ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufar Cire Haraji Za Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Wajen Zamanantar Da Kansu

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Haraji

A ranar 3 ga wata, kwanaki biyu bayan da Sin ta fara aiwatar da manufar cire harajin kwastam gaba daya ga kasashen Afirka da ke da huldar diflomasiyya da ita, wani jirgin ruwa dauke da ton 747 na kasusuwan shanu daga Najeriya ya isa tashar jiragen ruwa ta Dayaowan da ke birnin Dalian na arewa maso gabashin Sin, wadanda suka kasance kaya na farko da aka shigo da su daga Afirka ba tare da biyan harajin kwastam ba ta tashar kwastam ta Dalian, bayan da aka fara aiwatar da sabuwar manufar cire haraji.

A ranar 1 ga watan Mayun 2026, manufar cire harajin kwastam ga kasashe 53 na Afirka masu huldar diflomasiyya da Sin ta fara aiki. Wannan mataki ya shafi kashi 100% na kayayyakin kasashen, ba tare da iyaka ko sharadi ba.

Amma me ake nufi da cire harajin kwastam ga kasashen Afirka? Hakan yana nufin cewa, an shigo da wadannan kasusuwan shanu daga Najeriya ba tare da biyan kudin kwastam na kimanin yuan 300,000 (kudin kasar Sin) ba, wanda kuma yake nufin cewa farashin tuffa daga Afirka ta Kudu zai ragu da kimanin yuan 20 a kowane akwati. Har wa yau, yana nufin cewa koko daga Cote d’Ivoire da Ghana ba za su kara biyan harajin kwastam na kimanin kashi 8% zuwa 22% ba.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda kamfanin shigo da kayayyakin na kasusuwan shanu na kasar Sin ya bayyana, kasusuwan shanu su ne muhimmin sinadari wajen kera gelatin. Bayan aiwatar da manufar cire harajin kwastam, ana sa ran kudin da kamfanin ke biya wajen sayen kasusuwan shanu zai ragu da sama da yuan miliyan 3 a duk shekara.

Hakan zai bai wa kamfanonin Sin damar habaka sayen kayayyaki daga kasashen Afirka, yayin da masu sayayya na kasar Sin za su samu damar sayen kayayyakin Afirka masu inganci cikin rahusa. Ke nan wannan zai amfani kowane bangare.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Tun da dadewa, Afirka tana fitar da albarkatun kasa ne kawai a kasuwannin duniya. Wasu ‘yan uwanmu na Afirka na iya damuwa: Shin cire harajin kwastam yana nufin Afirka za ta ci gaba da fitar da albarkatun kasa cikin farashi mai rahusa? A hakika, manufar cire harajin kwastam tana rage farashin kayayyakin Afirka don kara samun damar shiga kasuwar Sin, a sa’i daya kuma, za ta jawo jari da fasaha daga kasa da kasa, wanda hakan zai taimaka ga inganta ayyukan sarrafa kayayyaki a gida don kara musu kima.

Ta haka ne ciniki zai taimaka wa Afirka raya sassan noma da masana’antu.

Bugu da kari, manufar cire harajin kwastam zai karfafa ma’aikatan Afirka ta hanyar ciniki, tare da inganta samar da ayyukan yi, kuma gaba daya tana baiwa kasashen Afirka damar tsayawa a kafafuwansu don raya kansu. Kamar yadda shugaban sashen koyon ilimin tattalin arziki na Jami’ar Kasa ta Lesotho, Dr. Leseko Makhetha, ya ce: “Manufar cire harajin kwastam kai tsaye tana tallafawa bunkasuwar masana’antu a Afirka, domin ba wai kawai ga albarkatun kasa ba, har ma ga kayayyakin da aka sarrafa da kayan karshe.

Manufar tana karfafa wa masana’antu na gida gwiwar habaka samar da kayayyaki, da inganta sarrafa kayayyakin da ke da karin kima, da samar da ayyukan yi a fannoni daban-daban.”A halin yanzu, tattalin arzikin duniya na fuskantar kariyar kasuwanci da kuma tashe-tashen hankula na siyasa.

Matakin cire harajin kwastam na Sin ba wai kyauta ce ta tattalin arziki ga kasashen Afirka ba, har ma da sakon siyasa mai karfi, wato yayin da tsarin kasuwancin duniya ke fuskantar matsaloli, Sin ta tsaya tsayin daka a kan bude kofarta ga kasashen Afirka, inda ta kafa sabon misali ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

A shekarar 2025, yawan ciniki tsakanin Sin da Afirka ya kai dala biliyan 348, wanda ya karu da kashi 17.7%, tare da kafa sabon tarihi. Sai kuma a rubu’in farko na shekarar 2026, yawan ciniki a tsakanin sassan biyu ya karu da kashi 26.8%.

Ba shakka, manufar cire haraji za ta taimaka wa cinikin Sin da Afirka ya kai wani sabon matsayi.

Haraji
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
Haraji
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Sanatan Kaduna Ta Arewa Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC

Sanatan Kaduna Ta Arewa Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.