ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, October 29, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar El-Rufai Ta Hana ICPC Da EFCC Kulle Asusunsa

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago
El-Rufai

Babban Kotun Tarayya da ke birnin Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta yi watsi da ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shigar da nufin hana hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa kulle asusun bankunansa a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2026.

El-Rufai ya shigar da ƙarar ne a gaban kotun yana neman a ba da umarnin hana Hukumar EFCC da ICPC, da DSS, da kuma Atoni-Janar na Ƙasa (AGF) neman izini ko aiwatar da duk wani umarni na kulle asusunsa ko ƙwace kadarorinsa.

A cikin takardun ƙarar, El-Rufai ya buƙaci kotun ta ba da kariya ga asusun bankunansa daban-daban, waɗanda suka haɗa da:

ADVERTISEMENT
  • Asusun Naira a Bankin Zenith (Zenith Bank Plc: 1007158671)
  • Asusun Kuɗaɗen Ƙasashen Waje a Bankin Zenith (Zenith Bank Plc Domiciliary: 5071511327)
  • Asusun Bankin Guaranty Trust (GTB Plc: 0023824978)
  • Asusun Dala a Bankin Access (Access Bank Dollar Account: 1396386493)
  • Asusun Naira a Bankin Access (Access Bank Naira Account: 1396382103)

Tsohon gwamnan ya kafa hujja da sashi na 36(5) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima) da sashi na 17(1) na Dokar Yaƙi da Zamba ta 2006, yana mai jayayyar cewa a matsayinsa na ɗan ƙasa yana da haƙƙin a ɗauke shi marar laifi har sai an tabbatar, kuma kulle asusunsa ba tare da kwararan hujjoji ba zai tauye masa haƙƙin samun shari’a mai adalci.

Sai dai a nasu ɓangaren, hukumomin da ake ƙara sun ƙalubalanci shari’ar. Hukumar ICPC ta nuna cewa El-Rufai ya shigar da makamantan waɗannan ƙararraki a gaban Babban Kotun Tarayya da kuma Babban Kotun Birnin Tarayya (FCT High Court), lamarin da zai iya haifar da karo a hukuncin kotuna masu matsayi ɗaya.

LABARAI MASU NASABA

Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin Da ‘Yan Daba Suka Kai Wa Magoya Bayan APC Hari A Katsina

Sojoji Sun Kama Mutane 2 Kan Ƙone Ofishin ’Yan Banga A Jos

A madadin Atoni-Janar na Ƙasa (AGF), Daraktar Ƙararrakin Farar Hula da Dokokin Gwamnati, Maimuna Lami-Shiru, ta bayyana cewa buƙatun El-Rufai zato ne kawai, kuma hukumomin bincike suna da cikakken ikon doka na neman umarni domin gudanar da bincike.

A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da hujjojin waɗanda ake ƙara, inda ta bayyana cewa ƙarar da El-Rufai ya shigar ta zama cin zarafin tsarin tafiyar da shari’a (abuse of court process).

Alƙaliyar ta jaddada cewa doka ba ta ba da damar a yi amfani da kotu wajen hana hukumomin tsaro da na tabbatar da doka gudanar da ayyukansu da doka ta tanadar musu ba.

El-Rufai
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata
  • Abubakar Sulaiman
    ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

MASU ALAKA

Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin Da ‘Yan Daba Suka Kai Wa Magoya Bayan APC Hari A Katsina
Manyan Labarai

Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin Da ‘Yan Daba Suka Kai Wa Magoya Bayan APC Hari A Katsina

October 29, 2026
Sojoji Sun Kama Mutane 2 Kan Ƙone Ofishin ’Yan Banga A Jos
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Mutane 2 Kan Ƙone Ofishin ’Yan Banga A Jos

October 29, 2026
Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a
Manyan Labarai

Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

October 28, 2026
Next Post
Ragin Farashin Fetur: Tasirinsa Ga Sufuri, Farashin Kayan Masarufi

Sin Ta Damu Matuka Game Da Ci Gaba Da Tashin Hankali A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Damu Matuka Game Da Ci Gaba Da Tashin Hankali A Yankin Gabas Ta Tsakiya

October 28, 2026
Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

October 28, 2026
Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

October 28, 2026
Tsibirin Lemu: Wuri Mai Ni’ima Da Ke Kunshe Da Tarihin Gwagwarmayar Kafuwar Kasar Sin

Tsibirin Lemu: Wuri Mai Ni’ima Da Ke Kunshe Da Tarihin Gwagwarmayar Kafuwar Kasar Sin

October 28, 2026
Sin Da Gambia Sun Gudanar Da Taron Musayar Kwarewa A Kungiyar Ciniki Ta Duniya

Sin Da Gambia Sun Gudanar Da Taron Musayar Kwarewa A Kungiyar Ciniki Ta Duniya

October 28, 2026
Sin Ta Yi Kira Da a Gaggauta Tsagaita Bude Wuta Tare Da Yin Tattaunawa Cikin Ruwan Sanyi Tsakanin Amurka Da Iran

Sin Ta Yi Kira Da a Gaggauta Tsagaita Bude Wuta Tare Da Yin Tattaunawa Cikin Ruwan Sanyi Tsakanin Amurka Da Iran

October 28, 2026
Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

October 28, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

October 28, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.