ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ta Hanyar Kyautata Fasahar Makamashi Kasar Sin Na Samar Da Damar Raya Kasa Ga Sauran Kasashe

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago

A duniyarmu, akwai kasar da ta kan ambaci burinta na sake zama wata kasa mai karfi. Sai dai mai karfi ba ya nufin wanda za a iya ta da rikici a duniya, ko kuma cin zarafin sauran kasashe yadda ya ga dama.

Hakika karfin wata kasa yana bayyana ne kawai ta hanyar kiyaye wani yanayi na ci gaban tattalin arzikinta, gami da raba damar ci gaba tare da sauran kasashe, a lokacin da ake fama da yanayin rashin tabbas da kwanciyar hankali a duniya.

A kwanakin nan, kasar Sin ta sanar da alkaluman tattalin arzikinta a rubu’in farko na bana, wadanda suka nuna cewa, jimillar GDPn kasar ta karu da kaso 5% idan an kwatanta da jimilla ta makamancin lokacin shekarar bara, inda ta kai wani matsayi na koli bisa burin karuwar GDP da kasar ke neman samu a shekarar 2026, wato tsakanin 4.5% da 5%.

ADVERTISEMENT

Sai dai ta yaya kasar Sin ta tabbatar da karuwar tattalin arzikinta cikin sauri, yayin da ake fuskantar tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya, da hauhawar farashin man fetur a wurare daban daban na duniya? To, wani babban dalilin da ya sa haka shi ne ci gaban kasar Sin a fannin sabunta nau’in makamashi.

Kasar Sin a matsayinta na kasa mafi karfin masana’antu a duniya, ta fi shigowa da danyen mai daga sauran kasashe. Kuma ta san cewa, don tabbatar da tsaro a fannin makamashi, abu mafi muhimmanci ba sayo karin mai daga mabambantan kasashe ba ne, a’a, abun yi shi ne rage dogaro kan makamashi na mai.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Saboda haka kasar Sin ta dade tana kokarin raya makamashi mai tsabta. Zuwa yanzu, kasar Sin tana kan gaba a duniya cikin shekaru 15 a jere, a fannin girke na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska.

Kana kasar ta zama ta farko a duk fadin duniya cikin shekaru 10 a jere, ta fuskar kafa tashoshin samar da lantarki ta hasken rana.

Ya zuwa karshen shekarar 2025, kasar Sin ta riga ta kafa wani tsarin makamashi mai tsabta mafi girma a duniya a cikin gidanta, inda yawan makamashi mai tsabta da ta yi amfani da shi a cikin dukkan makamashin da ta samar ya kai kaso 21.7%.

Sai dai hade tattalin arzikin Sin da na sauran kasashe, ya sa ci gaban kasar Sin shi ma ya haifar da ci gaba a sauran kasashe. Zuwa yanzu, kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasashe da yankuna fiye da 100 a fannin makamashi mai tsabta, kana ta samar da fiye da kaso 80% na na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana da ake amfani da su a duniya, da kaso 70% na na’urorin samar da lantarki ta karfin iska.

Ban da haka, kasar ta yi kokarin raba fasahohin raya tattalin arziki ta dabaru masu kare muhalli ga sauran kasashe, inda ta samar da horo ga mutane fiye da dubu 10 na kasashe masu tasowa fiye da 120, zuwa karshen shekarar 2025.

Dangane da rawar da kasar Sin ke takawa a fannin sabunta nau’in makamashi a duniya, wani marubuci mai suna Akin Yusuf, ya rubuta a cikin wata makalarsa da aka wallafa a jaridar Independent ta Najeriya cewa, kasar Sin abokiya ce da ake iya dogaro da ita, yayin da ake neman raya makamashi mai tsabta.

A cewarsa, “Ba kamar kasashen yamma ba, kasar Sin ba ta gindaya sharadin siyasa, kuma ba ta neman yin babakere a fannin mallakar fasahohi, yayin da take samar da fasahohi da kayayyaki masu alaka da sabon makamashi ga kasashe masu tasowa.

A ko da yaushe, kasar Sin tana tsayawa kan manufar samun daidaito da tabbatar da moriyar juna, inda ba kawai tana samar da fasahohi da kayayyaki ga sauran kasashe masu tasowa ba ne, har ma tana ba su taimako wajen horar da kwararru.” Mista Akin Yusuf ya kuma kara da cewa, bisa karfinta a fannin kimiyya da fasaha, da niyyarta ta sauke nauyin dake bisa wuyan babbar kasa, Sin ta samar da fasahohin sabunta makamashi, da raya tattalin arziki ga sauran kasashe masu tasowa. (Bello Wang)

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Matan APC A Kaduna Sun Gargadi Masu Shirin Zanga-zanga

Matan APC A Kaduna Sun Gargadi Masu Shirin Zanga-zanga

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.