ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Sin

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da wasu takwarorinsa na kasashen Afirka da suka zo kasar domin halartar taron ministocin da ke kula da aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, a jiya Laraba.

Ministocin harkokin wajen na Afirka da aka yi ganawar da su sun hada da: Yusuf Maitama Tuggar na Nijeriya, da Bakary Yaou Sangare na Nijar, da Jean-Claude Gakosso na Jamhuriyar Congo, da Ronald Lamola na Afirka ta Kudu, da Abdoulkader Houssein Omar na Djibouti, da Samuel Okudzeto Ablakwa na Ghana, da Therese Kayikwamba Wagner ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. Sauran su ne: Carlos Pinto Pereira na Guinea-Bissau, da Karamoko Jean-Marie Traore na Burkina Faso, da kuma Gedion Timothewos na Habasha.

Yayin ganawarsa da Tuggar, Wang ya ce, dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeriya na kara yin kyakkyawan tasiri a duniya bisa manyan tsare-tsare na shugabannin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, kasar Sin na da muradin bai wa Nijeriya damarmaki na samun ci gaba.

ADVERTISEMENT

A nasa bangaren, Tuggar ya yaba da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da kasar Sin, inda ya bayyana aniyar kara zurfafa hadin gwiwa tare da Sin a fannoni daban daban don ciyar da alakarsu ta kawance zuwa gaba a bisa manyan tsare-tsare.

Yayin ganawarsa da Sangare kuwa, Wang ya bayyana cewa, zumuncin Sin da Nijar wani bangare ne na hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma kasar Sin tana son ci gaba da sada asalin zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu, da kara amincewa da juna. Wang ya kuma bayyana fatan kasar Nijar za ta tabbatar da tsaro da kare hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin da kuma Sinawa da ke kasar ta Nijar.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

Sin Ta Bankado Laifukan Miyagun Kwayoyi 12,000 A Watanni Biyar Na Farkon Bana

Da yake nasa jawabin, Sangare ya ce, Nijar na bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana ba da fifiko ga hadin gwiwarta da kasar Sin, da mayar da hankali sosai kan harkokin tsaro, kana tana son kara amincewa da juna, da ci gaba da yin shawarwari bisa mutunta juna a tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Bankado Laifukan Miyagun Kwayoyi 12,000 A Watanni Biyar Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela
  • Sulaiman
    Buƙatar Mayar Da Hankali Wajen Kawo Ƙarshen Ciwon Sikila A Nijeriya
  • Sulaiman
    Sin Ta Bankado Laifukan Miyagun Kwayoyi 12,000 A Watanni Biyar Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

MASU ALAKA

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela
Daga Birnin Sin

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

June 26, 2026
Sin Ta Bankado Laifukan Miyagun Kwayoyi 12,000 A Watanni Biyar Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bankado Laifukan Miyagun Kwayoyi 12,000 A Watanni Biyar Na Farkon Bana

June 26, 2026
Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Next Post
Sin Ta sanya Indonesiya Cikin Tsarin Shiga Kasar Ba Tare Da Biza Ba Na Sa’o’i 240 Da Kara Yawan Kasashen Tsarin Zuwa 55

Sin Ta sanya Indonesiya Cikin Tsarin Shiga Kasar Ba Tare Da Biza Ba Na Sa'o'i 240 Da Kara Yawan Kasashen Tsarin Zuwa 55

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

June 26, 2026
Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

June 26, 2026
sikila

Buƙatar Mayar Da Hankali Wajen Kawo Ƙarshen Ciwon Sikila A Nijeriya

June 26, 2026
Sin Ta Bankado Laifukan Miyagun Kwayoyi 12,000 A Watanni Biyar Na Farkon Bana

Sin Ta Bankado Laifukan Miyagun Kwayoyi 12,000 A Watanni Biyar Na Farkon Bana

June 26, 2026
makarfi

Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi

June 26, 2026
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

June 26, 2026
Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
Kotu Ta Soke Rajistar Jam’iyyar NDC A Matsayin Jam’iyyar Siyasa

Kotu Ta Soke Rajistar Jam’iyyar NDC A Matsayin Jam’iyyar Siyasa

June 26, 2026
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

June 26, 2026
Za A Sake Nazarin Mafi Ƙarancin Albashi A Nijeriya – Gbajabiamila

Za A Sake Nazarin Mafi Ƙarancin Albashi A Nijeriya – Gbajabiamila

June 26, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.