Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, a wannan hira da Editocin Jaridar LEADERSHIP, ya yi magana kan rikicin cikin jam’iyyar PDP, halin da Majalisar Tarayya ke ciki, da kuma bukatar kafa ‘yansandan jihohi.
Ka taba zama shugaban kwamitin sasanta rikicin PDP sau da dama. Me ya sa ya zama da wahala PDP ta daidaita al’amuranta tun bayan da ta rasa mulki a matakin tarayya? Kuma me ka gani a matsayin babban abin da ke hana hadin kai?
Ya fi zama kalubale idan ba ku ne ke kan mulki ba. Ikon umarni da aiwatarwa ba abu ne mai sauki ba, a takaice.
Matsalar ita ce mutane suna da ra’ayoyi da matsayi daban-daban. Don haka kullum kana fama da mutane masu halaye daban-daban, suna da sabani, kuma babu wanda yake sauraron wani sosai. Idan kuna kan mulki, kullum akwai shugaban kasa, ko kuma kamar yadda yake a lokacin da PDP ke mulki, ya fi saukk a sasanta sabani.
Amma idan kuna jam’iyyar adawa, dole ne a rika yin sassauci da juna, domin babu wanda ya fi wani iko. Ba za ka iya kawai ka ce fadar shugaban kasa ta yanke hukunci, kuma kowa ya bi ba.
Idan kuma jam’iyyar adawa ce mai cike da manyan mutane tsofaffin gwamnoni, sanatoci, shugabannin majalisar dattawa, mataimakan shugabannin kasa, har ma da tsofaffin shugabannin kasa lallai lamarin yana bukatar hakuri da sadaukarwa sosai.
Mutane suna da son kai da girman kai daban-daban, amma dole ne a yi kokari a fifita jam’iyya, kasa da dimokuradiyya gaba. Kuma a cikin hakan, kalubale ba za su taba karewa ba.
Abin takaici, duk da cewa jam’iyya mai mulki na son mu yarda cewa duk abin da muke gani yana faruwa ne kawai a cikin jam’iyyarmu, mun san cewa akwai abubuwa da ke faruwa a wajen jam’iyyar da ke tasiri ga abin da ke faruwa a cikinta. Don haka, bai kamata mu yaudari kanmu ba. Wannan wani bangare ne na yanayin da muke ciki a yau, kuma dole mu yi la’akari da shi tare da neman mafita. Tun bayan zabe muke fama da wannan, kuma kokarin da wasu daga cikinmu suka yi ya kawo mu wannan mataki.
Idan ka lura, har zuwa yanzu PDP ita ce kadai babbar jam’iyyar adawa da ba ta kai ga rarrabuwar kawuna zuwa bangarori biyu ba. Akwai matsaloli, amma kullum muna kokarin dakile su, abin takaici, abin da ya kai ya faru ga Ibadan inda wasu daga cikinmu muka yi ta gargadi cewa kada a bi wannan hanya, amma duk da haka aka bi.
Mun yi tarurruka da dama domin ci gaba da sarrafa rikicin, amma abin takaici hakan ya faru. Yanzu muna kokarin janyewa daga wannan hali, kuma mun fara hakan. Kamar yadda muka sani, kotu ba ita ce wurin warware matsalolin siyasa ba; dole ne a koma teburin tattaunawa domin samun mafita.
Don haka, lamarin ya yi wahala, amma wannan abu ne da aka saba gani a jam’iyyun adawa, musamman manya. Kuma idan har jam’iyya mai mulki tana tsoma baki a cikin harkokin jam’iyyarmu, dole ne a sa ran irin wannan kalubale, wannan wani bangare ne na gwagwarmayar da muke yi.
Amma abin da ke karfafa mana gwiwa shi ne cewa, a zahiri, idan ka sauka zuwa kasa, PDP har yanzu suna ne da ya kafu a zukatan jama’a. Ka je kauyuka da garuruwa, za ka ga cewa jam’iyyar tana nan a zuciyar mutane. Ba abu ne da za a iya gogewa ba. Rikice-rikice irin wannan ba za su iya rushe jam’iyyar ba.
Shi ya sa wasu masu sharhi kan ce PDP ta mutu, amma idan ka zagaya jihohi, har yanzu PDP ita ce babbar jam’iyyar adawa. Don haka, na yi imani cewa mu a matsayin shugabanni muna da alhakin nemo mafita, ko da kuwa yana da wahala. Kuma ina ganin mun yi kokari sosai amma har zuwa taron Ibadan bai kasance da sauki ba, amma muna ci gaba da rike jam’iyyar a hade.
Abin takaici, mun yi kurakurai a can, kuma hakan ne ya kai mu kotu. Yanzu dole mu fito daga kotu mu koma teburin tattaunawa. Wannan shi ne abin da muke son yi a cikin kwanaki masu zuwa, wanda zai kai mu ga babban taron jam’iyya. Da fatan bayan wannan taro za mu iya haduwa mu yi abu mafi muhimmanci da ‘yan Nijeriya ke son gani wato PDP ta kasance a takardar zabe a shekarar 2027.
Ka ambaci batun son kai (ego) tsakanin wasu shugabanni. Manyan mutane biyu a jam’iyyar yanzu, Ministan FCT da Gwamnan Jihar Oyo na fama da sabani. Ta yaya jam’iyyar ke kokarin warware wannan matsala a yanzu?
Mu bar batun mutum daya, mu duba matsayin al’amura gaba daya. A yau, mafi yawan mambobin PDP, masu goyon bayanta, da ‘yan Nijeriya da suka ga amfaninta lokacin da take mulki, suna da ra’ayi guda: dole PDP ta kasance a takardar zabe a 2027.
Dole ne a yi duk mai yiwuwa domin bai wa mutane damar tsayawa takara a karkashin PDP. Ina farin cikin cewa, duk da sabanin da ke tsakanin bangarori, kowa ya amince cewa wannan shi ne babban buri. Ko kai Gwamna Seyi Makinde, ko Gwamna Bala, ko Ministan FCT, ko wani abu na farko shi ne PDP ta gabatar da ‘yan takara a 2027.
Duk wani abu da zai hana hakan, dole ne a ajiye shi a warware. Wannan shi ne matsayin da muka kai yanzu, kuma ba abu ne mai sauki ba, amma muna fatan za mu ci gaba da rike wannan matsayi.
Hanyoyin da za su kai mu ga hakan a bayyane suke. Dole ne mu samu Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) da zai jagoranci wannan aiki. A baya, wasu daga cikinmu sun ba da shawarar kafa kwamitin riko domin kauce wa wannan rikici, sannan bayan zabe na 2027 a gudanar da babban taro, amma hakan bai faru ba.
Yanzu, kotu ta yanke hukunci wanda ya kusan soke wani taro, ta kuma bude damar sake gudanar da wani taro. Wannan ita ce hanya guda tilo domin zabar sabon NWC. Abin da ake bukata yanzu shi ne kowa ya hada kai a kan wannan. A yi sassauci nan da can domin kowa ya ji ana damuwa da shi. Amma duk wannan dole ne ya bi bayan babban buri guda PDP ta gabatar da ‘yan takara a 2027.
Don haka, abin da ake tattaunawa yanzu shi ne: mu amince wannan shi ne babban buri. Na biyu, yadda za a hada mutane da dama a wannan tafiya. Ta yaya za a lallashi wadanda ke bukatar a lallashe su, ta yaya wadanda suka yi nasara a kotu za su nuna karamci, a dauki hakan a matsayin nasara ta kow, nomin nasara ta gaskiya ita ce idan an warware dukkan matsaloli, kuma babu sauran shari’o’i.
Hakan ne ya kai mu ga hanya guda da ta rage wato babban taro da za a yi a karshen mako. Ina fatan zai yi nasara, kuma a ga INEC ta halarta, domin su ne masu sa ido, kuma daga nan ne za a samu sahihanci da ingancin tsarin.
Idan aka ga INEC a wurin, za mu san cewa yanzu muna da jam’iyya da za ta iya gudanar da zabukan fidda gwani ga ‘yan takara. Idan muka cimma hakan, sakon da za a aika ga jama’a shi ne PDP ta dawo kan turba.
Daya daga cikin dalilan da ya sa muke rasa mutane da dama shi ne fargabar masu son tsayawa takara, wadanda ke ganin da wannan rikici ba za mu iya gabatar da ‘yan takara ba.
Amma idan muka aiwatar da abubuwan da muke cewa za mu yi, ba za mu ci gaba da haifar da shari’o’i da ke tambayar sahihancin shugabannin NWC ba. Idan INEC ta halarta, an yi taro, kuma shugabannin da aka zaba suna da ikon gudanar da zabukan fidda gwani, to PDP ta daidaita daga wannan bangaren. Wannan ita ce hanya guda da take akwai a yau, gaskiya kenan.
Kana ganin babban taron kasa na Abuja yana daya daga cikin hanyoyin magance rikicin PDP?
Ita ce hanya guda tilo a halin da muke ciki yanzu. Abin da ya kamata mu yi shi ne mu amince da hakan. A yau babu wata hanya daban da za ta ba mu damar samun Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) da ya dace da Dokar Zabe da ka’idojin INEC, wanda zai tabbatar da cewa ‘yan takarar da za su fito sun halatta a doka.
Yanzu, me ya sa wasu ba su gamsu ba? A fili yake cewa akwai wasu mutane da a baya suke ganin su ne shugabanni kamar shugabanni, sakatarori, mataimakan sakatarori, masu binciken kudi, amma yanzu sun rasa wadannan mukamai.
Amma da yake mu iyali daya ne, bai kamata a dauki cewa wani ya yi asara ba. Asara ta gaskiya ita ce idan ba za mu iya gabatar da ‘yan takara ba wannan asara ce. Amma idan dan uwa daya ne ya zama sakatare ko shugaban jam’iyya maimakon wani, bai kamata a dauki hakan a matsayin asara ba.
Idan hakan zai ba mu damar cike guraben tsayawa takara, to dukkanmu mun yi nasara. Wannan shi ne tunanin da muke kokarin yada wa a cikin PDP. Idan muka iya cimma hakan, ina ganin mun yi nisa sosai kuma mun samu gagarumar nasara.
Kana nuna alamar fata da kyakkyawan zato. Amma tabbas akwai damuwa cewa wannan babban taron na iya kara tsananta ko zurfafa rikicin cikin (PDP).
Babbar abin da ke zuciya shi ne ga duk wani mamba na gaskiya a PDP, duk wanda ke son PDP da gaske, duk wanda ya yi imani cewa PDP wata hanya ce da zai iya amfani da ita wajen bayyana burinsa ko tsayawa takara, ko kuma ya yi imani PDP na iya samar da gwamnati mai kyau, to babban abin da ya fi muhimmanci shi ne zabukan fidda gwani. A yi duk abin da ya dace, ku shugabanni da mambobin PDP, ku yi duk abin da ya kamata, ku tabbatar PDP ta gabatar da ‘yan takara a zaben 2027. Wannan shi ne babban abin da ya fi muhimmanci ga duk mai son PDP.
Bayan wannan ne ake maganar bukatu na mutum daidai. Bukatun mutum kamar cewa: “Na lashe zabe a Ibadan, an zabe ni a matsayin sakataren yada labarai, yanzu na rasa wannan mukami, ina matsayina?” A nan ne ake bukatar sadaukarwa.
Idan da akwai wata hanya daban da za ta taimaka mana mu ci gaba da hadin kai, saboda lokaci ba ya tare da mu, wannan ma wata matsala ce da za mu iya bi wasu hanyoyi. Da za mu ce muna da lokaci, mu ci gaba da gwagwarmaya har ma zuwa Kotun Koli. Amma ba mu da lokaci.
Babu amfani ka ci yaki daya ka rasa yaki gaba daya. Yakin da muke magana a kai shi ne: PDP ta kasance a takardar zabe a 2027. Don haka, duk abin da muke yi dole ne ya ta’allaka ga wannan babban buri. Wannan shi ne kiran da ake yi.
Idan muka ce abubuwa ba za su tafi cikin sauki ba, abin da ka iya hana hakan shi ne mutane su ki yarda cewa akwai lokuta a siyasa da dole ne ka fifita babban buri fiye da naka. Wannan ba yana nufin kai kasa ba, ko ba ka da gaskiya ba. Amma idan ka duba al’amura ka ga cewa, idan burinmu shi ne PDP ta kasance a takardar zabe, to idan dole ne ka sadaukar da mukaminka ko ka yi hakuri da hakan, zaka iya yin hakan. Domin a nan gaba akwai damar wasu mukamai daban-daban.
Amma tarihi ba zai yi adalci ba ga duk wanda ya taka rawa a hana PDP fitowa a zabe. Don haka, bai kamata mu kalli lamarin a matsayin wani ya ci nasara ko wani ya sha kashi ba. Wannan ba shi ne hanyar da ya kamata mu bi ba. Wannan shi ne abin da muke kokarin cimmawa.
Kana da kwarin gwiwa cewa bangarorin biyu da ke cikin rarrabuwar kai a PDP za su halarci wannan babban taro yanzu?
Ina fatan ba za mu samu halartar kashi 100 daga bangarorin biyu ba. Ina fatan za mu samu kusan kusan 100 daga bangare daya, sannan 50 zuwa 60 daga dayan. Muna fatan mutane za su zo su hadu. Idan sun hadu, ina ganin ba za mu kara samun matsalar rarrabuwar kai ba.
Domin me muke fada kuma muke yi yaki a kai? Kamar yadda na fada tun farko, abin da ya kamata mu yi yaki a kai ko wane bangare kake a jam’iyyar, shi ne PDP ta kasance a jikin takardar zabe. Wannan shi ne abin da ya kamata mu yi yaki a kai. Duk sauran abubuwa za su zo daga baya ne.
Ko ni ne auditor, ko kai ne auditor; ni ne shugaban jam’iyya, ko kai ne shugaban, duk wadannan na biyu ne. Idan babu dandalin siyasa da mutane za su tsaya takara a kai, me ya sa za a bukaci jam’iyyar siyasa?
Wasu shugabannin PDP sun fito fili suna bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. Mene ne matsayinka a kan hakan?
To, ka kasance cikin wannan harkar siyasa na tsawon lokaci ka san cewa abin da mutane ke fada da abin da suke yi ba koyaushe yake daidai ba, kuma wani lokaci ana ganin gaskiyar abin da za su yi ne a karshe. Don haka, ko za a yi zabe gobe ne? A’a, ba gobe ba ne. Saboda haka wannan ba abin da nake damuwa da shi yanzu ba, domin mutane na fadin abin da suke so.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne: mun bari al’amura suka kai mu wannan matsayi. Wadanda suka tuna, kafin taron Ibadan, akwai babban dimuwa da tashin hankali, mutane suna da bege kan abin da PDP za ta yi. Amma idan ba mu gyara gidanmu ba, ba za mu sa jam’iyya ta zama mai karfi da za ta ja hankalin ‘yan takara masu kima ba. Don haka wannan tsarin da muke ciki yanzu wani bangare ne na shirya jam’iyyar domin zabe.
Ka san ‘yan siyasa, abin da suke fada ba lallai ne shi suke aikatawa ba. Zabe yana zuwa a Janairu na shekara mai zuwa. Muna cikin Maris 2026 akwai lokaci mai yawa a gaba. Don haka kada ka damu sosai. Mu dauki lamarin mataki-mataki.
Da farko, mu tabbatar mun gina jam’iyya. Idan aka fito daga wannan taron na karshen mako, mutane suka ga cewa jam’iyya ta fara daidaituwa, za a fara ganin kwanciyar hankali. Misali a jihata, mutane suna zuwa suna tambayar wasu daga cikin mutanena cewa, “Me kuke yi a PDP? Ba ku da jam’iyya mai karfi.” Wasu suna cewa na yaudare su su zauna a PDP. Za ka ga mutane da dama suna rikicewa suna gasgata hakan.
Don haka, idan mutane suka fara cewa PDP ba za ta iya fitar da ‘yan takara ba, mutane za su fara gasgatawa saboda abin da suke gani a yanzu. Amma idan muka wuce wannan mataki, in sha Allahu za a samu daidaito. Za ka fara ganin mutane suna dawowa, kuma za a fara samun ‘yan takara masu karfi a kowane mataki.
Akwai maganganu da ke karuwa cewa jam’iyyar PDP ba za ta iya dawo da martabarta a kasa ba, kuma tana iya raguwa kamar yadda jam’iyyu irin su AD da ANPP suka ragu a baya, musamman ganin yadda ta rasa gwamnoni 11 zuwa jam’iyyar APC cikin shekara guda. Mene ne ra’ayinka a kan wannan?
Gaskiya, wannan irin hasashe ba sabon abu ba ne a siyasar Nijeriya. Duk jam’iyya da ke fuskantar rikici, rabuwar kai, ko rashin daidaito a cikin shugabanci na iya fuskantar ra’ayoyin cewa tana “raguwa” ko za ta bace. Amma tarihi ya nuna cewa manyan jam’iyyun da ke da tushe mai karfi a al’umma ba sa bacewa cikin sauki.
PDP, duk da kalubalen da take fuskanta, har yanzu tana da: Karfi a matakin jihohi da kananan hukumomi. Sunan da mutane da dama har yanzu ke danganta da mulki. ‘Yan siyasa da magoya baya da dama a fadin kasa
Rashin gwamnoni 11 zuwa APC babban kalubale ne, kuma yana nuna akwai matsaloli na cikin gida, irin su rashin hadin kai, rikice-rikice na shugabanci, da kuma siyasar jam’iyya da ke jawo sauya sheka. Amma a lokaci guda, hakan ba yana nufin an kawo karshen jam’iyyar ba. Sauya sheka a siyasar Nijeriya abu ne da ake yawan gani, kuma yana iya sauyawa idan aka samu gyara a cikin gida.
Abin da zai fi zama mafi muhimmanci ga PDP shi ne: Ta warware rikicinta na cikin gida. Ta samar da tsayayyen shugabanci. Ta bai wa mambobinta kwarin gwiwa da damar shiga siyasa cikin adalci. Ta shirya kanta da kyau domin tunkarar zabe mai zuwa
Idan wadannan sun tabbata, jam’iyya za ta iya dawo da karfinta. Amma idan rikice-rikice suka ci gaba, to tabbas hakan na iya rage tasirinta a siyasa.
A’a, ko kadan ba haka ba ne. Ba haka ba, ba haka ba ne.
Ka ga, mutane da dama suna sane da abin da ke faruwa a Abuja. Ka je jihohi, ka tura mutane zuwa jihohi, ka yi bincike a wuraren da yawancin ‘yan Nijeriya suke. A ra’ayin mafi yawan ‘yan Nijeriya, jam’iyyu biyu ne kawai a kasa. Duk da hayaniyar da ake yi game da PDP, idan da gaske PDP ba ta da wannan kakkarfan tushe, ya kamata tuni ta bace a yawancin jihohi. Amma idan ka je jihohi da dama a yau, za ka ga PDP har yanzu tana da karfi sosai.
Eh, an samu matsaloli da yawa, kuma ba su taimaka mana ba, ni kaina zan fara amincewa da hakan. Amma a karshe, mutane suna tambayar kansu: “Me ya sa har yanzu ina cikin PDP?” Wasu suna ganin cewa a lokacin da PDP ke mulki, sun ga wasu fa’idodi da suke ganin suna ci gaba da amfani da su har yanzu. Saboda haka suna ba PDP dama har yanzu.
Ina da tabbaci cewa idan muka wuce wannan lokaci, musamman idan PDP ta shirya kanta da ‘yan takara, za ka ga mutane suna dawowa. A koyaushe ina fada cewa motar APC ta cika sosai. Ta yi nauyi fiye da kima. Ba sabon abu ba ne jam’iyyar ta ce tana da jihohi 30 ko sama da haka, amma hakan na iya kawo matsaloli.
Akwai yiwuwar rikice-rikice a ko’ina, ba saboda ba su san yadda ake tafiyar da lamura ba, a’a saboda yanayin siyasar Nijeriya ne. A cikin APC ma, za ka iya samun mutum 20 na neman kujera daya ta Sanata a wuri guda, ko 40 na neman majalisar wakilai, da wasu 10 na neman gwamna. Ta yaya za su daidaita wannan rikici?
Don haka za su fuskanci nasu kalubalen. Ni ba abin da ke damuna ba ne abin da yake faruwa a yanzu. Abin da nake mayar da hankali a kai shi ne mu gyara gidanmu. Zabe ba gobe ba ne. Muna da lokaci, mu bari mu ga yadda al’amura za su gudana.
Shin kana goyon bayan ra’ayin da shugabannin ‘yan adawa ke yi cewa Nijeriya na karkata zuwa tsarin jam’iyya daya a karkashin APC?
Wannan tambaya tana da muhimmanci, kuma a siyasar Nijeriya ana yawan tattaunawa a kai. Ra’ayin cewa kasa na “karkata zuwa jam’iyya daya” yawanci yana fitowa ne idan: Jam’iyya mai mulki tana samun rinjaye mai yawa a jihohi. ‘Yan siyasa suna sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki. Ana ganin raunin jam’iyyun adawa wajen hadin kai da tsari
A gefe guda kuma, wasu suna ganin cewa Nijeriya har yanzu tana da tsarin dimokiradiyya mai jam’iyyu da dama, inda jam’iyyu kamar PDP da sauran kananan jam’iyyu suke ci gaba da wanzuwa da kuma fafatawa a zabe a matakai daban-daban.
Gaskiyar magana ita ce: Yawan sauya sheka na ‘yan siyasa ba lallai ya nufin kasa ta zama jam’iyya daya kai tsaye. Amma idan jam’iyyar adawa ta kasa gyara kanta, ta rasa hadin kai, ko ta kasa ba da kwarin gwiwa ga ‘yan takara da masu jefa kuri’a, hakan na iya rage karfinta Dimokiradiyya mai karfi tana bukatar jam’iyyun adawa masu karfi, domin su samar da madadin zabi ga al’umma
Don haka, damuwar na da tushe a wani bangare, amma har yanzu Nijeriya na da tsarin jam’iyyu da dama. Abin da zai kayyade makomar shi ne yadda jam’iyyun adawa za su tsara kansu, da kuma yadda tsarin zabre da cibiyoyin dimokiradiyya za su ci gaba da aiki.
A’a. Wannan ba ra’ayina ba ne. Ba abin karba ba ne, kuma na bayyana a fili cewa hakan ba gaskiya ba ne. Idan ka tuna, a wani lokaci a shekarar da ta gabata, wasu daga cikinmu mun fito muka yi bayani a fili a kan wannan batu. Har ma jam’iyyar APC ta ja baya daga wannan magana, ta ce ba wannan ce manufarsu ba.
Ko da yake ba za mu iya tabbatar da gaskiyar niyyarsu dari bisa dari ba, zan iya tabbatar maka cewa a fahimtarmu, ba itace manufarsu ba. Ka ga, dukkanmu muna da zabubbuka. Kamar yadda ka sani, wasu daga cikinmu ma sun kasance cikin wadanda suka kafa APC. Don haka ba sabon abu ba ne a gare mu.
Idan na ce maka wani zai iya zuwa can gobe, ba wai ba mu san wurin ba ne, amma batun zabin da muka yi ne. Mu muna nan a wannan jam’iyya, kuma za mu ci gaba da tafiya da ita har zuwa karshe. Muna ganin wannan kawai wani mataki ne na wucin gadi.
Bai kamata mu duba harkar jam’iyya kawai ta fuskar zabe ba. Akwai abubuwa da dama da jam’iyya take yi fiye da zabe. Dole ne a samu jam’iyya mai karfi da kuma ‘yan adawa masu kwazo. Dimokiradiyya ba ta tsaya ga jam’iyya daya mai mulki ba.
Don haka, a bar batun tsarin kasa mai jam’iyya daya, ba abin da yake da tushe a zahiri. Kuma mutane da dama za su yi aiki don hana hakan faruwa.
Kana da abokai a APC da ADC, Shin an taba yi maka tayin shiga daya daga cikin wadannan jam’iyyun?
A’a, ban samu irin wannan tayin ba, kuma kamar yadda na fada, ni na yi zabina kuma ina nan a jam’iyyar PDP. Mun himmatu wajen ci gaba da aiki a cikinta har zuwa karshe.
Siyasa tana da wata al’ada, mutane su yi hulda da abokai daga jam’iyyu daban-daban, amma hakan ba lallai yana nufin canjin jam’iyya ba ne. Kowane mutum yana da zabinsa, kuma a halin yanzu, ni na zabi in ci gaba da kasancewa a PDP.
Da tawali’u, eh, na ji irin wadannan maganganu. Wasu cikin raha suna cewa, “Ka dawo wannan gidan da kai ka gina shi.” Wasu kuma suna cewa, “Mun kasance kamar fasinjoji ne a tafiya; yanzu muna zuwa wani wuri.” An ma tunkare ni a wasu lokuta, amma na yanke shawarar ci gaba da zama a PDP.
Wasu na ganin cewa jam’iyyar APC na da hannu a rikicin cikin gida na PDP. Mene ne ra’ayinka a kan wannan?
A irin wannan magana, ya kamata a yi taka-tsantsan. A siyasar Nijeriya, ana yawan zargin cewa jam’iyya mai mulki na da hannu a matsalolin jam’iyyun adawa, amma tabbatar da hakan yana da wahala. Sau da yawa rikice-rikicen jam’iyya na tasowa ne daga cikin gida irin su rashin jituwa tsakanin shugabanni, fafutukar mulki, bambancin ra’ayi, da kuma rikice-rikicen tsari.
A gefe guda, yana yiwuwa a ce siyasar waje da mu’amalar ‘yan siyasa na iya kara zafi ko tasiri ga wasu rikice-rikice, amma hakan ba hujja ba ce kai tsaye cewa jam’iyya mai mulki ce ke haddasa rikicin.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne: Jam’iyyar da ke da karfi tana da ikon gyara kanta daga ciki. Idan aka samu matsaloli, mafita ta farko yawanci tana cikin tattaunawa da sulhu na cikin gida
Zargin waje kadai ba ya magance matsalar; dole a duba abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar da kanta.
Don haka, wannan ra’ayi ya na wanzuwa a siyasa, amma ba abu ne da ake tabbatarwa cikin sauki ba. Jam’iyyun adawa kamar PDP suna da alhakin daidaita kansu, komai tasirin waje, domin su ci gaba da zama masu karfi a fagen siyasa.
Ga yadda yake, ba za a dora duk laifin a kan jam’iyyar mai mulki kadai ba. Jam’iyyar mai mulki tana kama da wanda ke zuwa kasuwa yana kokarin shawo kan mutane su shiga cikinta. Ko hakan yana da adalci ko a’a, wanna wata muhawara ce daban. Wasu daga cikinmu suna cewa ba adalci ba ne, domin dole ne a guji tsarin jam’iyya daya. Dimokiradiyya na bukatar tsarin jam’iyyu da dama.
Ko da na kasance a jam’iyyar mai mulki, akwai inda zan ce, “A’a, dole mu ci gaba da samun jam’iyyar adawa.” Ra’ayina shi ne, jam’iyyar mai mulki ya kamata ta karfafa samun dimokiradiyya mai karfi. Dimokiradiyya ba ta cika ba sai da jam’iyya mai mulki da jam’iyyar adawa. Idan babu adawa, babu dimokiradiyya. Wannan shi ne ra’ayina. Kuma kasa kamar Nijeriya ya kamata ta zama abin koyi ga wasu kasashe.
Har ila yau, yanayin jam’iyyar adawa yana nuna halayen shugabannin da ke jagoranta. Mu fadi gaskiya: halaye a nan yana nufin mutane su tsaya kan abin da suka yi imani da shi. Ya kamata ka kasance da abin da ka tsaya a kai. Shi ya sa nake dariya idan mutane suka ce, “Kana shiru sosai,” ko kuma “Watakila ka fi kusa da APC.”
A bisa tarihin siyasar da na yi, yawancin mutane sun san cewa idan na dauki matsaya kan wani abu, ina tsaya wa da karfi a kai. Ba na canza magana cikin sauki, ba na zama wanda zai ce abu daya da rana, wani daban kuma da yamma.
Wane kokari PDP ke yi wajen wayar da kan jama’a da kuma tattara su, domin su fahimci ainihin halin da ake ciki kamar yadda ka bayyana?
Jam’iyyar PDP na daukar matakai daban-daban domin wayar da kai da kuma karfafa mambobinta da al’umma gaba daya. Wasu daga cikin abubuwan da ake yi sun hada da: Taron wayar da kai da tattaunawa: Ana shirya tarurruka a matakin kasa, jihohi da kananan hukumomi domin bayyana matsaloli da kuma hanyoyin magance su, tare da jawo mambobi su shiga cikin tattaunawa.
Sadarwa ta kafofin yada labarai da na zamani: PDP na amfani da jaridu, rediyo, talabijin da kafofin sada zumunta wajen isar da sakonni ga jama’a da kuma fayyace matsayinta.
Gangamin siyasa da tuntubar al’umma (grassroots mobilisation): Ana kokarin komawa matakin kasa-kasa domin jin ra’ayoyin mutane da kuma karfafa goyon baya daga tushe.
Horar da mambobi da shugabanni: Ana shirya shirye-shiryen gina karfin shugabanci da fahimtar tsarin dimokiradiyya da dokokin zabe.
Kokarin hada kai da sulhu a cikin gida: Domin warware rikice-rikice, ana gudanar da tattaunawa da sasanci tsakanin bangarori daban-daban na jam’iyyar.
Manufar wadannan matakai ita ce a karfafa jam’iyya ta zama mai hadin kai, ta fahimci matsalolinta, kuma ta iya gabatar da ‘yan takara masu karfi a zabe mai zuwa.
Wannan yana daga cikin irin tattaunawar da nake yi tare da wasu shugabanni, kokari ne na ci gaba da yi wa mutane bayani da wayar da su.
Na yi imani cewa yawancin mutanen da suka fice daga PDP, ko suke ficewa, sun yi hakan ne saboda tsoron cewa PDP ba za ta kasance a kan takardar zabe a 2027 ba. Zan raba su zuwa rukuni-rukuni:
Akwai wadanda suka fita da gaske saboda wannan dalili, kuma akwai wadanda na yi imani za su dawo bayan Lahadi da Litinin, bayan mun gudanar da babban taron jam’iyya. Za su ga hukumar zabe ta kasa INEC, wadda ke tabbatar da sahihancin abin da muka yi. Za mu samu NWC da ya fito daga wannan taro, wanda zai iya gudanar da zaben fidda-gwani. Daga nan, ‘yan takara za su iya zuwa su karbi fom na PDP su tsaya takara na majalisar jiha, gwamna, shugaban kasa, da sauransu.
Wannan shi ne rukuni na farko. Misali, wani kamar Dabid Emmanuel Ombugadu daga Nasarawa ya riga ya dawo. Haka kuma, a wasu jihohi, mutane sun yi taro kwanan nan, inda duk masu niyyar takara suka aike da sako cewa PDP ce zabinsu na farko.
Idan irin wadannan mutane suka ga an warware matsalolin da aka samu, kuma bayan taron ya gudana lafiya, za su samu kwarin gwiwa su dawo su nemi fom na PDP.
Mun gode kwarai da gaske
Nima na gode















Discussion about this post