ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwastam Ta Kama Jabun Magunguna Da Miyagun Ƙwayoyi A Legas

by Sulaiman
3 months ago
Kwastam

Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ta kama magungunan jabu masu ɗauke da lambar rajistar NAFDAC ta bogi, miyagun ƙwayoyi da kuma magungunan da wa’adinsu ya ƙare, waɗanda jimillar ƙimarsu bayan biyan haraji ta kai Naira biliyan 53.39 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da Legas.

Hukumar ta bayyana kamen a matsayin wani babban ci gaba a ƙoƙarinta na kare lafiyar al’umma da kuma tsaron ƙasa.

Da yake jawabi yayin miƙa waɗannan miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adinsu ya ƙare ga hukumomin da abin ya shafa a hedikwatar rundunar Apapa a ranar Laraba, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce an samu nasarar kama kayayyakin ne sakamakon tattara bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa tsakanin Kwastam da NDLEA.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, kayayyakin da aka kama sun haɗa da sama da tan 6.7 na tabar wiwi da aka ɓoye a cikin kwantena biyu masu ƙafa 40 tare da motocin da aka shigo da su da kuma kayan gyaran motoci.

Sauran abubuwan da aka kama sun haɗa da kwalabe 339,800 na maganin tari mai ɗauke da sinadarin Codeine, kwantenoni da dama na magungunan da wa’adinsu ya ƙare, maganin yara na Piccan Teething Powder, da kuma magungunan jabu masu ɗauke da lambobin rajistar NAFDAC na bogi.

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Ƙaddamar Da Aikin Ceto Limaman Da Aka Sace Bayan Taron APC A Zamfara 

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Adeniyi ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin kayayyakin da aka kama ya ƙunshi fakiti 1,100 na maganin CHACOLD Chlorpheniramine Maleate Capsules, waɗanda ke ɗauke da lambar rajistar NAFDAC ta bogi tare da ƙarin ranar ƙarewar wa’adi ta ƙarya.

Kwastam
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya
  • Sulaiman
    Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
  • Sulaiman
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

MASU ALAKA

Dansanda Ya Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 1 Kan Ya Saki Wani Barawon Mutane A Kano
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Ƙaddamar Da Aikin Ceto Limaman Da Aka Sace Bayan Taron APC A Zamfara 

September 14, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola
Manyan Labarai

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Next Post
An Gudanar Da Bikin Murnar Cika Shekaru 29 Da Dawowar Yankin Hong Kong Kasar Sin

An Gudanar Da Bikin Murnar Cika Shekaru 29 Da Dawowar Yankin Hong Kong Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

September 14, 2026
Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

September 14, 2026
Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

September 14, 2026
Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

September 14, 2026
Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

September 14, 2026
Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

September 14, 2026
Kwastam

Babu Dalilin Da Zai Sa Nijeriya Yin Talauci – Obasanjo

September 14, 2026
Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

September 14, 2026
Kwastam

Air Peace Da United Nigeria, Jirage 2 Masu Latti Sosai Watan Agusta — NCAA

September 14, 2026
Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.