ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Disu

Babban Sufeton Janar na  Ƴansandan Nijeriya, IGP Olatunji Disu, ya umarci ɗaukacin jami’ai maza da mata na Rundunar  (NPF) da su guji duk wani aiki na dandalin sada zumunta (social media) da ba su da izini a kai, wanda zai iya zubar da mutunci, ƙwarewa, da kuma kimar rundunar a idon jama’a.

Wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴansandan Ƙasa (FPRO), CSP Anietie Okokon Iniedu ya fitar, ta bayyana cewa wannan umurni ya biyo bayan fargabar da ake da ita game da yadda jami’an ƴansanda ke ƙaruwa wajen ƙirƙira da wallafa bidiyoyi, gudanar da shirye-shiryen kai tsaye, da sauran ayyukan soshiyal midiya suna sanye da kayansanda, ko kuma a cikin wasu yanayi da ke nuna su a matsayin mambobin NPF ba tare da samun izini na hukuma ba.

Yana mai cewa: “IGP ya jaddada cewa, duk da cewa shafukan sada zumunta na zamani muhimmin makami ne na sadarwa da mu’amala da jama’a, amfani da su da jami’ai masu hidima za su yi dole ne ya kasance cikin tsarin dokoki, ka’idoji, da kuma Tsarin Manufofin Soshiyal Midiya na NPF.”

ADVERTISEMENT

Kakakin ya bayyana cewa Shugaban Ƴansandan ya lura da cewa: “An haramta wa jami’ai kirkira ko raba abubuwan da ba su da izini a kansu suna sanye da kayan sanda, yin tsokaci a gaban jama’a kan al’amuran yau da kullum na ƴansanda, bayyana bayanan sirri na ayyukan tsaro, ko amfani da matsayinsu na jami’an ƴansanda domin tallata kansu, nishaɗi, ko neman riba ta kasuwanci.”

“Domin tabbatar da bin wannan doka, an umarci Kwamishononin Ƴansanda, Shugabannin Ma’aikatu, Kwamandoji, da sauran jami’ai masu sanya ido da su gaggauta faɗakar da ma’aikata na ƙarƙashin umurninsu, sannan su tilasta bin wannan umurni baji-ba-gani.”

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

“Za a gurfanar da jami’an sa ido kuma a gudanar da bincike a kansu idan suka gaza ɗaukar matakin da ya dace kan duk wani saɓa doka da aka samu a yankunansu na kulawa.”

Haka zalika, CSP Iniedu ya ƙara da cewa: “IGP ya ƙara umartar Sashen Leƙen Asiri na Rundunar (FID) da Sashen Kula da Ƙa’idojin Ƙwarewa (Ɗ-Sƙuad) da su ƙarfafa sanya ido kan dandalolin sada zumunta na zamani, domin gano jami’an da ke gudanar da ayyukan da suka saɓa wa ƙa’idojin ƙwarewa na NPF.”

A cewar Kakakin rundunar (FPRO): “NPF tana jaddada aniyarta na tabbatar da ɗa’a, ƙwarewa, da kuma riƙon amana wajen sadarwa da jama’a, tare da tabbatar wa mambobin al’umma ci gaba da sadaukarwarta wajen kiyaye amincewar jama’a da kuma mutuncin hukumar.”

Disu
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Kotu Da Ɗansanda

Gwanjon Kadarori: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da Sani Sha’aban Ya Shigar

June 18, 2026
Next Post
Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Sabbin Matakan Dakile Haɗura A  Titin Bypass

Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Sabbin Matakan Dakile Haɗura A Titin Bypass

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.