kasashe. A sa’i daya kuma, batun ya sa ana kara fatan ganin wani misalin huldar kasa da kasa mai dacewa. Hakika ma iya cewa, huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wani misali ne mai kyau a wannan fanni.

Victor K’Onyango, shahararren dan jarida ne na kasar Kenya, wanda ya rubuta wani bayani da aka wallafa a jaridar “The Independent” ta kasar Uganda a kwanan baya, inda ya ce, cikin shekaru 20 da suka wuce, an gina dimbin hanyoyin mota, da layin dogo, da tashoshin jiragen ruwa, da yankunan masana’antu a kasashen Afirka. A cewarsa, wannan ci gaba ba aikin jin-kai da na tallafi ne suka haifar da su ba, dalilin cimma wadannan nasarori masu armashi, shi ne yadda kasashen Afirka suke yin hadin gwiwa da kasashen da suke kallonsu a matsayin abokai masu matsayin daidai-wa-daida. A ganin Victor K’Onyango, sauyin tunanin kasashen Afirka, daga dogaro kan samun tallafi daga ketare zuwa kulla huldar abota, ta riga ta zama tushen ci gaban masana’antun kasashen nahiyar. Kana huldar hadin gwiwa da aka kulla tsakanin Sin da Afirka tun tuni, ita ce babban dalilin da ya sa ake samun wannan sauyi na tunani.

ADVERTISEMENT

Kana a nasa bangare, Silence Charumira, babban editan shafin yanar gizo na “Africa News 24” na kasar Lesotho, shi ma ya rubuta wani bayani a kwanan baya, inda a cikinsa ya ce, huldar abota dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, ban da haifar da ci gaba a nahiyar Afirka, ta kuma yi amfani da wasu ka’idojinta na tushe, wato daidaito da cimma moriyar juna, da girmama ikon mulkin kan juna, da dai sauransu, wajen aza harsashi ga yunkurin kafa wani tsarin jagorancin duniya mafi adalci, da inganta kulawa da ayyuka daban daban.

A cewar Mista Charumira, alkaluma da misalan da aka samu cikin shekaru 5 da suka gabata, sun nuna yadda aka tabbatar da cikakken daidaito da adalci a huldar abota ta Sin da Afirka, inda ake ta gina kayayyakin more rayuwa, gami da samar da karin ma’aikata masu kwarewa; da kokarin dogoro da kai maimakon dogaro kan wasu; kana ana himmantuwa wajen raba fasahohi, maimakon tilasta wani bangare ya dauki wani salo na raya tattalin arziki da aka tilasta masa. A ganin Mista Charumira, huldar abota ta Sin da Afirka ta nuna cewa, za a iya maye gurbin salon raya tattalin arziki da na jagorancin duniya na baya, wanda ya ba kasashen yamma wani matsayi na jagora, kuma ya dace a dauki mataki don samar da sauye-sauye da ake son gani.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A daidai lokacin da nake rubuta wannan bayani, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, yana gudanar da ziyarar aiki a kasashen Habasha, da Somaliya, da Tanzania, gami da Lesotho, al’amarin da ya kasance karo 36 a jere, da ministan wajen kasar Sin ke ziyartar nahiyar Afirka a farkon duk sabuwar shekara. Ta wannan lamari za mu iya ganin sahihancin kasar Sin wajen karfafa zumunta tsakaninta da kasashen Afirka. Kana wannan sahihanci shi ma ya tabbatar da cewa, a ko da yaushe za a iya cin gajiyar huldar abota tsakanin Sin da Afirka.

Don tabbatar da makomar duniyarmu mai haske, ya kamata a yi kokarin samun karin huldodin kasa da kasa masu kama da huldar abota dake tsakanin Sin da Afirka. Idan dai a karkashin tasiri mai yakini da huldodin suka samar, kasashe masu tasowa za su iya karfafa hadin kansu a kai a kai, to, tabbas wata rana za a kai ga ganin bayan mulkin danniya da ake yi a duniya. Kamar dai yadda masu iya magana kan ce “Komai nisan dare gari zai waye.” (Bello Wang)

Dare
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Dare
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
APC Ga Atiku: Dimokuraɗiyyar Nijeriya Ba Ta Cikin Barazana

APC Ga Atiku: Dimokuraɗiyyar Nijeriya Ba Ta Cikin Barazana

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.