ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manoma Sun Tafka Asara A Wannan Shekarar

by Sulaiman
4 months ago
Manoma

Manoman tumatir a Nijeriya, a tsawon shekaru, na fuskantar manyan kalubale na ajiya bayan girbi, ciki har da rashin ingantaccen tsarin abubuwan sanyaya kayan gona, wanda hakan ke haifar da asarar har zuwa kashi 50 cikin 100 ko fiye da hakan ga manoma, musamman wadanda suka dauki bashi don noma a lokacin bazara, da kuma faduwar farashi sakamakon yawaitar samfur.

 

Manyan matsalolin sun hada da:

ADVERTISEMENT

Rashin isasshen wurin ajiyar dake sanyaya kayan gona. Rashin ingantaccen tsarin sufuri, Saukin lalacewar kayan gona (high perishability), inda amfanin zai rayu na tsawon makonni 2 zuwa 3. Kwari da cututtuka kamar Tuta.

Jaridar Weekend Trust ta ruwaito cewa, bayan yin aiki tukuru wajen noman tumatir na kusan watanni biyar, kayan sun lalace a cikin awanni 48 kacal.

LABARAI MASU NASABA

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

Daga gonaki har zuwa kasuwa, babban adadin tumatir da manoman lokacin bazara ke nomawa a Alau da wasu sassan Jihar Borno na lalacewa ne kawai.

Wannan lamari, wanda abin tausayi ne kuma mai girma, shi ne abin da dubban manoma a Jihar Borno ke fuskanta a halin yanzu. Manoman sun roki gwamnati da ta tsoma baki ta hanyar kafa masana’antar sarrafa tumatir, domin ceto kayan daga asarar bayan girbi a matsayin wata hanyar taimakonsu.

Majiya daga wurin wadda ta ziyarci gonakin ban ruwa a Alau, Maiduguri da Jere, ta ruwaito yadda wannan yanayi ke haifar da tashin hankali, tana barin yawancin manoma cikin damuwa da wahala.

Yayin da manoman tumatir a Alau ke fuskantar manya-manyan asara sakamakon tsadar sufuri, manoman tumatir a cikin garin Maiduguri suna cewa ba za su iya samun masu saye ba ko kuma farashin tallafi mafi kankanci ga kayansu, wanda ke ci gaba da wanzuwa a manyan kasuwanni a fadin jihar da ma wasu wurare na waje.

A wata hira da Weekend Trust ta yi, mafi yawan wadannan manoma sun ce suna samun dimbin amfanin gona, amma suna ci gaba da fuskantar matsaloli na rashin isasshen ko cikakken wurin ajiya da hanyoyin kiyaye kayan gona domin kaucewa asara, wanda ya zama matsala ta dindindin ga manoman tumatir da kayan lambu a jihar.

A cewarsu, suna shuka iri tun farkon Oktoba kuma su kula da shukar na tsawon watanni hudu zuwa biyar, har sai ta fara bada ‘ya’ya a watan Janairu, amma mafi yawan tumatir din da aka girbe yana lalacewa ne sakamakon rashin ingantaccen tsarin wurin ajiya.

Daya daga cikin manoman tumatir a Alau, Malam Ardo Modu, wanda ya shuka kuma ya samu girbi mai yawa sakamakon ingantattun iri da taki, ya ce a halin yanzu ba shi da wani zabi sai ya bar wani bangare na tumatir ya lalace, yayin da mafi yawan girbin ya zubar a bakin dam.

“Wani lokaci ba mu da wani zabi sai mu zubar da tumatir din, saboda sun lalace kuma suna wari. Wannan shi ne abin da muke fuskanta tsawon shekaru da dama.

“Ina girbe kwandon tumatir 30 a kowace rana, amma idan aka kwatanta da abin da na saka a gona, asarar ba za a iya misultuwa ba,” in ji shi.

Modu, wanda ke cewa ya shigar da noman lokacin bazara tsawon shekaru 40, ya ce kafin ambaliyar da ta biyo bayan fashewar rijiyar ruwa ta Alau, yana da gonakin kayan lambu guda shida da yake nomawa.

“Ko da yake kowace kakar noma na zuwa da kalubalen ta, amma ba mu taba fuskantar matsala mai tsanani kamar wannan ba. Ba ma samun riba sosai, kuma kayan aikin gona sun yi tsada matuka. Buhunan taki yanzu suna kai Naira 70,000.

“Jiya, na zubar da tumatir din da na kai kasuwar Gambarou a cikin kogin saboda mutane sun ki saya ko ma karba a lamunin bashi. Duk abin da na sayar bai isa ya rufe kudin sufuri ba,” in ji shi cike da damuwa.

A cikin wannan mawuyacin hali, ya roki gwamnatocin jiha da tarayya da su tsoma baki ta hanyar gina masana’antu na zamani da za su iya ajiye tumatir da sauran kayan lambu masu saurin lalacewa da suke nomawa da girbe a kowace shekara.

“Muna so a kafa kamfani na sarrafa tumatir domin dakile asara. Haka kuma muna so a rage farashin taki. Idan farashin ya sauka daga Naira 70,000 zuwa Naira 25,000 zai kasance da amfani sosai, saboda muna noma shinkafa, rogo, dankali da sauran nau’ikan amfanin gona a nan,” in ji shi.

Modu da abokan aikinsa suna fatan cewa rokon nasu zai isa ga masu ruwa da tsaki, kuma yayin da hakan ke faruwa, ya tabbatar cewa noma lokacin bazara zai ci gaba da bunkasa kuma ya kawo tasiri mai kyau ga tattalin arziki.

Alaramma Zarami, wani manomi tumatir, ya ce gwamnati ta karfafa su komawa gona don noma amfanin gona da kayan lambu domin samun abin dogaro, amma ya koka cewa shigo da abinci yana karuwa, lamarin da ke barin manoma cikin asara da wahala.

Ya yi tsokaci yana cewa, “Maimakon a tallafa mana a cikin gida, an bude iyakoki don shigo da abinci, kuma mu manoma na gaskiya ne ke fuskantar asara.

“Ana shigo da tumatir a cikin gwangwani da kuma busasshen tumatir, barkono, har ma da albasa cikin kasar, yayin da amfanin gona namu ke lalacewa a gonaki. Ba mu da karfin kafa masana’antar sarrafa kayan gona, kuma gwamnati ba ta taimaka mana wajen gina su ba.

“Haka kuma muna so su tsoma baki wajen samar da kayan aikin gona, kamar iri masu inganci, magungunan kwari, da injinan ban ruwa domin habaka amfanin gona,” in ji shi.

Wani manomi kuma, Muhammad Kudu, ya ce sun dauki watanni hudu wajen noman tumatir, amma ba su samu masu saye ba bayan girbi.

“Lokacin da muka girbe kuma ba mu sayar ba, muna saurin busar da tumatir kafin ya lalace. Daga nan sai mu sake sayarwa ga masu amfani a matsayin tumatir busasshe.

“Noman tumatir aiki ne mai wahala kuma yana iya lalacewa, don haka sai wadanda ke da karfin jiki da kudi ne kawai za su iya ci gaba da noma, saboda dole ka saya man fetur don injin ban ruwa, taki, da magungunan kwari.

Kudu, wanda a farko ya ki yin magana da Weekend Trust, ya ce ‘yan jarida da dama sun riga sun yi hira da shi a baya amma ba su samu wani taimako daga gwamnati ba.

“Gwamnatin Jihar ta bayyana sau da yawa cewa suna tallafa wa manoma, amma ban taba ganin wani tallafi daga gare su ba a cikin shekaru 50 na wannan aikin.”

“Na yi amfani da dukiyata wajen noman tumatir, amma yanzu ba mu da inda za mu sayar da su. Ko dai mu busar da su cikin kwana biyu ko kuma su lalace.

“Ko ma ‘yan sayar da kaya masu yawa daga wasu sassan Jihar sun daina zuwa, saboda yawaitar tumatir a wannan kakar. Babu damar sayar da kayan a cikin gida.

“Mun zuba jari mai yawa a wannan gona; fetur, iri, aikin hannu, magungunan kwari da taki. Wasu daga cikinmu dole ne su biya basussukan da muka dauka don noma wadannan kayan lambu,” in ji shi.

Ya roki gwamnati da su aiko tawaga zuwa gonaki don tantance halin da ake ciki da kuma tsoma baki a fannoni da za su ceci manoma daga mawuyacin halin da suka tsinci kansu.

“Idan gwamnati za ta tallafa wajen kafa masana’antar sarrafa tumatir, hakan zai karfafa mana gwiwa mu kara yawan amfanin gona. Muna shirye mu yi aiki. Mu manoma ne, wannan ne aikinmu,” in ji shi.

A tattaunawa da mujallar mu, malami kuma masani a harkar noma, Magaji Zakari, ya ce mafi yawan manoman sun tilasta zubar da kayan saboda yawan amfanin gona da aka samu.

“Tun bayan faduwar farashin hatsi, da yawa daga cikin manoma sun koma noman tumatir da sauran kayan lambu, wanda ya haifar da yawaitar kayan a kasuwa, lamarin da ya kai ga faduwar farashi,” in ji shi.

Ya lura cewa tumatir din da aka girbe ya zama nauyi ga manoma, har sai da ake ganin ya fi rahusa a zubar da su fiye da mayar da su gida daga kasuwa.

Haka kuma ya lura cewa rashin masana’antu na sarrafa kayan gida ko tsarin sanyaya kayan gona da ke aiki yadda ya kamata domin ajiye kayan da suka wuce bukata na ci gaba da raunana kokarin manoma da rage ribarsu idan masu ruwa da tsaki ba su dauki wannan lamari da muhimmanci ba.

Har ila yau, ya ambaci cewa yanayin zafi da danshi na Maiduguri ne ke sa kayan lambu su lalace cikin sauri.

“An tabbatar cewa, ba tare da isasshen wurin ajiya ba, tumatir na lalacewa cikin sa’o’i 48 a yanayi mai zafi da danshi kamar na Maiduguri,” in ji shi.

A martaninsa, Kwamishinan Noma na Jihar Borno, Bawu Musami, ya ce gwamnatin jihar ta riga ta sayi kuma ta girka wani tsarin sarrafa tumatir na Modular domin magance wasu daga cikin matsalolin da manoma suka kawo.

“Mun kammala girkawa fiye da watanni biyu zuwa uku da suka wuce a cikin Industrial Park. Yanzu muna da biyu; wanda aka girka a farko nau’in kasuwanci ne wanda ke bukatar babban adadin tumatir domin ya yi aiki yadda ya kamata.

Ya ce, a matakin mafi girma, suna bukatar hadin gwiwa da wani kamfani masu zaman kansu inda musamman yankin sarrafa kayan gona zai shiga. “Zai fara aiki yadda ya kamata idan sun shiga cikakke cikin aikin START 2.”

Ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa kashi 30 cikin 100 na dukkan amfanin gona na lalacewa sakamakon rashin ingantacciyar ajiya bayan girbi da rashin kulawa bayan girbi, kuma ya amince cewa akwai gibi tsakanin ma’aikatar da wasu daga cikin manoma game da kara kima ga kayan da aka girbi.

Manoma
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
  • Sulaiman
    Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
  • Sulaiman
    Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

MASU ALAKA

Manoma
Rahotonni

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

May 17, 2026
Manoma
Rahotonni

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

May 16, 2026
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada
Rahotonni

Almajiranci:Matsala Ko Maslaha

May 10, 2026
Next Post
An Shirya Bikin Share Fagen Shirin Talibijin Na CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar Gargajiyar Kasar Sin A Cape Verde

An Shirya Bikin Share Fagen Shirin Talibijin Na CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar Gargajiyar Kasar Sin A Cape Verde

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.