ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Yi Gwanjon Kaddarorin Sani Sha’aban Bisa Taurin Bashi

by Bello Hamza
1 month ago
Kotu

Sashen Sheriff da Gudanar da Hukunce-hukuncen Farar Hula na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya yi gwanjon wasu kadarori mallakin tsohon dan majalisar tarayya, Alhaji Mahmood Sani Sha’aban, sakamakon wata takaddama ta bashi da ta dade tana gudana tsakaninsa da dan kasuwa Alhaji Umar Faruk Abdullahi, a ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026.

Kadarorin da kotun ta yi gwanjonsu sun hada da fili da gine-ginen da ke bayan babban gidan Sha’aban da ke gaban Makarantar Sakandaren Therbow a Zariya, mai Takardar Shaidar Mallaka (C of O) mai lamba KD 3984; da kuma fili da gine-ginen da ke kan Plot No. 3, Churchill Road, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 11226.

Sauran kadarorin sun hada da fili da gine-ginen da ke Tulips, mahadar MTD da ke gefen titin Kueen Elizabeth, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 15052, da kuma kamfanin Mazari Nails Limited da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kano, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 6246.

ADVERTISEMENT

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala gwanjon, Mista Abdullahi Yahaya, SAN, lauyan Umar Faruk Abdullahi ya ce abin da aka gudanar a ranar shi ne gwanjo da sayar da kadarorin wanda ake bin bashi kamar yadda hukuncin Babbar Kotun Shari’a ta 1 da ke Zariya ya tanada.

Ya kara da cewa kotun ta kwace kadarori guda biyar na wanda ake bin bashin, inda hudu daga cikinsu suke a Zariya, yayin da daya ke Kano.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

“Ya zuwa yanzu mun yi gwanjon kadarorin da ke Zariya, yayin da za a gudanar da gwanjon kadarar da ke Kano a wani lokaci nan gaba,” in ji Yahaya.

Idan zaa tuna ita wannan shari’ar ta samo asali ne daga wata yarjejeniyar bashi da aka kulla a shekarar 2018 tsakanin Hon. Sani Mahmud Sha’aban (Dan Buran Zazzau) da Alhaji Umar Faruk Abdullahi domin taimaka wa Sha’aban wajen warware wata matsala da ta shafi kama shi da tsare shi a gidan yari a kasar Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a shekarar 2018.

A karkashin yarjejeniyar, mai bin bashin ya bai wa Sha’aban rancen Dala miliyan daya ta Amurka (US$1,000,000) da kuma Naira miliyan 11.2 ba tare da ruwa ko karin riba ba, bisa tsarin shari’ar Musulunci. Lauyoyin Sha’aban ne suka tsara kuma suka shaida yarjejeniyar, yayin da dansa ya sanya hannu a madadinsa, sa’ilin da shi kan shi Sani Sha’aban din bayan dawowar shi daga gidan yari ya sake sanya hannu don tabbatar da amincewarsa da yarjejeniyar.

Daga bisani, Sha’aban ya biya Dala 290,762 daga cikin bashin dala miliyan daya, da ake bin shi amma daga baya ya ki biyan sauran kudin da suka rage. Daya daga cikin sharuddan yarjejeniyar ita ce a biya bashin cikin watanni shida kuma da irin kudin da aka karba.

A ranar 12 ga Fabrairu, 2024, Babbar Kotun Shari’a ta 1 da ke GRA Zaria ta umarci Sani Sha’aban, tsohon dan takarar gwamnan Jihar Kaduna, da ya biya bashin Dala 709,238 da kuma Naira miliyan 11.2 ga Alhaji Umar Faruk Abdullahi.

Kotun ta kuma bayar da umarnin kwace kadarorin Sha’aban da aka jingina a matsayin lamunin tabbatar da bashin.

Sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin, Sani Sha’aban ya garzaya inda ya shigar da korafi mai dalilai takwas a Kotun Daukaka Kara ta Shari’a ta Jihar Kaduna a ranar 13 ga Fabrairu, 2024.

Ya kuma nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin, saidai kuma Babbar Kotun Shari’a ta GRA Zaria ta yi watsi da bukatar, sannan daga bisani Kotun Daukaka Kara ta Shari’a ta Kaduna ma ta yi watsi da ita.

Daga nan ya sake garzayawa zuwa Sashen Daukaka Kara na Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke Kaduna, inda shi ma ya sha kaye. A ranar 29 ga Satumba, 2025, kotun ta tabbatar da hukuncin da karamar kotu ta yanke.

Kwafin sahihin hukuncin da wakilinmu ya samu a cikin Shari’a mai lamba KDH/Z/12A/2024 ya nuna cewa kotun ta umarci Sha’aban, da ya biya dukkan kudaden da kotun ta yanke a cikin Naira da Dala ga Babban Magatakardar Babbar Kotun Jihar Kaduna.

Kwamitin alkalan da Mai Shari’a Bilkisu Mohammed da Mai Shari’a Nana Fatima Mohammed suka jagoranta ya bayyana cewa ana iya aiwatar da hukuncin kudi sai dai idan wanda ya shigar da kara ya tabbatar da cewa wanda zai karbi kudin ba zai iya mayar da su ba idan daukaka karar ta yi nasara.

Kotun ta ce:

“Babu wani abu a gabanmu da ke nuna cewa wanda ake kara ba shi da hali kuma ba zai iya mayar da kudin hukuncin ba idan daukaka karar ta yi nasara.”

Alkalan sun kara da cewa kotuna ba sa son hana wanda ya yi nasara a shari’a cin moriyar hukuncin da ya samu, amma an bayar da sharadin dakatar da aiwatar da hukuncin ne domin tabbatar da adalci.

Hukuncin ya tabbatar da kiyaye kudaden da aka yanke yayin da ake ci gaba da aiwatar da matakan karbar bashin karkashin kulawar kotu.

A halin yanzu, Umar F. Abdullahi, wanda ya samu hukuncin kotu, ya samu izini daga Babbar Kotun Jihar Kano domin aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Shari’a ta 1, GRA Zaria ta yanke na sayar da kadarorin wanda ake bin bashin.

Kadarar da ke lamba 48, Yusuf Road, kusa da Hadejia Road, Bompai, Kano, na daga cikin kadarorin da aka jinginar domin tabbatar da bashin.

Sashen Sheriff da Gudanar da Hukunce-hukuncen Farar Hula na kotun ya sanya ranar 13 ga Yuni domin gudanar da gwanjon wannan kadara bisa umarnin da Mai Shari’a Faruk Lawan Adamu ya bayar a ranar 4 ga Mayu.

Kotu
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba

MASU ALAKA

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027
Labarai

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Siyasa

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Wasu Ma’aurata A Abuja

Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Wasu Ma'aurata A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026
Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

July 16, 2026
Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

July 16, 2026
Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.