ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC

by Sadiq
2 months ago

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, a matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC na ƙasa.

Mai shari’a Musa Liman ya yi watsi da ƙarar da ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya shigar, yana mai cewa kotu ba ta da hurumin tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyyar.

Kotun ta kuma ce Abejide bai nuna yadda aka take wata doka ko haƙƙi ba, sannan bai bi hanyoyin sasanta rikicin cikin jam’iyyar ba kafin ya garzaya kotu.

ADVERTISEMENT

Kotun ta yanke cewa tsarin da ya bai wa David Mark shugabancin jam’iyyar da kuma tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, muƙamin Sakataren Jam’iyyar na ƙasa ya bi kundin tsarin mulkin ADC da kuma Dokar Zaɓe.

Haka kuma, ta ce miƙa shugabanci daga tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, zuwa David Mark an yi shi bisa doka.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Kotun ta umarci Abejide ya biya kowanne daga cikin waɗanda aka shigar da ƙarar tarar Naira miliyan biyu, sannan ta ci lauyansa tarar Naira miliyan 10 bisa tanadin Dokar Zaɓe.

Abejide, ya nemi kotun ta soke naɗin David Mark da Aregbesola tare da hana INEC amincewa da su a matsayin shugabannin ADC.

Sai dai daga baya ya fice daga jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 12, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Wang Yi Ya Zanta Da Takwaransa Na Amurka Ta Wayar Tarho

Wang Yi Ya Zanta Da Takwaransa Na Amurka Ta Wayar Tarho

LABARAI MASU NASABA

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.