ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Tasirin Amerika A Idon Duniya Ke Ci Gaba Da Dushewa

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago
The White House is seen shortly before a storm May 30, 2025. (Francis Chung/POLITICO via AP Images)

The White House is seen shortly before a storm May 30, 2025. (Francis Chung/POLITICO via AP Images)

Ga dukkan alamu al’amuran siyasa da na shugabanci a duniya suna daukar wani sabon salo, musamman kan lamuran duniya.

Kowa dai ya san da cewa Amerika ta dade tana yin kaka gida a cikin harkokin duniya, musamman a fannin siyasa da tattalin arziki, wato sai abin da take so za a yi, domin ita ce ke juya akalar tattalin arzikin duniya, ta sanya takunkumin karya tattalin arziki ga duk kasar da ta bijirewa manufofinta, ko kuma ta tumbuke shugaban kasar da ya ki amincewa ya zama dan amshin shatan Amerika, ya Allah ko kai tsaye ko kuma irin abin da ya faru da shugaban kasar Venezuela.

Hakika zalunci ba ya dorewa, domin kuwa alamu suna bayyana cewa, wannan shugabanci na kama karya da Amerika ke aiwatarwa, ya fara samun koma baya. Kasashen duniya sun fara dawowa daga rakiyar shugabanci irin na zalunci.

ADVERTISEMENT

Hatta kawaye da ’yan koren Amerika sun fara juyawa Amerika baya a kan manufofinta na rashin adalci. Kamar kungiyar NATO ta ki amincewa ta shiga cikin yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da kasar Iran, shi ma firaministan Burtaniya ya fito karara ya ce Burtaniya ba za ta shiga cikin wannan yaki na rashin hankali ba.Yanzu haka dai kasar Sin ta zarce Amerika ta fannin samun goyon baya na jagoranci a duniya. Wannan ya bayyana ne a samakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a shekara ta 2025, inda Sin ta samu kashi 36, yayin da Amerika ta samu kashi 31.

Da ma dai kasar ta Sin ta taba zarce Amerika a irin wannan kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan shugabanci har sau biyu, wato lokacin gwamnatin Geoge W. Bush da kuma lokacin shugabancin Donald Trump a karo na farko.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Manyan abubuwan da suka haifar da wannan sauyi sun hada da yadda Sin take maida hankali kan sakamako mai kawo ci gaba a kasashe musamman masu tasowa. Akwai kuma batun hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe wanda aka gina kan tubalin cude ni in cude ka.

Sannan sai batun sabunta manufar nan ta mutuntawa da kiyaye cikakken ’yancin kasa ba tare da la’akari da girma ko kankanta ba, ko kuma karfi ko rauni ba.

Wadannan batutuwa sun taimaka wajen baiwa Sin damar yin zarra da kwarjini a tsakanin kasashen duniya. Yayin da a waje daya ita kuma Amerika take ta fuskantar kalubale kan manufofinta na rashin adalci, zalunci da kuma rashin sanin ya kamata.Wani muhimmin abin da ya kara zubar da mutuncin Amerika shi ne yadda kasar ta fice daga kungiyoyi na kasa da kasa kimanin 66, wadanda suke ba da gudummuwa ta fannoni daban daban ga bil adam. Janye tallafin da Amerika ke baiwa irin wadannan kungiyoyi na kasa da kasa ya haifar da mummunan tasiri musamman ga kasashe masu tasowa.

A waje daya kuwa, sabanin hakan, kasar Sin ta kara bunkasa manufarta ta hadin gwiwa domin amfanin kowa da kowa.

Kasashe da dama suna amfana da Sin a fannoni daban daban, kamar tashoshin jiragen ruwa, filayen saukar jiragen sama, titunan mota, layukan dogo da sauransu. Kasashe da dama daga nahiyar Afirka, Asiya da Latin Amerika sun amfana da irin wannan manufa ta kasar Sin.

Kuma abin ban sha’awa a nan shi ne kasar Sin ba ta shimfida wasu sharudda ga kasa kafin samar da irin wadannan ababen more jin dadin rayuwa. Sannan kuma ta tsaya kan manufar nan ta kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashe. (Lawal Mamuda)

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
An Sake Samun Ɓullar Cutar Korona A Nijeriya

An Sake Samun Ɓullar Cutar Korona A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.