Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar, bayan ya samu kuri’u 511,067 a karkashin jam’iyyar Accord.
Sakamakon karshe da aka fitar ya nuna cewa jam’iyyar Accord ce ta samu kuri’u mafi yawa, inda ta kayar da jam’iyyar APC, wadda ta samu kuri’u 444,815 da kuma Jam’iyyar ADC da ta samu kuri’u 17,180.
A cewar alkaluman sakamakon zaben, jimillar masu rijistar zabe a jihar Osun sun kai mutane 2,339,544, yayin da adadin wadanda aka tantance kafin kada kuri’a suka kai 1,010,684.
Daga cikin kuri’un da aka kada, kuri’u 1,005,800 ne aka samu a matsayin jimillar kuri’un da aka kada. Daga ciki kuma Kuri’u 985,079 ne aka ayyana a matsayin sahihai, yayin da kuri’u 20,721 aka soke saboda rashin inganci.
Sakamakon ya nuna cewa Adeleke ya samu tazarar kuri’u 66,252 tsakaninsa da dan takarar APC, inda Accord ta samu kuri’u 511,067, yayin da APC ta samu 444,815.
Wannan nasara ta bai wa Adeleke damar ci gaba da rike jagorancin gwamnatin Jihar Osun, bayan da ya samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben.













