ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro: Davido Ya Mayar Wa Rarara Martani Kan Rashin Tsaro

by Sadiq
3 months ago

Fitaccen mawaƙin Kudancin Nijeriya, Davido, ya caccaki mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, inda ya zarge shi da fifita siyasa a kan gaskiyar halin rashin tsaron da Nijeriya ke ciki.

Taƙaddamar ta samo asali ne bayan Davido ya bayyana a bikin buɗe gasar Kofin Duniya ta 2026 da aka gudanar a Los Angeles, inda ya sanya wata riga da aka rubuta “Bring Them Home” (A Dawo Da Su Gida), tare da sunayen ɗalibai da malamai sama da 40 da aka sace a Jihar Oyo.

Rarara ya soki matakin, yana mai cewa bai dace a riƙa bayyana matsalolin tsaron Nijeriya a idon duniya ba.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, hakan na iya ɓata sunan ƙasar tare da jefa ta cikin mummunan hali a idon ƙasashen duniya.

Ya kuma yi zargin cewa matakin Davido na iya kasancewa yana da nasaba da siyasa.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Da farko, Davido ya mayar masa da martani cikin raha a shafinsa na sada zumunta, amma daga baya ya fitar da cikakken bayani inda ya ce bai kamata ‘yan Nijeriya su yi shiru kan matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar ba.

Mawakin ya ce kishin ƙasa na gaskiya shi ne a yi magana kan matsalolin da ke damun al’umma maimakon kare muradun siyasa.

Ya kuma zargi wasu da fifita buƙatunsu na siyasa da na ƙashin kansu a kan muradun ƙasa da walwalar jama’a.

“Ya kamata kowane ɗan Nijeriya ya yi magana kan matsalar rashin tsaro,” in ji Davido.

“Ku daina fifita siyasa a kan gaskiya, ku sanya Nijeriya a gaba a cikin duk abin da kuke yi.”

Ce-ce-ku-cen ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda magoya bayan ɓangarorin biyu ke ganin ko bayyana matsalar rashin tsaro a duniya zai taimaka wajen jawo hankali ga matsalar ko kuwa zai ɓata sunan Nijeriya.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 12, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Sace Limami Da Wasu Mutane 7 A Filato

'Yan Bindiga Sun Kashe Hakimin Gwande A Jihar Filato

LABARAI MASU NASABA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.