ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar ADC Ta ADC Ce BA Ta APC Ba Ce

by Sulaiman
2 months ago
ADC

Wannan shi ne abu na karshe da jam’iyyar (ADC) za ta so ta ji, amma dole ne a fada, ko da kuwa jam’iyyar ta ki sauraro. Lamarin ya fara ne da jinkirin rajistar jam’iyyar.

Lokacin da abubuwa ba sa tafiya da gaggawa sauya sheka na farko galibi daga jam’iyyar (PDP), lamarin da ba su za ta ba sai suka zargi jam’iyyar (APC) mai mulki da jinkirta rajistar, tare da zargin cewa tana amfani da bangaren da Ralph Okey Nwosu ke jagoranta domin kara jan kafa.

  • Kwankwaso Zai Koma ADC Ranar Litinin
  • Ding Xuexiang Ya Gana Da Direktan Hukumar Kare Ikon Mallakar Fasaha Ta Duniya

A karshe an yi rajistar jam’iyyar a watan Yuni. Amma hakan bai kawo karshen sabani ba. Yayin da PDP ke durkushewa kuma mambobinta da dama musamman gwamnoni suka sauya sheka, ADC ta zargi APC da lallashi, bayar da cin hanci ko kuma matsin lamba domin mayar da Nijeriya kasa mai kama da jam’iyya guda daya.

ADVERTISEMENT

hakan na zuwa ne bayan sun gaza bayar da gamsasshiyar jujja, wadda ke cewa ko da dukkan gwamnoni a Nijeriya sun koma APC, hakan ba zai ceci jam’iyyar mai mulki daga hukuncin masu zabe mai tsauri a shekara mai zuwa ba, saboda rashin kyakkyawan aikinta.

 

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Zaben Shugabanni

Sabuwar hujjar ita ce, jam’iyyar APC na shirin amfani da irin dabarar da ta yi amfani da ita wajen tarwatsa jam’iyyar Labour Party da kuma PDP a kan ADC: wato dasa shugaba domin raunana jam’iyyar, raba ta gida biyu, da kuma haddasa rikice-rikicen cikin gida.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Litinin ta zargi jam’iyyar mai mulki da shirin amfani da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin amincewa da wani dan jam’iyyar da aka kora, Nafiu Bala Gombe, a matsayin shugaban kasa na ADC.

Me ya sa? “Domin tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ba tare da hamayya ba a matsayin dan takara guda daya mai karfi a takardar zabe ta 2027.”

Ban san wane irin wani sabon kulli ko zargi ADC za ta kirkiro kafin kasuwa ta gaba ba, amma ina ganin babbar matsalar jam’iyyar ita ce kanta. Idan ta ci gaba a haka, kafin APC ta kashe ta, tuni za ta riga ta mutu, kuma a kan kabarinta za a rubuta: nan ne ragowar wata jam’iyya da ta yi tunanin za ta samu mulki cikin sauki kamar ana zabar abinci daga menu!

 

Hanyoyin Karbe Shugabanci

Ba a ba da mulki; ana karbarsa ne, har ma a kwace shi ta hanyar tsari, shiri, da aiki. Ba a kafa jam’iyyar ADC domin ta dade ba, kamar yadda ake gina gida daga tushe, tubali bayan tubali, da hakuri a kowane mataki tare da bin tsari.

A mafi yawan lokuta, jam’iyyar hadin gwiwa ce ta masu jin haushi da kuma masu matsananciyar sha’awar mulki, bayan wasu manyan jiga-jiganta sun lalata ta ta hanyar komawa jam’iyyar PDP.

Mun fi sanin burin zama shugaban kasa na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da Peter Obi, da kuma Rotimi Amaechi, fiye da abin da jam’iyyar take tsayawa a kai a zahiri.

Kwanan nan a Benin, Jihar Edo, an samu sabani tsakanin Odigie Oyegun da Rowland Owie, dukkansu dattawan siyasa masu shekaru da suka koma ADC, kan ko yankin Kudu maso Kudu ya kamata ya mara wa Amaechi ko Atiku baya, yayin da magoya bayan Obi ke gefe suna nuna damuwa.

Abin da ake fadda da kuma aikatawa domin tabbatar da tikitin takarar shugaban kasa ga daya daga cikin ukun ya fi yawa fiye da abin da muka sani game da kokarin gina jam’iyyar.

A cikin wani yanayi da ya zama juyin akida mai muni ga asalin manufar jam’iyyar siyasa a matsayin wata cibiya, jam’iyyun sun zama kamar takardun nade-nade da ake yarwa, yayin da sauya sheka ya zama kamar wata dabara ta yaudara.

 

Dubi Ga Tarihi

Makomar jam’iyyun siyasa a Jamhuriyar Nijeriya ta Hudu na nuna wani labari mai tayar da hankali.

Tsakanin 1999 zuwa 2015, lokacin da ludayin jam’iyyar PDP ke kan dawo, har yanzu tana iya raba ganimar siyasa ta hanyar da ta bai wa dimokuradiyya makoma da kuma fata. Shugaba Olusegun Obasanjo ya lashe zaben shugaban kasa da kashi 62.78 cikin dari na kuri’u, rinjaye cikakke wanda ya kayar da abokin hamayyarsa Olu Falae, wanda shi ne dan takarar hadin gwiwa na jam’iyyun (APP) da (AD).

Jam’iyyar PDP ta rike jihohi 21 cikin 36, yayin da jam’iyyun APP da AD suka rike jihohi 9 da 6 bi da bi. Haka kuma PDP ta samu kujeru 59 cikin 109 na Majalisar Dattawa da kuma kujeru 206 cikin 360 na Majalisar Wakilai a wancan lokacin. Don haka abin mamaki ne ga masana tarihin siyasa cewa cikin kasa da shekaru 27 kacal na kasancewa kungiya mai karfi haka, PDP ta zama kamar ba a iya ganinta, ko da kuwa don a adana ta ne kamar gawar da aka shanya.

Tambayar, me ya faru, tana samun amsa mai sauki amma mai dacewa, wato dora laifi kan Tinubu, duk da cewa tsutsar da ke cin ‘yan adawa tana cikin ‘yan adawar ne da kansu.

 

Tuna Baya Shi Ne Roko

Bayan zaben gama-gari na 2023, PDP, ragowar da daga ciki da yawa daga mambobin ADC suka fito ta samu kujerun gwamna 10: Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Delta, Enugu, Oyo, Filato, Ribers, Taraba, da Zamfara, yayin da ta 11 ita ce Bayelsa a zaben da aka yi a lokacin da ba cikakken zagaye ba. Wannan ya isa don bai wa jam’iyyar damar fafatawa, idan shugabanninta suna da gaskiya.

Manyan jam’iyyun da suka haifa su ne APC (ACN, CPC, da ANPP), wadanda suka kayar da PDP a 2015 tare da taimakon wasu gwamnonin da suka tsere daga PDP, sun rike jihohi 11 kacal. A gaskiya, bayan zaben 2003, Lagos ce kawai jiha ta AD a Kudu maso Yamma, sauran jihohi biyar kuwa PDP ta cinye.

Amma a kidayar karshe, PDP ta rasa tsofaffin matsugunninta na karfi a Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas, da Arewa Tsakiya saboda ambaliyar sauya sheka. Gwamnoni da ke kallon sake zabe da wasu da ke neman ritaya mai dandano zuwa Majalisar Dattawa kusan gaba daya sun bar PDP kamar masu sauka daga jirgi mai fadowa.

A cikin wani yanayi mai tsanani na juyin kaddara, jam’iyyar ta zama wacca kaddara ta shafa saboda mugun misalin da ta kafa a harkar siyasa, inda babu sakamako ga wadanda suka tsere daga jam’iyya ko suka shiga, suna dauke da kujerunsu tare da su.

Daga cikin gwamnonin 11 a watan Mayu 2023, biyu kacal Bala Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde na Oyo ne suka rage a bangaren PDP.

Mohammed, wanda ya yi kokari sosai wajen jan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan cikin zaben shugaban kasa na 2027, ya ga mafarkinsa ya rushe yayin da jam’iyyar ke rugujewa a cikin rikice-rikicen shari’a, sauya sheka, da rikicin iko. Kuma jita-jita na cewa Bala na kan kusurwar barin duk abin da ya rage na tagwayen PDP tare da Makinde nan ba da jimawa ba.

 

Kula Da Yadda Abubuwa Ke Tafiya

Halin da ake gani a fadin Nijeriya gabadaya yana nuna sakamakon daya a zaben gama-gari na shekara mai zuwa nasara ga jam’iyyar APC mai mulki. Ba saboda kyakkyawan aikin da ta yi ba, sai don saboda ‘yan adawa, musamman ADC, sun shimfida tsari ta hanyar sanya kansu ba a matsayin madadi don canji ba, amma a matsayin wuri inda ‘yan siyasa kadan masu matsananciyar sha’awar mulki ke fafatawa.

Ina dariya duk lokacin da ADC ke kiran kanta jam’iyyar adawa. Kusan tana adawa ne. Za ka yi mamaki ka san cewa wani babban jigon ADC yana sadaukar da kansa ga manyan shugabannin APC domin kare muradunsa na kasuwanci da ke cikin hadari.

 

Tantance Tarihi

A karshe, babban abokin adawar APC zai kasance APC kanta. Wannan shi ne darasin tarihi. Daga Jam’iyyar Conserbatibe ta Birtaniya zuwa Indian National Congress, kuma daga African National Congress zuwa ragowar PDP ta Nijeriya (wadda nan ba da jimawa ba za ta dauki Tinubu a matsayin dan takararta), tarihi ya nuna cewa jam’iyyun da ke mulki a karshe suna lalacewa da raguwa daga cikin kansu.

Hadewar rashin kulawa, rarrabuwar cikin gida, da gazawar daidaitawa da sabbin yanayi na jama’a, ko cin hanci da rashin dabi’a mai kyau, a karshe yana shafar su kuma ya rinjaye su.

Halin APC ba zai bambanta ba, ba saboda hayaniyar da ADC ke yi ba.

ADC
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
  • Sulaiman
    Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
  • Sulaiman
    Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

MASU ALAKA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya
Manyan Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

June 3, 2026
Next Post
Gwamnan Zamfara Zai Halarci Taron Horaswa Na Dabarun Shugabanci A Jami’ar Coventry Ta Ƙasar Birtaniya

Gwamnan Zamfara Zai Halarci Taron Horaswa Na Dabarun Shugabanci A Jami’ar Coventry Ta Ƙasar Birtaniya

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.