ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Menene Hukuncin Yin Aure Da Cikin Shege?

by Sulaiman
3 months ago
Cikin shege

Salam. Malam, wata ce ta yi cikin shege da wani mutum, sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta, yanzu haka ya aure ta. Mene ne hukuncin auren?

Wa’alaikumus salam. Zina sabon Allah ce da kuma yaɗa fasadi a bayan ƙasa. Aure kuwa, sunnar Manzon Allah ne da samar da zuriya mai albarka, sannan kuma an kwaɗaitar da mu yin sa.

Amma Mazhabar Malikiyya, suna ganin matar da aka yi zinar da ita, sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a ɗaura mata aure, domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an ɗaura aure ba ta yin wannan jinin ba, to za a raba wannan auren ko da sun haifi ƴaƴa, domin suna ganin an ɗaura auren ne a cikin idda, kuma Allah ya hana ɗaura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.                               

ADVERTISEMENT

Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`I, suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an ɗaura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka ƙara da cewa, ko da tana da cikin zinar ne aka ɗaura mata aure, to auren yana nan. Sai dai, Imam Abu Hanifa ya ce; mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.                       

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, “Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa,” Abu- dawud 1847.

LABARAI MASU NASABA

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

Zan Iya Cin Bashin Banki Na Biya Aikin Hajji?

Domin neman ƙarin bayani, duba AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin a yi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin so ne, sannan kuma za a kaucewa faɗawa haɗari, amma idan an riga an yi auren, to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, sai dai ya wajaba su nisanci saduwa kafin ta haihu, saboda hadisin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

Cikin shege
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
Bakon Marubuci

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

May 27, 2026
Cikin shege
Fatawa

Zan Iya Cin Bashin Banki Na Biya Aikin Hajji?

May 16, 2026
Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
Addini

Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

March 20, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Kama Mutane 5 Kan Satar Wayoyin Lantarki A Katsina

Ƴansanda Sun Kama Mutane 5 Kan Satar Wayoyin Lantarki A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.