ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Wasu Ma’aurata A Abuja

by Abubakar Sulaiman
1 month ago

Jami’an rundunar ‘yansandan Abuja sun daƙile wani yunƙurin garkuwa da wasu ma’aurata a yankin Byazhin da ke Abuja, bayan fafatawa da suka yi da waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

A yayin farmakin, jami’an sun ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya, da sinƙin harsasai da kuma harsasai bakwai.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce jami’an sashin yaƙi da garkuwa da mutane sun samu bayanan sirri kan motsin wasu da ake zargi a kusa da yankin Redeemed Church da ke Byazhin.

ADVERTISEMENT

Da isarsu wurin da misalin ƙarfe 12:34 na dare, sun tarar da maharan na ƙoƙarin shiga wani gida ta ƙarfi da yaji domin yin garkuwa da mazaunansa.

Ta ce da maharan suka hango jami’an tsaro sai suka buɗe musu wuta, lamarin da ya haddasa musayar harbi na sama da mintuna 30. Daga bisani jami’an suka fatattaki maharan, waɗanda suka tsere cikin daji ɗauke da raunukan harbin bindiga.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

An ceto ma’auratan da aka bayyana sunayensu da Mista Samson da matarsa ba tare da sun ji rauni ba.

Daga bisani an kai su Asibitin Gwarinpa domin kula da lafiyarsu, yayin da Kwamishinan ‘Yansanda na FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya yaba wa jami’an tare da umartar ƙara tsaurara sintiri da matakan tsaro a yankin.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark
  • Abubakar Sulaiman
    Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
An Yi Tir Da ‘Yan Takarar Da Suka Fice Daga APC Saboda Faduwa Zabe

An Yi Tir Da ‘Yan Takarar Da Suka Fice Daga APC Saboda Faduwa Zabe

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.